Udokaha Esuene
28 Mayu 1967 - ga Yuli, 1975 - Paul Omu → | |||
| Rayuwa | |||
| Cikakken suna | Udoakaha Jacob Esuene | ||
| Haihuwa | 1936 | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Ƙabila | Mutanen Ibibio | ||
| Harshen uwa | Harshen Ibibio | ||
| Mutuwa | 1993 | ||
| Karatu | |||
| Harsuna | Turanci Harshen Ibibio Hausa Pidgin na Najeriya | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a | ɗan siyasa | ||
| Imani | |||
| Jam'iyar siyasa | Jam'iyyar SDP Peoples Democratic Party | ||
Udokaha Jacob Esuene (1936–1993) wani jami’in Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ne wanda ya yi aiki a matsayin Gwamnan Soja na Jihar Kudu maso Gabas (South-Eastern State), wadda daga baya aka sauya mata suna zuwa Jihar Cross River, daga Mayun 1967 zuwa Yulin 1975, a lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon.
Shi ne gwamna na farko bayan kafa jihar a watan Mayun 1967, lokacin da aka raba tsohuwar Yankin Gabas (Eastern Region) zuwa Jihar Tsakiyar Gabas (East-Central State), Jihar Rivers, da Jihar Kudu maso Gabas.[1]
Esuene, wanda ya fito ne daga kabilar Ibibio, ya kasance matukin jirgi ne kafin a nada shi gwamna na Jihar Kudu maso Gabas.[2][3] Janar Murtala Muhammed ya sallami Esuene lokacin da ya kwace mulki a watan Yulin 1975, an tuhume shi kuma an same shi da laifi na wadatar da kansa ba bisa ka'ida ba yayin da yake ofis, kuma an sallame shi daga soja.[4] Duk da haka, Majalisar Sojojin da ke karkashin jagorancin Shugaban Sojojin na lokacin; Janar Ibrahim Babaginda ta sauya korar. An dawo da matsayi da fa'idodi na Janar Esuene kuma an sake dawowa zuwa 1975. [ana buƙatar hujja]A cikin tseren zaben shugaban kasa na 1993, ya kasance dan takarar tikitin shugaban kasa na Jam'iyyar Social Democratic Party (SDP). [2]
Bayan mutuwarsa, an nada matarsa Helen Esuene Ministan Lafiya, sannan daga baya Ministan Muhalli da Gidaje a cikin Ma'aikatar Shugaba Olusegun Obasanjo tsakanin 2005 da 2007. [2]
Bayanan da aka ambata
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Nigerian States". WorldStatesmen. Retrieved 2010-01-01.
- 1 2 3 Nseobong Okon-Ekong (12 December 2009). "Helen Esuene Emerging From the Shadow of a Famous Husband". ThisDay. Retrieved 2010-02-24. Cite error: Invalid
<ref>tag; name "helen" defined multiple times with different content. - ↑ Nowa Omoigui (24 September 2004). "The Bakassi Story" (PDF). Omoigui.com - Blog of Nigerian Military History. Retrieved 2010-02-27.
- ↑ Empty citation (help)