Umuganuro
| Iri | ranar hutu |
|---|---|
| Ƙasa | Burundi |
Umuganuro ya kasance biki ne na gargajiya a ƙasar Rwanda wanda aka keɓe don murnar girbi da kuma gabatar da addu’o’i na albarka ga kakar noma ta gaba. Yana daga cikin bukukuwan tarihi da ke nuna haɗin kai, godiya, da al’adun ƙasar Rwandawa. Yadda ake gudanarwa.[1]
Yadda ake gabatar da bikin
[gyara sashe | gyara masomin]Ana fara shirin bikin da addu’o’i da shirya abubuwan gargajiya da abinci na al’ada, musamman hatsi kamar dawa da masara. A ranar bukin, mutane daga sassa daban-daban na ƙasar suna haɗuwa a cikin gari ko wuraren ibada don gudanar da taro. Ana gabatar da waƙoƙi da raye-rayen gargajiya, gami da nune-nunen al’adun ƙasar Rwanda.
gabatar da bikin girbi
[gyara sashe | gyara masomin]An shirya girbin kaka a matsayin alama na godiya ga Ubangiji da kakannin ƙasa Ana gabatar da abinci ga shugabanni da manyan gari a matsayin sadaukarwa don albarkar kakar noma ta gaba.[2]
Ƙarfafa Zumunci
[gyara sashe | gyara masomin]Bukin yana kasancewa wani lokaci na haɗin kai, inda mutane ke cin abinci tare, suna hira da sada zumunta tsakanin iyalai da al’umma.