The Innocent (1986 fim)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
The Innocent (1986 fim)
Asali
Lokacin bugawa 1986
Asalin suna البرئ
Asalin harshe Larabci
Ƙasar asali Misra
Characteristics
Genre (en) Fassara drama (en) Fassara
During 159 Dakika
Launi color (en) Fassara
Direction and screenplay
Darekta Atef El Tayeb
Marubin wasannin kwaykwayo Wahid Hamed
'yan wasa
Other works
Mai rubuta kiɗa Ammar El Sherei (en) Fassara
External links

The Innocent (Larabci البرئ, lafazin: Alparee') Fim ne na Masar, wanda aka saki a ranar 15 ga Agusta 1986, tare da Ƴan wasa irin su Ahmed Zaki, Gamil Ratib, da Mahmoud Abdel Aziz .

Labari[gyara sashe | gyara masomin]

Fim ɗin ya nuna Ahmed Sabe' El Leil (Ahmed Zaki), matashin matalauci manomi, wanda ke cika shekarar soja ta tilas. Sakamakon kwazonsa, an zabe shi a matsayin mai gadin gidan yari. A gidan yari yakan ci karo da fursunonin siyasa da ake wulakanta su. Yana bin umarnin azabtarwa da wulakanta fursunonin, har ma da aiwatar da hukuncin kisa, an kawo motocin da ke cike da daliban jami’a da suka yi rikicin biredi a shekarar 1977 zuwa wannan gidan yari, daga cikinsu akwai tsohon abokinsa Hussein Wahdan. Ta hanyar Hussein matashin mai gadi ya gano yadda ake zalunci da cin hanci da rashawa, kuma Ahmed ya ki azabtar da Hussein.[1] A fage na ƙarrshe, wanda aka yi wa katsalandan a Masar, Ahmed ya bude wuta ga jami'ai da sauran sojoji, har sai da aka harbe shi a yayin da wata sabuwar motar da ke cike da daliban tarzoma ta zo.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Al Bary' (1986) The Innocent". El Cinema. Archived from the original on 2 January 2019. Retrieved 1 January 2019.
  2. Zeinab Abul-Magd (April 7, 2010). "Ahmed Zaki: The rise and fall of a generation". Egypt Independent. Retrieved 1 January 2019.