Jump to content

Thomas Mends Kodwo-Mercer

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Thomas Mends Kodwo-Mercer
high commissioner (en) Fassara

1954 - 1956
Rayuwa
Haihuwa Accra, 1916
ƙasa Ghana
Mutuwa Landan, 28 Nuwamba, 2003
Ƴan uwa
Ahali James Mercer
Karatu
Makaranta Adisadel College (en) Fassara
Achimota School
University of Birmingham (en) Fassara Digiri a kimiyya : commerce (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yaren Fante
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa
Wurin aiki Landan
Imani
Jam'iyar siyasa Convention People's Party (en) Fassara

Thomas Mends Kodwo-Mercer (kuma aka sani da TM Kodwo Mercer 1916- 2003) jami'in diflomasiyyar Ghana ne. Shi ne Bakar fata na farko daga yankin Gold Coast (a halin yanzu Ghana) da aka naɗa a matsayin Babban Kwamishina a Burtaniya. [1]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mercer a ranar 17 ga watan Janairu 1916. Ya halarci Kwalejin Horar da Ma'aikata ta Achimota. [2] Ya kuma halarci Kwalejin Adisadel inda daga baya ya zama malami daga shekarun 1938 zuwa 1943. [2] [3] Ya ƙara karatun kasuwanci a Jami'ar Birmingham a shekarar 1948. [2]

Rayuwar Siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Mercer ya kasance memba na Jam'iyyar Convention People's Party. [2]

Mercer ya kasance Kwamishinan Gold Coast na Burtaniya daga shekarun 1954 zuwa 1956. [2] Ya kasance Shugaban Kamfanin Siyan koko, Hukumar Tallace-tallacen Noma da Hukumar Tallace-tallacen Cocoa. [2]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Mercer ya kasance tagwaye ga James Mercer kuma ƙaninsu shine Mr. Krakue Mercer. [3] [4] Ekwow Spio-Gabrah da Andrew Egyapa Mercer su ne yayan nasa. [2] Sally Mugabe ta kasance 'yar yayansa. Shi ɗan Anglican ne. [2]

Mutuwa da binnewa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya rasu yana da shekaru 86 kuma an binne shi a Landan. [2]

  1. "Thomas Mends Kodwo Mercer, the first Black African to be appointed..." Getty Images (in Turanci). 12 September 2023. Retrieved 2023-11-28.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 2.6 2.7 2.8 "Burial of First African Gold Coast Commissioner to UK". Modern Ghana. 28 November 2003. Retrieved 28 November 2023. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":0" defined multiple times with different content
  3. 3.0 3.1 "Adisadel College Old Boys Association – Year Group Reports". www.adisadelonline.com. Retrieved 2023-11-28. Cite error: Invalid <ref> tag; name ":1" defined multiple times with different content
  4. "joefrans.se". joefrans.se. Retrieved 2023-11-28.