Umar ibn Ali
| Rayuwa | |
|---|---|
| Mutuwa | Karbala, 680 (Gregorian) |
| Makwanci |
Imam Husayn Mausoleum (en) |
| Ƴan uwa | |
| Mahaifi | Sayyadina Aliyu |
| Mahaifiya | Al-Sahba bint Rabi'a |
| Ahali | AlHusain dan Aliyu bin Abi Talib |
| Sana'a | |
| Aikin soja | |
| Ya faɗaci | Yaƙin Karbala |
| Imani | |
| Addini | Musulunci |
Umar bn Ali ( Arabic ), yana ɗaya daga cikin ‘ya’yan Ali bn Abi Talib wanda ya raka dan uwansa Husaini bn Ali zuwa Karbala an kashe shi a ranar Ashura. An ce ban da shi (wanda ake ce masa Umar al-Asghar) Ali ya haifi wani dansa Umar al-Akbar, mahaifiyarsa ita ce Ummu Habib Al-Sahba, ba ta halarci taron Karbala ba.
Zuri'a
[gyara sashe | gyara masomin]Wasu kafofin Sunni sun ambaci Umar a matsayin Umar al-Akbar wanda sunan sa shine Abu al-Qasim ko Abu Hafs. Wasu kafofin tarihi [waɗanda?] sun ba da rahoton sunan mahaifiyarsa a matsayin Al-Sahba (Umm Habib), 'yar Rabi'a al-Taghlibi. Wasu sun ambaci sunanta Layla bint Mas'ud al-Darami. Masanin Sunni al-Fakhr al-Razi ya ambaci cewa Umar shi ne ƙaramin ɗan Imam Ali.
A Yaƙin Karbala
[gyara sashe | gyara masomin]An ruwaito cewa Umar ya yi kukan yaqi a ranar Ashura, ya kai wa maqiya hari. Ya afkawa Zahr wanda ya kashe ɗan uwansa ya kashe shi. Malamin fikihu Akhtab Khwarazm ya ruwaito shahadarsa bayan shahadar dan uwansa Abubakar. An ce da farko dokinsa ya faɗi sannan suka yi shahada.