Jump to content

User:Mmnasir

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sheikh Abdulwahab Abdallah

Haihuwarsa da Karatunsa

Shaikh Abdulwahab dan Mika'il dan Abdullahi dan Muhammad Sani. An fi saninsa da Shaikh Abdulwahab Abdallah. An haifeshi a ranar Juma’a 17 ga watan Zul Hijja shekara ta 1373 Hijiriyya wanda ya dace da 28 ga watan Agusta shekara ta 1953 Miladiyya. Ya fara karatun alkur’ani a wajen wan mahaifinsa Alhaji Yahaya dan Imam Abdullahi. Sannan ya karanta littattafan fikihu har zuwa risala, a wurin babban almajirin kakansa Alhaji Tahir, wanda ya yi karatu a kasar Saudiyya. Sai gidan malam Shamsu a kabara wajen Malam Muhammad Ghali Inuwa, ya yi littattafan nahawu da ishiriniyya da tafsiril jalalaini da littafin Adab da Madahu. A wajen Liman dan Amu kuma ya karanta Riyadus Salihin da Warakatu Uslul fikhu. Sai littafin Nahawul Wadi na 1 dana 2 a wajen Malam Nasiru Kabara. Malam Shehu Mai hula ya karantar dashi Askari, haka kuma malam ya halarci cibiyar yada al’adu ta kasar Misra mai reshe a nan Kano (Markazul Sakafi al-Misri), daga nan ne Allah ya kaddara tafiyarsa zuwa kasar Saudiyya, Jami'ar Islamiyya da ke Madina, a Darul Hadith Makiyyah a shekara ta 1976. Ya fara da Mutawassida (junior) daga nan ya shiga babbar sakandare a jami'ar daga nan kuma ya cigaba da kulliyatul hadith (Degree).

Malamansa

A cikin Malamansa na kasar Saudiyya akwai Shaikh Abdul Muhsin Abbad, malamin da yake karatu a Masallacin Madina wanda malam ya karanci littafin sahihul Bukhari da sahih Muslim a wajensa. A Zamansa na kasar Saudiyya kuma ya halarci karatun Shaikh Uthaimin na tafsir da muhaddarorin da yake yi lokacin watan Ramadan. Kuma ya karanta sunan At-Tirmizi da Nahawu a wurin Uztaz Sa'id Al-Ethiopy, wanda mazaunin Makkah ne da ke bayar da karatu a arewacin ka'aba. Haka kuma malam ya yi karatu wajen Shaikh Abdul'aziz Abdulladif da Shaikh Muhammad Madar Az-Zahrani da sauran malamai da dama.

Ayyukansa

Bayan Malam ya dawo Kano 1991 ya ci gaba da da'awa inda ya bude majalisan karatu a birnin Kano da kewaye. Daga ciki akwai karatun Sahihul Bukhari, wanda yake yi ranar asabar da lahadi da safe. Sai littafin Sunan Abi Dawud a kowace ranar Talata tsakanin magriba da issha. Sannan kuma ya karantar da littafin Sunan At-Tirmizi da Subulus Salam da Bulugul Maram da Umdatul Ahkam da sauransu a majalisai daban-daban dake birnin kano da kewaye. Haka kuma malam yana rubuce-rubuce, daga cikin wadanda ya kammala akwai littafin fatawoyin azumin Ramadan da fatawoyin hajji da umra da fatawoyin falalar goman farko na watan babbar salla da littafin hisba da fatawoyin aure da matsalolinsa da sauransu. Sannan kuma malam yana gabatar da shirye-shirye a gidajen radiyo da talabijin na kasar nan da kuma kasashen waje kamar Togo da Benin da Niger da sauransu. A yanzu haka Malam yana zaune a unguwar Sharada a birnin Kano, inda ya shagaltu da harkar da'awa da karantarwa da rubuce-rubuce. Kuma Allah ya albarkance shi da mata da `ya `ya.