Timkat
Timkatbikin murnar baftismar Yesu Almasihu a kogin Urdun, wanda ya kasance wani muhimmin al’amari a addinin Kiristocin Orthodox na Ethiopia. Ana gudanar da wannan biki a ranar 19 ga watan Janairu ko 20 idan shekara ta shiga.[1] Babban abin da ke faruwa a lokacin Timkat shine fitar da Tabot (abin da ke wakiltar Lamarin Alkawari) daga coci zuwa wurin ibada a fili. Ana yin addu'o’i, kiɗa, rawa, da faretin gargajiya. Masu ibada suna shiga cikin ruwa don tunawa da baftisma. Timkat yana ƙarfafa biyayya ga addini da kuma haɗin kai tsakanin mabiyan Orthodox a Ethiopia da ƙasashen ketare. Bikin ya kasance ɗaya daga cikin muhimman al’adu da addinai na Ethiopia.[2]
Yadda ake gabatar da Timkat
[gyara sashe | gyara masomin]Ana fara bikin a ranar da tayi dai-dai da 19 ga wata ko 20 ga wata inda ake shirya Tabot a cikin coci. Ana tsarkake shi da addu’o’i da kiɗa. A safiyar ranar Timkat, manyan kiristoci suna fitar da Tabot daga cikin coci. Ana ɗauke shi a kan kafada cikin farin ciki da kiɗa da rawa. Jama’a suna tare da kiristoci suna bin Tabot zuwa wurin ruwa (tabki ko kogi). Ana rera waƙoƙin addini da kiɗa tare da faretin.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ name=https://www.cpafrica.org.uk/african-culture/timkat-timket-ethiopia-christian-festival/#:~:text=Timkat%20(also%20known%20as%20Timket,re%2Denactment%20of%20the%20baptism.
- ↑ name=https://www.cpafrica.org.uk/african-culture/timkat-timket-ethiopia-christian-festival/#:~:text=Timkat%20(also%20known%20as%20Timket,re%2Denactment%20of%20the%20baptism.