Jump to content

Tsarin tarayya na Ƙabilanci

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Tsarin tarayya na ƙabilanci ko na kasa da kasa, wani nau'i ne na tsarin tarayya wanda a cikinsa ake ba da ma'anar yankunan tarayya ko na jihohi ta hanyar kabilanci . An samar da tsarin tarayya na ƙabilanci a yunƙurin biyan buƙatun neman yancin cin gashin kan kabilanci da kuma gusar da rikicin ƙabilanci a cikin wata jiha. Ba koyaushe suke samun nasara akan hakan ba: Matsalolin da ke tattare da gine-gine da kuma kula da tarayyar ƙabilanci sun kai ga wasu jihohi ko ɓangarorin jaha ko dai sun wargaje, ko su koma ga mulkin kama-karya, ko kuma su koma ga kabilanci, wariyar launin fata, canjin al’umma, ƙaura daga cikin gida, kawar da ƙabilanci, da / ko ma hare- hare na kabilanci. [1]

Meles Zenawi ya aiwatar da wannan nau'in tarayya daga shekara ta alif ɗari tara da casain da huɗu 1994 zuwa shekara ta 2018 a Habasha . Meles Zenawi da gwamnatinsa sun amince da tsarin tarayya na kabilanci da nufin tabbatar da samun da tsaida daidaito tsakanin dukkanin kabilun kasar Habasha . [2] Hakanan an nuna fasalin tsarin tarayya na kabilanci a wasu ƙasashen ƙetare, ciki kuma har da Indiya, Nepal, Pakistan, Sudan ta Kudu, Yugoslavia, da Afirka ta Kudu - zamanin Apartheid (duba Bantustans ).

  1. "Ethiopia: Understanding Oromia's mayhem after Hachalu's murder". The Africa Report.com (in Turanci). 2021-01-11. Retrieved 2021-10-27.
  2. Alem Habtu. "Ethnic Federalism in Ethiopia: Background, Present Conditions and Future Prospects" (PDF). Western Michigan University. Archived from the original (PDF) on 2006-09-20.