User:Musaddam Idriss

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

TAKAITACCEN TAHIRIN JIHAR YOBE


ASALIN SUNAN JIHAR Kalmar 'YOBE' sunane na tekun yammacin nahiyar afirka da ya gangara izuwa tafkin Chadi daga Nijeriya da kuma jamhuriyar Nijar. Cibiyoyinsa sun hada da kogin Hadeja, da Jama'are da Komadugu. Wannan ruwan Yobe shine ya kwaranya har zuwa Kano ya samar da tafkin TIGA da kuma tafkin kafin zaki a jihar Bauchi. Fitattun garuruwan dake kusa da ruwan yobe sun hada da Gashua, Geidam da Damasak duk a jihar, sai kuma DIFFA a jamhuriyar Nijar.

GAME DA JIHAR Jihar Yobe tana daga cikin jihohin arewa maso gabashin nijeriya, an kuma samar da itane a ranar 27 ga watan agustan 1991 (shekaru 27 baya). Damaturu ne babban birnin jihar, anan ne kuma gidan gwamnatin jihar yake da zama. Jihar ta yobe ta hada iyakokintane da jihar Borno daga gabas, sai jihohin Bauchi da Jigawa daga yamma, jihar Gombe daga kudanci, yayinda daga arewaci kuma take makotar kasa-da-kasa da jamhuriyar Nijar.

TARIHIN KAFUWAR JIHAR Kamar yadda jawabin sama ya nuna, an kagi jihar Yobe ne a watan agusta, ranar 27 na shekarar 1991. An kuma kagotane daga jikin jihar barno a lokacin mulkin soja karkashin jagorancin janar babangida, a bisa lura da girman jihar ta barno a wancan lokaci wanda kan iya kawo tsaiko aikin cigaba da bunkasuwar yankin da kuma uwa uba wahalar jagoranci.

MUTANEN JIHAR An kiyasta a shekarar 2011 bayan kidayar kasa cewa mazauna jihar Yobe sun kai 2,757,000. Kuma kabilu mafi yawa a jihar sune: Karai-karai, Mangawa, Fulani, Bolewa, Hausawa, Ngizimawa da Kanuri.

AL'ADUN MUTANEN JIHAR Jihar Yobe, jihace da al'adun mutanen cikinta kusan ya zamo iri daya, duk kuwa da rabe-raben harsuna da al'ummar jihar suke da shi. Al'adun mutanen jihar, al'adune irin na hausawa dan dama duk tushen su guda ne (iyalan harshen kasar chadi). Maza suna sa hula dara, zanna, damanga dasauransu gami da doguwar riga da wando ko babbar riga. Masu sarauta kan yi rawani su kuma dora alkyabba. Mata kuma dinkin riga da zani da dan kwali sai kuma hijabi ko mayafi (gyale). Harshen hausa ne yaren da aka fi magana da shi a birane da manyan garuruwan jihar ta Yobe. A kauyuka kuma yaren kabilun jihar yafi tasiri.

KANANAN HUKUMOMIN JIHAR A jihar Yobe akwai kananan hukumomi guda goma sha bakwai, sun hada da: Bade, Damaturu, Gujba, Gulani, Fika, Fune, Jakusko, Karasuwa, Machina, Nangere, Nguru, Potiskum, Tarmuwa, Yunusari da kuma Yusufari.

ABUBUWAN BIRGEWA DA BUDE IDO A JIHAR A jihar Yobe akwai guraren tarihi da kuma ziyara dan bude ido, daga ciki akwai: 1. Bikin masunta na shekara-shekara a garin Bade. 2. Tsaunukan Daniski 3. Fadar mai Madrinnama (Mai yana nufin sarki). 4. Garin Ngarzargamu 5. Dajin Tulo-Tulowa 6. Bikin al'ada na kamti 7. Rumbun ajiya na Daniski 8. Rijiyar Daura ta dogon kuka a Fune. 9. Kwalekwalen Dufuna (mafi tsufa a afirka kuma na 3 a duniya) 10. Tsanukan garin Fika 11. Kasuwar dabbobi a Potiskum (mafi girma a kaf yammacin afirka).

HARKAR ILIMI A JIHAR Ilimin boko ya samu karbuwa matuka a jihar Yobe, ya kuma samu kulawa sosai wanda hakan ya kai jihar ta Yobe ga mallakar makarantun firamare 631, ga na sakandire da kuma manyan makarantu da jami'o'i. Batun ilimin addini kuwa, wannan ba a magana dan jihar ta Yobe tayi gadon uwargijiyarta kuma makociyarta wato jihar Borno.


Musaddam Idriss (talk) 07:22, 8 Disamba 2018 (UTC)