Jump to content

Tunawa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Tunawa shine tsarin kiyaye abubuwa na musamman a ƙwaƙwalwar ajiya, na mutane ko na taro da suka faru. Zai iya zama a nau'i na tunawa, kwatance (adireshi) ko Ƙorafi, ko bikin tunawa ko jimami.

Tunawa da Adalci me ɗorewa

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin ma'anar adalci me ɗorewa, Tunawa yana girmama wadan ya fuskanci cin zarafin 'yancin ɗan adam. Tunawa na iya taimaka wa gwamnatoci su sulhunta rikici ta hanyar nuna kulawa da girmamawa ga wadanda abin ya shafa dakuma hahimatar da abin da ya gabata. Hakanan zasu iya taimakawa wajen samar da tarihi bayanan faruwar abun domin hana sake faruwar cin zarafi.[1]

Tuna baya mafi na iya zama karfin zamantakewa da siyasa a kokarin Gina dimokuradiyya.

Tuna baya har ila yau wani nau'i ne na ƙyale fansa ko ƙoƙarin biyan diyya ga wanda a keyi domin nuna cin zarafin bil'adama da akayi. Manufar su shine niyyar samar da diyya ko fansa sakamakon asarar da wadanda aka azabtar yayi ko ya jimre saboda cin zarafin.

kuma a hukumance suna kallon wanda akaci zarafin matsayin wanda yake da kima kuma wanda zai iya bin haƙƙin shi. Dokar majalisar ɗinkin duniya ta "Yancin ramuwa ko ƙyalewa" sun Fahimci Jajantawa ga waɗanda cin zarafi ya shafa" a matsayin wani nau'in fansa.[2]

Akwai nau'ikan tunawa ga wanda akaci zarafi da yawa da ake amfani da su domin shirya adalci me ɗorewa. Sun haɗa da abubuwan tunawa na gine-gine, gidajen tarihi, da sauran taruka na jimami. Misali, a arewacin Uganda, an kirkiro abubuwan tunawa, taron addu'a na shekara-shekara, da haƙa kabari don tunawa da ka aka gudanar da tsakanin masu adawa da masu goyon bayan Sojojin Tsayayya na sarki.

Wani misalin shine Gidan Tarihi da 'Yancin Dan Adam na Chile, wanda aka kirkira don ajiye tarihin cin zarafi a tsohon mulkin kama-karya na soja a can.[3]

Kalubalen Tuna baya

[gyara sashe | gyara masomin]

Tuna baya na iya tayar da rikici kuma ya janyo wasu haɗura. A cikin yanayin siyasa mara Tabbas tunawa da abubuwan tarihi na iya ƙara sha'awar ramuwa kuma su kara tashin hankali da hargitsi. Su ne matakai masu girma da ake siyasantarwa domin wandan ke da mulki azukatan al'umma

Guy Beiner ya gabatar da ra'ayi na decomemorating dangane da ƙiyayya ga ayyukan tunawa wanda zai iya haifar da hare-hare masu tsanani da kuma lalata ko lalata abubuwan tunawa. Nazarin Beiner ya nuna cewa maimakon kawar da tunawa, decommemorating na iya aiki a matsayin wani nau'i na tunawa mai rikitarwa, ci gaba da sha'awar abubuwan tunawa masu rikitarwa. Halakar abubuwan tunawa na iya haifar da sabunta ayyukan tunawa (wanda Beiner ya lakafta "sake tunawa").

  1. "Truth and Memory". International Center for Transitional Justice (ICTJ). 25 February 2011.
  2. United Nations. (Report). Missing or empty |title= (help)
  3. "Sobre el Museo". Museo de la Memoria y los Derechos Humanos (in Sifaniyanci). 20 April 2012. Archived from the original on 9 February 2015. Retrieved 9 February 2015.