User:Aliyusamba
An haifi Aliyu Samba a shekarar 1993 a Unguwar Hausawa sabon Titi, jihar kano, Najeriya, mahaifin sa da mahaifiyar sa mutanen kasar Gambiya ne a yammacin Afirka. Ya fara karatun Alkur'ani a makarantar allo kana daga baya ya koma karatun islamiyya a wata makaranta mai suna Khulafa'urrashideen Ridwan Ibrahim Babban Malami, ya kuma koyar a makarantar na tsawon shekaru huɗu. Ya shiga makarantar firamare yana 'dan shekara biyar. Ya yi karatun sa na firamare a makaranta mai zaman kanta a jihar Kano mai suna Melmas International School a Unguwar hausawa sabon titi, sai kuma Sakandire da yayi a makarantar Crown Science and Commercial College dake jihar Kano. Ya rubuta jarabawar kammala sakandare a Makarantar sakandaren Larabci ta Gwale mai suna Government Arabic College Gwale, inda bayan nan ya soma karatun digiri a jami'ar Bayero dake Kano.
Yayi karatu ta hanyoyin kara karatu na zamani dake yanar gizo inda ya karanci fannoni daban daban a kan aikin Jarida, ya kuma samu shedar kwarewa a fannin daga manyan jami'o'i a duniya.
Aliyu Samba ya fara rubutu ne a Kafafen sada zumunta a shekara ta 2010, kuma ya wallafa rubuce rubuce kala kala a fannoni daban daban, kama daga addini, zamantakewa, siyasa, matsalolin al'umma da sauransu.
Yana cikin kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyi masu wayar da kai da dama, kuma a yanzu haka shine manajan gidan rediyon Jarida Radio dake gudanar da shirye-shirye a kan yanar gizo.
Ya zama shugaban jam'iyyar PRP People's Redemption Party (Tsagin Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu) a Jihar Kano a watan Febrairu cikin shekara ta 2022 bayan gabatar da taron jam'iyyar na kananan hukumomi da jiha a gidan Mambayya dake Gwammaja a jihar Kano. [1] [2]