Ulla Isaksson
|
| |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | Stockholm, 12 ga Yuni, 1916 |
| ƙasa | Sweden |
| Mutuwa | Stockholm, 24 ga Afirilu, 2000 |
| Ƴan uwa | |
| Abokiyar zama |
David Isaksson (en) |
| Karatu | |
| Harsuna |
Swedish (en) |
| Sana'a | |
| Sana'a | marubuci da marubin wasannin kwaykwayo |
| Kyaututtuka |
gani
|
| Mamba |
Royal Society of Arts and Sciences in Gothenburg (en) |
| IMDb | nm0410694 |
Ulla Isaksson (an haife ta a ranar 22 ga watan Yuni, shekara ta 1916, ta kuma mutu a ranar 24 ga watan Afrilu shekarar 2000) marubuciya ce kuma 'yar kasar Sweden. An haife ta kuma ta mutu a garin Stockholm, kasar Sweden . Baya ga gajerun labaru da litattafanta, Isaksson ta kuma rubuta rubutun fina-finai da wasan kwaikwayo.
Farkon Rayuwa da karatun ta
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Isaksson a garin Stockholm a shekara ta 1916, ta kasance 'yar Knut Lundberg da Greta Brasch, mahaifiyar ta, wacce ta kasance memba na cocin Immanuelkyrkan; wanda hakanne ya sa Isaksson ta taso da hali mai karfi na addini, wanda ya nuna a litattafan da ta rubuta na farko.[1] Isaksson ta kammala karatun ta daga makarantar sakandare a 1937; daga nan sai ta fara karatun falsafa. A shekara ta gaba ta auri David Isaksson . An ba ta digiri na girmamawa na Dokta na falsafar a shekarar 1978.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar 1940 Isaksson ta yi labari Trädet kuma a cikin 1952 ta sami nasarar ta a bainar jama'a ta hanyar labarin Kvinnohuset, wanda Erik Faustman ya yi fim a kai.[2] Ingmar Bergman ta daidaita littafinta na Det vänliga, värdiga (1954) a cikin shekarar 1958, bayan haka ya ɗauki Isaksson inda ta rubuta wasan kwaikwayo na fim ɗin Jungfrukällan (1960). Littafin nata Klänningen Vilgot Sjöman ne ya daidaita shi a cikin 1964, Paradistorg ya zama fim a shekarar 1977, wanda Gunnel Lindblom ya jagoranta, kuma Bergman ya yi fim ɗin a talabijin na labarin littafin ta De två saliga (1962).[2]
Yawancin litattafan Isaksson na shekarun 1950 suna dauke da matsalolin addini, kamar yadda a ƙarshen littafin Havet da Dit du icke vill, inda a ciki aka kwatanta gwajin sihiri na ƙarni na 17 a ƙauyen Dalarna na tushen ƙa'idodin zamani. A cikin litattafanta na baya tayi rubutun ta na farko game da rikice-rikicen addini . A cikin litattafan ta na baya kuma ta jagoranci bincike kan abubuwan sha'awa, matsalolin duniya, batutuwan mata, da tarbiyyar iyaye [3].
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Nordisk Kvinnolitteratur". Larsson, Lisbeth. Retrieved 2014-03-24.
- ↑ 2.0 2.1 "Ingmar Bergman". Holmgren, Jan. Retrieved 24 March 2014.
- ↑ "Albert Bonniers Förlag". Wägner, Elin. Retrieved 24 March 2014