Jump to content

User:Mustapha Abbas

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Samfuri:Infobox writerMustapha Abbas (an haife shi a shekarar 1989 a Rijiyar Lemo, Kano, Najeriya) marubuci ne na Hausa da ya shahara wajen rubuta kagaggun labarai da suka shafi rayuwar al'umma, soyayya da darussa na zamantakewa.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Mustapha Abbas a unguwar Rijiyar Lemo da ke birnin Kano a shekarar 1989. Ya fara neman iliminsa ne ta hanyar karatun Islamiyya, kafin daga bisani ya shiga makarantar firamare mai suna 'Yammata Special Primary School.

A shekarar 2004 ya shiga karamar makarantar sakandire ta J.S.S Gogau, daga nan kuma ya kammala babbar sakandire a G.S.S Kwachiri, duk a cikin birnin Kano.

Rubuce-rubuce

[gyara sashe | gyara masomin]

Mustapha Abbas ya fara rubuce-rubucen adabi a shekarar 2008 da labarinsa mai taken Kaddarar Mutum. Daga bisani ya rubuta wasu kagaggun labarai da suka hada da:

  • Kaddarar Mutum
  • Girman Alkawari
  • Halacci Ko Butulci
  • Kuɗi Ko Rai

Rubuce-rubucensa sun fi mayar da hankali kan al'amuran rayuwar al'umma da darussan zamantakewa.