Umar Ibn Aliyu Babba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Umar ibn aliyu babba)
Jump to navigation Jump to search

Umar Ibn Aliyu Babba (1881 – 1891) shine Kalifa Umaru Dan Aliyu Babba ne wanda shine Kalifa na hudu (4) a sokoto. Kuma jika wajen Muhammadu Bello Shehu Usman Dan Fodio. An haifeshi a Wurno a shekarar 1877. Umar Ibn Aliyu Babba ya fito daga ahalin Toronkawa (Torobe) dangin Fulani.[1]

Karatu[gyara sashe | Gyara masomin]

Kalifa Umar kamar sauran yayan sarki ya taso ne a gidan ilimi, al’ada ne na shugabannin addini su gina makarantu duk inda suke. Saboda haka Wurno, Salame , Chimmok da Sokoto duk garuruwa ne na karatu.

Tsaiko[gyara sashe | Gyara masomin]

An samu tsaiko wajen hada tarihin Kalifa Umar inda kusan kowa ke boye tarihinsa. Dayawa daga cikin mutane sukan fadi cewa basu san komai a kanshi ba. Wannan harda yan uwanshi na jiki ma sun nuna cewa basu san komai akan shi ba.[1]

Sarauta[gyara sashe | Gyara masomin]

Rasuwar Kalifa Mu’azu, ta bada daman nada wani Kalifa kamar yadda addini ya tanada. Mutum biyar ne suka nemi Kalifanci a lokacin. Inda a cikin su Allah ya zabi Kalifa Umar ya bashi mulki. An nada Umar Kalifa a shekarar 1881 a Sokoto. A lokacin yanada shekara 59.

An nada shine a Ranar Lahadi 9 ga watan Zulkida a masallacin Kalifa Bello.

Rasuwa[gyara sashe | Gyara masomin]

An ruwaito cewa Kalifa Umaru ya rasu ta sanadiyar harbi da doki ya masa a lokacin da yake shafanshi, da yammaci. Ya rasu a fadar sarkin Kiyawan Kaura Namoda a Laraba 25 March, 1891. A lokacin yana da shekara (69). Yayi mulki na tsawon shekara (9) da wata goma (10).[1]

Bibiliyo[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. ISBN 978-978-956-924-3. OCLC 993295033.
  • The Sokoto Caliphate : history and legacies, 1804-2004. Bobboyi, H., Yakubu, Mahmood. (1st ed ed.). Kaduna, Nigeria: Arewa House. 2006. ISBN 978-135-166-7. OCLC 156890366.
  • Smaldone, Joseph P. (1977). Warfare in the Sokoto Caliphate : historical and sociological perspectivesISBN0-521-21069-0OCLC2371710

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 Sultans of Sokoto : a biographical history since 1804. Abba, Alkasum,, Jumare, I. M. (Ibrahim Muhammad),, Aliyu, Shuaibu Shehu,. Kaduna, Nigeria. p.p 171-191 ISBN 978-978-956-924-3.