User:Abuihisan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
                                               HUDUBARMU TA YAU


                            DAGA MIMBARIN ABU HURAIRA (RA), SOKOTO

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

An gabatar da ita a 7 ga Rabi’ Awwal 1432H (11/2/2011)

Ya al’ummar musulmi! Da yawa daga cikin mu suna koken bushewar zuciya. Zaka ji wani na cewa, imanina ba ya da karfi, ba ni jin kuzari in lokacin sallah ya yi, ban sha’awar karatun alkur’ani, ko na so in tashi sallar dare ban iyawa, iyakata da himmar ibada lokacin azumi. Wa’azi ba ya kama zuciyata da dai sauran irin wadannan koke-koke. Akwai abubuwa da dama da muke yi masu nuna raunin imani a cikin rayuwarmu ta yau da kullum.

Akwai yawan sabon Allah. Da farko in mutum ya yi shi zai rinka jin damuwa a zuci amma idan ya yi yawa a hankali sai mutum ya fara sabawa da shi ya daina damuwa. Idan ba a ci sa’a ba ma sai ya zan bai damu da bayyana shi ba, sai ya fada cikin wani babban tarko na shedan don manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yana cewa, Duk al’ummata suna cikin rahama ban da masu bayyana sabo. Yana kuma daga cikin alamar raunin imani musulmi ya ga an saba ma Allah bai ji ya damu ba. To, ina kuma ga ace ya ji dadi ko ma har ya bada gudunmawa? Akwai kuma rashin kyautata ibada ta hanyar daukuwar hankali da shagaltuwa a cikin ta. Sai ka ga mutum na sallah bayan liman amma bai ko san raka’a nawa aka yi ba. Yana biye kawai in an duka ya duka ba don ya san abinda yake yi ba. Idan mutum na sauraren alkur’ani ba zai mayar da hankali ya ji umurnin Allah ba ko ya ji gargadi ko wa’azi ko jan hankali. Mafi girman wa’azi shi ne mutuwa. Amma a yau ko makabarta aka je ba zaka ga wani alamun karaya ga mutane ba. A nan ma aka sace handset din wani!

Daga cikin abinda ke bayyana raunin imani mutum ya kasa damuwa da kubcewar aikin lada amma yana damuwa in ya yi hasarar kudi. A da magabata in wanin su ya rasa raka’a ta daya a sallar jam’i ya isa ya bakanta ma sa rai tsawon wunin nan ko abin da ya fi. Dubi yadda annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce game da masu jinkiri daga sahun farko a sallah: (لا يزال قوم يتأخرون عن الصف الأول حتى يخلفهم الله في النار) رواه أبو داود رقم: 679 وهو في صحيح الترغيب رقم 510 Mutane ba zasu gushe ba suna jinkiri daga sahun farko har sai Allah ya bar su cikin wuta. Da Allah Ta’ala ya bada labarin annabawa; Ayyub da Isma’il da Idris da Yunus sai ya ce: Sun kasance suna gaggawar shiga cikin ayyukan alheri kuma suna kiran mu cikin kwadayi da tsoro, kuma sun kasance masu kankan da kai gare mu. Suratul Anbiya'i: 90.

Yana daga cikin abinda ke bayyana raunin imani mutum ya sa ma ransa son girma, da sha’awar mulki da fatar kullum ya zama gaba ga mutane. Wannan bai tsaya ga ‘yan siyasa kawai ba, har da malamai masu karantar da addini. Misali, wani shi bai taba yarda ya zama mamu ba sai dai har abada ya zama liman, ko kuma in za ayi magana dole sai shi zai yi, ko yana son in ya zo a tashi tsaye. Manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yana cewa, Duk wanda ke son a tashi tsaye in an gan shi, to ya nemi mazauninsa a cikin wuta. Akwai kuma rowa. Tana daga cikin manyan abubuwan da mummuni ba ya sifaituwa da su. Tarbiyyar alkur’ani ita ce, mutum ya dauka arziki na Allah ne kuma duk inda ya ba da shi ya bayar ne don bayinsa su amfana kuma addininsa ya daukaka.

Daga cikin alamun raunin imani akwai cika baki da fadin abinda ba a aikatawa. Allah Tabaraka Wa Ta’ala na cewa : Ya ku wadanda suka yi imani don me kuke fadin abinda ba ku aikatawa? Abin kyamar ya yi girma a wurin Allah ku rinka fadin abinda ba ku aikatawa. Yawan jayayya da rigingimu a kan lamurran addini shi ma yana daga cikin alamun raunin imani. Akwai kuma rashin kula da al’amarin musulmi da raunin ‘yan uwantaka ta yadda wani ma ba shi jin wannan ‘yan uwantakar a zuciya. Bai damu da al’amarin musulmi ba a ko ina suke sai wadanda shi yake da wata dangantaka da su.

Ya ku al’ummar musulmi! Dole ne kowa ya kula da ci gaban imaninsa da inganta shi. Mu sani cewa, imani ba batun zuci ba ne kawai da akida. Aiki ma yana cikin imani. Ibada tana cikin imani. Kyakkyawar zamantakewa da kyautata hulda da shi da sauran dabi’u na gari kamar fadin gaskiya da kiyaye amana da jin kunya da kamun kai da tausaya ma jama’a duk suna cikin imani. Kuma kowane aikin imani ka kara imaninka zai karu daidai yadda ka kara shi. Kamar yadda sabo kowane iri yana rage kaifin imani.

Ya ku bayin Allah! Daga cikin matakan da ke kaifafa imani akwai:

1. Karatun alkur’ani a cikin natsuwa da tuntunin ma’anarsa. Saboda alkur’ani waraka ne ga kowace cuta. Magabata ba su taba sakaci ba da wannan. Al-Hafiz Ibnu Kathir ya fadi a cikin tafsirin Suratut Tur: 7-8 cewa, sayyidina Umar ya yi rashin lafiya har ana zuwa duba shi a kan karanta wadannan ayoyi biyu. Karanta yanayin magabata shi kan sa a yayin da suke karanta alkur’ani abu ne mai sa kara kaifin imani. Wani daga cikin su ma yakan kashe dare guda dukkansa yana bitar wata aya yana wa’aztuwa da abinda ke cikin ta. 2. Karanta ilimin akida tatacciya wadda aka debo daga alkur’ani da hadisi. A cikin ta ne mutum ke sanin girman Allah da daukakarsa ta hanyar sanin siffofinsa masu ban sha’awa da sa son Allah da sanin girmansa. Haka ma ilimin shari’a kowanne. Mai zuwa makaranta da wuraren da ake bayyana maganar Allah da manzo ba yadda za ayi ya zama daya da wanda bai zuwa ta karfin imaninsu. Shi ya sa yake da kyau malamai magadan annabawa su ci gaba da dagewa wajen buda majalisu na karantar da akida da kaifafa imani da kara ma musulmi karfin sanin Allah madaukakin sarki. 3. Daga cikin matakan kaifafa imani akwai tuna mutuwa wadda kan iya zuwa ko wane lokaci. Agogon da ke lisafin rayuwarka baya baya yake tafiya. Kuma ba ka san ko karfe nawa yake gwadi ba. Wani wata daya ya rage ma sa, wani sati daya, wani wuni daya. Kai, wani fa sauran sa awa daya amma bai sani ba. Zuwa ziyarar makabartu da yi ma su addu’a na kaifafa imani shi ya sa manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yi mana izini bayan da ya hana mu. Ambaton mutuwa a cikin alkur’ani yana dawa. Da ita ne Allah yake mana wa’azi kodayaushe. Haka ma abinda ke bayan mutuwa. Karanta surar Kaf da Waki’ah da Alkiyama da Wal Mursalat da Amma Yatasa’alun da Idhas shamsu kuwwirat da makamantansu yana taimakawa ga taushin zuciya da lankwasa rayuwa zuwa ga da’ar Allah. Haka kuma yana rage ma mutum kwadayin duniya wanda shi ne babban abinda ke cin imani, ya bushe zuciya. 4. Akwai wasu ayyuka na zukata da ke kaifafa imani, kamar son Allah da son manzo da son muminai. A kullum idan zuciyar musulmi ta rataya ga wanin Allah ko ta cika da son wanda Allah bai so to, ta kan yi rauni a dalilin wannan. Kamar kuma mika wuya ga Allah da yarda da kaddara da dogaro ga Allah da gode ma sa. Duk wadannan suna kaifafa imani. 5. Daga cikin matakan kaifafa imani, mutum ya fadada ayyukansa na bidar lada. Kofofin aljanna yawa gare su. Haka ma ayyukan da ke sa a kai gare ta. Saboda haka kar ka dauki aiki guda daya. Yi kokari ka kwankwasa kowace kofa, ba ka san wacce ce zaka yi dace a bude ma ba. Amma a lura da yin gaggawa, kada a bata lokaci kamar yadda Allah ya ce: Ku yi gaggawa zuwa wajen neman gafarar ubangijinku da samun aljannar da ta yi fadin sama da kasa. A kuma dage. Kada a fara a bari. Sannan a sa himma da kokari da kwazo da nacewa amma fa ba tare da an kai ga kosawa ba. Yana da kyau ka saba da wata ibada ta nafila tsayayya wadda ba ka fasawa a cikin kowane irin yanayi. Idan kuma aka saba da wata ibada to, duk lokacin da uzuri ya gitta sai a samu wani lokaci a ramka ta. Wannan ita ce dabi’ar manzonmu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Dangane da maganar ibada dole ne mu sani cewa, Allah ba ya karbar duk wani aiki da mutum zai yi sai in ya kasance bisa ga koyarwar manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Duk aikin da bai yi daidai da sunnah ba shi ake kira bidi’a. ibada ta kan iya saba ma sunnah ta dayan fuskoki guda shida: • Jinsinta ya yi daidai da na manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. • Adadinta ma haka kamar rakao’i da tasbihin bayan sallah • Wurin da za ayi ta idan mai kebantaccen wuri ce kamar hajji • Haka kuma lokaci kamar sallolin farilla • Siffar da aka yi ta kamar sallar dare da makamantan ta. • Dalilin yin ta. Misali ana hamdala in an yi atisshawa bisa ga karantarwar manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Idan wani ya yi tasbihi ko salati a nan ya yi bidi’a. Haka duk wata ibada da mutum zai jingina ga wani dalili ya mayar da ita buki ko makoki ko makamancin haka. A cikin hasken wannan bayani zamu fahimci abinda mujaddidi dan Fodiyo Allah ya yi ma sa rahama ya fadi na cewa, bukukuwan mauludi bidi’a ne da shiga gaban manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Akwai dalilai bakwai da ke sa mu kauce ma wadannan bukukuwan da mutane ke yi a cikin wannan wata: 1. Kasancewar ba su da asali a cikin addini. Don kuwa manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam bai yi su ba, bai yi umurni da ayi ba. Haka ma duk halifofinsa shiryayyu da magabata mutanen kirki. Ba shi kuma yiwuwa a ce mun fi wadancan bayin Allah sanin shiriya ko son manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. 2. An kago su ne a zamanin raunin addinin musulunci, sa’adda ‘yan shi’a suke mulki. Kuma suka tilasta a rufe shaguna da wuraren aiki a fito a bayyana murnar haifuwar manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. 3. Wadannan bukukuwan – tare da cewa, ba a umurce mu da yin su ba – sun yi kama da wadanda kiristoci ke yi ma Annabi Isah Alaihis Salam alhalin an umurce mu da mu saba ma su. 4. Babu wata tsayayyar rana da aka tabbata cewa ita ranar haifuwar manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Da yawa ma daga cikin masana na musun ranar 12 ga Rabi’ul Awwal. 5. In da bukukuwan masu kyau ne to, yin su don tuna ranar da aka aiko shi manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya fi dacewa don da aiko shi din ne rahamar Allah ta tabbata ga talikai kamar yadda ya ce: Ba mu aiko ka ba sai don ka zan rahama ga talikai. 6. Za ka ga akasarin masu mayar da hankali ga wadannan bukukuwan ba su ma damu da bin sunnar manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ba sam. Suna da wasu shaihunai da waliyyai da wasu Gausi da Kudubi da makamantansu wadanda gare su suke jingina kansu, kuma al’amarinsu suke biya ba na manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ba. 7. Ga kuma wuce gona da iri da ake yi wajen wadannan bukukuwa. Ana karanta abubuwan da ba a san ma ma’anarsu ba. Ko kuma an sani, kuma an san akwai tabargaza da barna a ciki amma an hakikance daidai ne. Kamar wakokin Busiri, wani babanbade da ya zama shatan karni na takwas yana fadanci ga sarakuna da mawadata. A karshe kuma sai ya yi ma manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam irin wannan fadancin da yake ma sarakuna wanda ya wuce gona da iri. Misali a ciki yana cewa: يا أكرم الخلق ما لي من ألوذ به سواك عند حدوث الحادث العمم إن لم تكن آخذاً يوم المعاد يدي صفحاً وإلا فقل يا زلة القدم فإن من جودك الدنيا وضرتها ومن علومك علم اللوح والقلم Wannan ya hada dukkan nau’oin shirka guda ukku; Shirka a Uluhiyyah da Shirka a Rububiyyah da kuma Shirka a cikin siffofin Allah. Wannan kenan. Zaka kuma tarar da yana da wuya ayi wadannan bukukuwan ba a shigar da wasu abubuwa da suke ajanabai daga addini ba kamar raye-raye da makamantan su.

Ya ku bayin Allah! dole ne mutum ya rinka yi yana yi ma kansa hisabi, yana duba ayyukansa don yin gyara. Dole ne kuma ya yawaita addua yana mai rokon Allah imani mai karfi wanda ba ya sassafcewa. Kamar yadda Abdullahi bin Mas’ud Radiyallahu Anhu ya kasance kasance yana rokon Allah da cewa:

اللهم إني أسألك إيمانا لا يرتد ونعيما لا ينفد ومرافقة محمد في أعلى جنة الخلد

Manzon allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya same shi yana karanta suratun Nisa’i kuma yana wannan addu’a (Silsila Sahiha 2301).

Ya Allah! kayi mana kariya daga kowane irin sharri da ake kulla ma na, ka daukaki musulunci da musulmi, ka taimaki masu taimakon addininka.