User:Bakandamiyacameroun

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kungiyar Bakandamiya ta ɗauki damarar bada gudumuwarta iya gwargodo don cigaban ƙasar kamaru. Cigaban da mai girma shugaban ƙasa Paul Biya ke jagoranta, wanda kuma ke buƙatar gudumuwar duk ‘ya ‘yan kamaru a jumulce da kuma al’ummar hausawa a kebance. Saninda ƙungiyar keda shi cewa hanyoyin kawo cigaban ba masu sauƙi bane, yasa ta nemi kowa ya bada tasa gudumuwa domin cimma buri. Domin cimma waɗannan manufofin ne muka kafa kungiyar Bakandamiya, wadda burinta shine ta sanya daukacin al’ummar hausawan kamaru cikin shirin kawo cigaban tattalin azriƙin kasa a kowane fanni.



Kalmar Bakandamiya na nufin ‘’mafi inganci, mai kyawo, mafi shahara’’. Dalilin saka wannan suna shine domin mu haɗa karfi da karfe, ta hanyar cimma wadansu sakamako domin magance ƙalubale uku dake gaban mu. Musamman yaki da jahilci, kare al’adun gargajiyarmu da kuma yaki da talauci a cikin al’ummar hausawa. Wato makasudi shine koda yaushe a (zanka) rinka nema nagarta da inganci.

Wadannan abubuwa (ababe) uku sune ke ɗauke da manufofin wannan ƙungiya kamar yadda yake bayyane dalla-dalla a cikin sashe na 4 na dokokin kungiya.

A jajibirin kafa kungiyar Bakandamiya, mu dauki lokaci mai tsawo domin tattaunawa akan Kalmar ‘’bahaushe’’. Kuma a ganinmu yanada kyau mu sake bayyanar da hakan a bainar jama’a. Idan muka ce bahaushe, muna nufin duk wanda ya rungumi al’adun malam bahaushe. Wannan ma’ana ta Kalmar bahaushe tafi bada fifiko kan al’adun gargajiya.

Domin ƙara fahimtar wannan ma’ana ta Kalmar bahaushe da muka bayar, kayi la’akari kawai da tunaninda galibin mutane sukeyi akan wannan Kalmar a yau. Kamar haka, majalisar zartarwa ta Bakandamiya tayi al’faharin kafa ressan kungiya da suka ƙunshi ƙabilu daban-daban.

Mun zabi fannonin gudanar da ayyukanmu ne saboda la’akari da matsalolin da al’ummar mu a dunkule da kuma hausawa a kebance ke fuskanta: kamar uwa-uba yaki da rashin karatu, rashin kishin-kasa, da kuma talauci. Domin samun nasara cikin wannan aiki, ya zama tilas, kowa ya bada gudumuwarsa ko ta hanyar ƙarfinsa ko dukiyarsa. Muna kuma anfani da wannan dama domin muyi kira ga manyanmu, masu muradu irin namu, ‘yan kungiya a mataki na kasa, shuwagannin larduna, kauyuka da ma anguwanni da su ƙara himma domin ayyukan Bakandamiya su dada cigaba.

A ƙarshe, mu dai (waɗanda suka kafa wannan kungiya) wani gungu ne na mutane da suke da cikakken ƙwarin-gwiwar haɗa al’ummar hausawa domin sanyata ta taka rawa wajen kyautata zamantakewa da kuma gina ƙasa. Kamar yadda kuka sani, ɗan Adam tara yake bai cika goma ba, wannan aiki namu ma haka yake. Suhugaban ƙasar Amruka, wato Roosevelt ya ce: ‘’ rashin samun nasara ba shine abu mafi muni ba a rayuwa, abu mafi muni shine rashin gwadawa (gwaji)’’. Saboda haka muke kira ga duk waɗanda suka karanta wannan bayani da su tuna cewa mu ‘yan Adam ne idan suka ga kusakuren mu ko tuntuɓen harshe. Hakazalika muna dakon martini da gudumuwar mu domin ƙara inganta ayyukanmu.

Dotti Ali Salihou

Shugaban ƙungiya na ƙasa