Umar dan al-Khattab

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Umar bin Khaddab)
Jump to navigation Jump to search
Simpleicons Interface user-outline.svg Umar dan al-Khattab
Abu bakr2.jpg
Khalifofi shiryayyu

ga Augusta, 22, 634 - Nuwamba, 3, 644
Sayyadina Abubakar - Sayyadina Usman dan Affan
Rayuwa
Haihuwa Makkah, 585 (Gregorian)
ƙasa Khulafa'hur-Rashidun
ƙungiyar ƙabila Larabawa
Mutuwa Madinah, Nuwamba, 3, 644
Makwanci Masallacin Annabi
Yanayin mutuwa kisan kai (stab wound (en) Fassara)
Template:P Pirouz Nahavandi (en) Fassara
Yan'uwa
Mahaifi Khattab ibn Nufayl
Mahaifiya Hàntama bint Hixam
Abokiyar zama Umm Kulthum bint Ali ibn Abi Talib (en) Fassara
Atiqa bint Zayd (en) Fassara
Umm Kulthum bint Asim (en) Fassara
Yara
Siblings
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a statesperson (en) Fassara
Aikin soja
Ya faɗaci Badar
Yaƙin Uhudu
Yaƙin gwalalo
Battle of Khaybar (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Signature Believed To Be Of ʿUmar B. Al-Khaṭṭāb.png
Rashidun Caliphs Umar ibn Al-Khattāb - عُمر بن الخطّاب ثاني الخلفاء الراشدين.svg

Umar, ko kuma Omar a Larabci kuma عمربن الخطاب Umar Ibn Al'Khattab hausa Umaru dan Kaddabi Allah ya yarda da shi.

Daya ne daga cikin manyan Sahabban Annabi Muhammad (s.a.w), kuma shine na biyu cikin halifofin Musulunci. Yana daya daga cikin Halifofinnan guda Hudu na Halifancin Annabta, sannan kuma yana daya daga cikin sahabbai goman da Annabi yayima bishara da au yan Aljanna ne tun suna Duniya. Umar ya kasan ce mai taka tsantsan tare da gudun duniya, kasancewar sa mutumin da yayi kaurin suna kwarai wajen rarrabewa tsakanin gaskiya da karya be yasa akayi masa lakabi da Al'farook.


Umar ya kasance babban jagora, kuma dukkannin hadisai ruwayar shi ana kallonsu a matsayin hadisai ingantattu.

Farkon rayuwar sa[gyara sashe | Gyara masomin]

An haifi Sayyadina Umar a birnin Makka daga kabilar Banu Adi. Mahaifinsa Al'Kattab ibn Nufayl mahaifiyar sa itace Hantama bint Hisham, yar kabilar Banu Makhzun. A lokacin kuruciyar sa. Umar ya kasance yana taya mahaifin sa kula da rakuman sa n.

Tun a lokacin kuruciyar sa , Sayyadina Umar ya kasance mai sha'awar koyon rubutu da karatu bw. Hakane yasa ya samu kwarewa wajen iya rubutu da karatu, harma ya zama gagara badau wajen iya rubuta wake-wake kamar yadda larabawa suka shahara wajen rubuce rubuce na wake-wake a zamanin kafin zuwan Musulunci. Ana danganta Basirar Umar da gado daga wajen Mahaifin sa.

Hakanan dai a zamanin kuruciyar Sayyadina Umar, ya zama babban dan kaauwa inda yake zuwa kasashen Romaniya da Farisa fatauci. Sai dai harkar kasuwancin bata karbe shiba sosai kamar sauran takwarorin sa.

Zamanin Annabi Muhammad (s.a.w)[gyara sashe | Gyara masomin]

Takobin Sayyadina Umar

Kafin Musuluntar sa[gyara sashe | Gyara masomin]

A shekara ta 601M. Annabi Muhammad (s.a.w) ya fara kira zuwa ga musulunci, kamar sauran mutanen makka shima Umar bai bayar da gaskiya ga Annabi ba da farko. Harma ya kasance babban mai adawa da Annabi (s.a.w). Sakamakon takurawar da Umar da sauran kafiran makka na lokacin sukema Annabi da wadanda suka musulunta ne yasa Annabi (s.a.w) ya umarci wasu daga cikin musulmai da suyi hijira zuwa kasar Sham. Lokacin da sahabbai sukabi Umarnin Annabi (s.a.w) ne sai ganin haka ya kara tayar da hankalin Sayyadina Umar harma ya fara shirya kashe Annabi Muhammad (s.a.w).

Musuluntar Sayyadina Umar[gyara sashe | Gyara masomin]

Umar ya shiga musulunci ne a ahekarar 616M. wato shekara daya kenan bayan hijirar Sham. Ibn Ishak, yayi rubutu a lattafin sirar shi game da Musuluntar Sayyadina Umar.

Ga tarihin Daga gidan ‘yan- uwansa kai tsaye ya wuce zuwa Darul-Arqam da ke karqashin dutsen Safa wanda kuma nan Manzon Allah (s.a.w) ya samu mafaka. Da isar Sayyadina Umar (r.a) wannan gida sai ya kwankwasa kofa. “ Sai mai gadin Gidan yace Wanene yake kwanKwasa kofar?” Sayyadina Umar ya amsa da “Umar ne”. . Da mai gadin ya leko ya gan shi da takobi zare, sai ya yi shakkar bude kofar. . Sai Sayyadina Hamza (r.a) ya ce da shi, “Bude masa idan da alheri ya zo muna maraba da shi idan kuma da akasin haka ya zo ai sarkin yawa ya fi sarkin karfi”. . Aka bude masa ya shiga, Da shigarsa sai Sayyadina Hamza (r.a) ya dakume shi ya ce da shi “Umar, me ke tafe da kai?” . Sauran Musulmi kuma suka zazzare takubbansu suka yi masa kawanya (suka zagayeshi) da zimmar ko da zai tada jijiyar wuya sai su cimmasa. . Da jin wannan hayaniya sai Manzon Allah (s.a.w) ya fito daga dakinsa ya ce da Sayyadina Hamza (r.a) “kyale shi ya karaso gare ni”. . Da Sayyadina Umar (r.a) ya kusanci Manzon Allah (s.a.w) sai Manzan Allah (s.a.w) ya ce da shi “Wane irin lokaci za ka dauka kana fada da Musulunci? Har yanzu lokacin da za ka karbi Addinin gaskiya bai yi ba?” , Sai Sayyadina Umar (r.a) ya ce: “Hakika lokacin da zan karbi Addinin gaskiya ya yi. Na zo ne na yi imani”. . Sai Manzan Allah (s.a.w) ya mikar da hannunsa shi kuma Sayyadina Umar (r.a) ya dora nasa a kan Na Manzan Allah (s.a.w) cikin ladabi sannan ya ce “Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Muhammadu Manzon Allah ne”. . Da jin haka sai Musulmi suka ce “Allahu Akbar” cikin jin dadi. Sai Manzan Allah (s.a.w) ya rungume shi, sannan sauran Musulmi ma suka rika rugumarsa daya bayan daya. . Sayyadina Umar (r.a) shi ne na arba’in (40) a shiga Musulunci. A wannan ranar da Sayyadina Umar ya Musulunta har Mala’ika Jibrilu (a.s) sai da ya taya Manzan Allah (s.a.w) murna saboda musuluntar sayyadina Umar (r.a). Ya ce da shi, “Ya Manzan Allah jama’ar Aljanna suna murna da musuluntar Umar (r.a) kuma suna mika sakon taya murna gareka”. . Sayyadina Umar (r.a) Saboda tsananin jin dadin musuluntar da ya yi saida ya rika bi kwararo-kwararosako-sako a Makka yana shelanta Musuluntar sa.

Hijirar Sayyadina Umar[gyara sashe | Gyara masomin]

Sakamakon tsanani yayi yawa daga wajen kafiran Makka ne sai Annabi Muhammad(s.a.w) ya umarci sahabbai da suyi hijira zuwa birnin da ake kira Yazrab a wancan lokacin wanda daga bisani aka mayar dashi Madina. Sai sahabbi suka runka bin dare suna sulalewa daga garin Makka saboda gudun cutarwa daga kafiran Makka na wancan lokacin. Amma shi Sayyadina Umar a fili kuma da rana yayi tasa hijirar har ma yana fadin Ina wanda yake son matar sa ta zama bazawara to ya zo ya hana ni Umar yai hijirar sa tare da rakiyar dan dan'uwan sa da kuma dan'uwansa Sa'id dan Zaidu

Rayuwar sa a Madina[gyara sashe | Gyara masomin]

A Madina kuwa, Umar (R.A) na daya daga cikin zaratan mayaka wadanda su kayi ruwa da tsaki wajen kare martabar Musulunci da ruguza abokan fadansa. Ya kusanci Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har ya kai matsayin wazirinsa na biyu. A shekara ta uku bayan hijira sai Allah ya karrama shi da surukuta da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama inda Manzo ya nemi auren 'yarsa Hafsah, aka ba shi ita, aka daura aure, sai ta zama ita ce ta uku daga cikin matansa bayan rasuwar uwargidansa Khadijah. A wurare da dama Umar (R.A) ya dace da hukuncin Alkur'ani kafin saukarsa. Misali, Umar ne ya ba da shawarar kada Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya halarci sallar jana'iza a kan munafukai, kuma sai AlKur'ani ya sauka da wannan hukuncin. Haka kuma Umar (R.A) ya bai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shawarar ya hana mutane shiga gidansa, kuma Allah ya saukar da wahayi a kan haka. Shi ne kuma ya nemi a shamakance mata daga maza ta hanyar amfani da hijabi, sai Allah ya saukar da wahayi a kan haka. Ya bada shawarar a kashe fursunonin Badar, Allah ya karfafi ra'ayinsa a Suratu Ali Imran. Wadannan duka suna nuna irin kaifin basirarsa da kusancinsa ga Allah da sanin abin da Allah yake so da wanda ba ya so.

Khalifancin Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | Gyara masomin]

Taswirar daular Musulunci a zamanin Kalifancin Sayyadina Umar R.A

Sayyadina Abubakar (R.A) ya ayyana ma Musulmi Umar a matsayin wanda zai gaje shi bisa ga shawararsu. Don haka da Abubakar ya cika nan take mutane su kayi masa mubaya'a kuma ya kama aiki. Wani muhimmin abinda ya kamata a sani game da khalifancin Umar (R.A) shi ne kwarjinin da yake da shi matuka a idon jama'a. Amma kuma duk da haka talakawa sun more a lokacin khalifancinsa, domin kuwa ya kasance yana kula da al'amuransu ta ko wane fanni. Bayan dai kulawarsa da tsayuwar addini, Umar (R.A) yana kulawa da jin dadin rayuwar jama'a da inganta lafiyarsu da gyaruwar tattalin arzikinsu da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya a tsakaninsu.

Irin kwarjinin da Umar (R.A) yake da shi a zukatan jama'a ya sanya wata mata ta yi barin cikinta a lokacin da ta samu labarin an kai kararta ga Sarkin Musulmi Umar. Wannan ya sanya Umar ya tara jama'a ya nemi shawararsu a kan wannan abinda ya faru don sanin ko diyya ta wajaba a kansa. Ya kuma yi aiki da ra'ayin Sayyadina Ali (R.A) na biyan diyyar jinjirin da aka rasa. Ba za mu yi mamakin wannan mata ba idan muka san cewa, manyan Sahabbai irin su Zubairu dan Awwam da Sa'adu dan Abu Waqqas sukan tafi wajen Umar da nufin gaya masa wata magana ko gabatar da wata bukata, amma su je su dawo ba su samu damar yin haka ba saboda kwarjininsa da ya cika masu fuska. Ibnu Abbas ma duk da irin kusancin da yake da shi ga Umar amma ya yi shekara daya yana son ya tambaye shi game da wata aya bai samu damar haka ba saboda kwarjininsa.

Wani wanzami kuma ya saki iska saboda tsoro a lokacin da Sarkin Musulmi Umar ya yi tari shi kuma yana yi masa aski. Umar (R.A) da kansa ya kan damu wani lokaci da yadda jama'a suke fargabarsa, har ma ya kan ce, Ya Allah! Ka san na fi tsoronka fiye da yadda su ke tsorona.

A game da kulawarsa da talakawa kuwa, Umar (R.A) ya shahara da ziyarar sa ido wadda yake yi a cikin dare yana sintiri a tsakanin hanyoyi da gidaje don sanin halin da kasarsa ta ke ciki. A cikin irin wannan ziyarar ne yake gano idan akwai barayi ko wasu miyagu ko mabarnata masu fakewa a cikin duhun dare su yi aikin assha, ko kuma bako wanda bai samu masauki ba.

Kisan Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | Gyara masomin]

Makwancin Kalifa Umar a masallacin Annabi (s.a.w) Madina. Tagar farko daga dama tana nuna Kabarin Sa

A shekarar 144M. ne wani bawa bafarishe maisuna Abu Lulu ya kai hari kan Sayyaduna Umar (r.a). Dama ansha shirya kashe Umar watanni kafin aiwatar da kisan. Adadidai lokacin da Sayyaduna Umar yake jagorancin sallar asuba ne maharin yazo da wuka ya daddabawa Sayyaduna Umar (r.a) har sau shida nakarshe ne ya daba masa ita a makogwaron sa. A kokarin sauran mutanen na ganin aun kama maharin Lulu ne sai da ya raunata mutum goma sha biyu. Daga baya shida ko tara na mutanen Allah ya karbi rayuwar su dalilin wannan raunin. Shima Lulu daga bisani kashe kansa. Sayyadina Umar ya rasu sakamakon raunukan da maharin wato Luli (l.a) yayi masa bayan kwana uku. Wato ranar Laraba ta 26 ga watan Dhu al Hijja shekara ta 23 bayan hijira. Da Umarnin Aisha ne aka binne mahaifin ta wato Sayyaduna Umar a cikik dakinta gefe kadan da Makwancin Annabi Muhammad (s.a.w) da kuma na Sayyadina Abubakar(r.a).

Iyalin Sayyadina Umar (r.a)[gyara sashe | Gyara masomin]

Sayyadina Umar(A.S) Ya auri mata Tara ne a iya rayuwar sa. Yana da yaya goma sha hudu, goma maza hudu mata.