Tony Nwoye
25 ga Faburairu, 2023 - ← Stella Oduah District: Anambra North | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Onitsha, 13 Satumba 1974 (51 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Harshen uwa | Harshen, Ibo | ||
| Karatu | |||
| Makaranta |
Jami'ar Najeriya, Nsukka Ebonyi State University | ||
| Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa da likita | ||
| Imani | |||
| Addini | Kiristanci | ||
| Jam'iyar siyasa |
All Progressives Congress Nigeria Labour Party | ||
Tony Okechukwu Nwoye (an haife shi 13 ga watan Satumban shekara ta 1974) ɗan siyasan Najeriya ne, Sanatan Anambra ta Arewa Sanata. Tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar mazaɓar Anambra Gabas/Yamma ta jihar Anambra. Ya kasance ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, a zaben gwamnan jihar Anambra a 2013, kuma ya kasance ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Anambra na 2017. A halin yanzu mamba ne a jam'iyyar Labour.[1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Nwoye ya fito daga Iyalan Chif da Mrs. Lawrence Nwoye na Offinta Nsugbe an haife shi ranar 13 ga watan Satumban shekara ta 1974. Ya tafi Makarantar Sakandare ta Metropolitan da ke Onitsha inda ya yi karatunsa na sakandare inda ya ci gaba da karatun likitanci a kwalejin likitanci Jami’ar Najeriya Nsukka sannan ya kara samun ilimin likitanci a jami’ar jihar Ebonyi inda aka rantsar da shi a matsayin likita.[2]
Harkokin Siyasarshi
[gyara sashe | gyara masomin]Nwoye ya fara harkar siyasa duk da cewa shi ɗalibin likitanci ne, inda ya yi ayyuka daban-daban a matsayin jagora a harkar siyasa. Ya yi gwagwarmaya sosai don haɗa kan ɗalibai. Ya zama ɗalibi a ɓangaren likitanci na farko da ya zama shugaban ƙungiyar ɗalibai ta majalisar wakilai daga jami’ar Najeriya Nsukka. Ya kuma samu lambar yabo daga Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Ginigeme Mbanefo, bisa rawar da ya taka wajen yaƙar ƙungiyoyin asiri a makarantar. Ya zama shugaban ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa a watan Disamban shekara ta 2003.
Ya hau mulki a matsayin mataimakin sakataren kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na jihar Anambra a shekarar 2005 kuma a shekarar 2006 yana da shekaru 31 ya zama shugaban kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na jihar Anambra inda ya zama shugaban jam'iyya a jihar mafi ƙarancin shekaru a wata babbar jam’iyyar siyasa a fadin ƙasar nan. A shekarar 2014 bai yi nasara ba a zaɓen jihar Anambra a ƙarƙashin jam'iyyar PDP. [3] A shekarar 2015, ya samu nasara a kotun zaɓe kan ɗan takarar jam’iyyar APGA ( All Progressive Grand Alliance ), Peter Madubueze, ya zama wakilin Anambra Gabas da Yamma a Majalisar Wakilai ta Tarayya. [4]
A shekarar 2016, Nwoye ya bar PDP ya koma APC (All Progressives Congress). [5] Ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani na gwamna na jam'iyyar a kan manyan ƴan siyasa irin su Andy Uba. Ya tsaya takarar gwamnan jihar Anambra a shekarar 2017 tare da Dozie Ikedife Jr. a matsayin abokin takararsa. Sun sha kaye ne a hannun tsohon mai ci Willie Obiano na jam’iyyar APGA.[6]
A shekarar 2022 ya koma jam’iyyar Labour inda ya lashe zaɓen sanatan Anambra ta tsakiya. Ya lashe zaɓen kuma ya fara zama Sanata a watan Yunin shekara ta 2023. [7]
Harkokin Kasuwanci
[gyara sashe | gyara masomin]Shi ne wanda ya kafa kuma ba Babban Darakta na Vintage Consolidated Ltd. [8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Report, Agency (2017-08-27). "Anambra Governorship: Tony Nwoye emerges APC candidate, floors Andy Uba, others". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-08-09.
- ↑ "Politics - Anambra Election: 10 Things You Should Know About APC Candidate, Tony Nwoye". Nigerian Bulletin (in Turanci). 13 November 2017. Retrieved 2022-08-09.
- ↑ "› 2013 › 08 Anambra 2014: Can Tukur save PDP - Vanguard News". vanguardngr.
- ↑ Odunsi, Wale (2015-10-13). "Tribunal declares PDP's Tony Nwoye winner of Anambra Reps election". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-12-03.
- ↑ eribake, akintayo (2016-05-31). "Nwoye dumps PDP for APC". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2022-12-03.
- ↑ vanguard (2017-11-20). "Anambra election: Obaze rejects results as INEC declares Obiano winner". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-10-07.
- ↑ Obianeri, Ikenna (2023-03-04). "INEC officially declares Nwoye winner Anambra North senatorial seat". Punch Newspapers (in Turanci). Retrieved 2024-10-07.
- ↑ "› Bio | Tony Nwoye". tonynwoye.com. Archived from the original on 2021-12-23. Retrieved 2025-04-30.