Jump to content

Umuerum

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Umuerum

Wuri
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Umuerum, wanda aka fi sani da Umuolum, wani gari ne a cikin Ƙaramar Hukumar Ayamelum a Jihar Anambra, Najeriya.

Garin Umuerum na yankin iyakar Kogin Omambala da Kogin Ezu. Garin ya ƙunshi ƙauyukan Ukpambaka / Umunkwele, Ayigo, Umuodu / Umuoli, Umuerike / Obinagu da Otu-oyibo (yanki na gari). Garin ya yi iyaka da makwaftan garuruwan garin da suka haɗa da ; Anaku, Omor, Umumbo da Awba (ovemmili).[ana buƙatar hujja][1]

Ana noman doya, shinkafa, garin rogo, masara da sauran kayan lambu iri-iri a garin. Ana samun kifi masu kyua dalilin koguna da tabkunan garin. A cikin shekarun 1970s kamfanonin haƙar mai, sun gano man fetur da iskar gas da yawa a yankin, sai dai har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta yi wani abu akai ba.[2]

  1. Emeka Mamah, Vincent Ujumadu & Ishola Balogun (March 5, 2013). "Ezu River: The unending mystery". Vanguard. Retrieved March 5, 2013.
  2. Imaobong Ekpo, Ofonmbuk Obot andGift Samuel David (December 2018). "Impact of oil spill on living aquatic resources of the Niger Delta region: A review". Journal of Wetlands and Waste Management.

Hanyoyin hadi na Waje

[gyara sashe | gyara masomin]