University teacher
Malamin Jami'a shine mutum wanda yake aikin koyar da ɗalibai a jami'a . malami ne wanda jama'a suke ganin shi da kima fiye da sauran malaman ƙananun makarantu musamman Saboda yadda yawancin su suka kai wani matsayi na ilimi da ake musu laƙabi da sunayen girmamawa irinsu,Dakta da Farfesa. Rayuwar malaman Jami'a tana burge mutane da yawa saboda tasirin su cikin al'umma dakuma yadda ake ganin suna gudanar da rayuwar su cikin tsari me kyau da tsafta duk da a zahiri abinda ake basu bekai yanda jama'a ke tsammani ba.Aikinsu anayi mishi kallon me sauki duk da cewa a zahiri bashi da sauki kamar yadda wani malamin jami'ar Bayero a Kano yafada saboda aikin da yake buƙatar binciken ƙwa-ƙwaf kafin malami yazo ya tsaya gaban ɗalibai da nufin basu darasi.[1]
Albashin Malaman jami'a be kai yawan yanda jama'a suke tsammani ba musamman a Nigeria domin kuwa ko a kwana-kwana nan wani malamin jami'a daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya ya fito ya bayyana yanda albashinsu baya isar su ɗaukar nauyin iyalansu Saboda haka al'umma da kungiyoyin kare haƙƙin bil adama sukayi ta kiraye-kirayen karama Malaman albashi duba da irin gudunmawar su a cikin al'umma
- ↑ Academic Excellence