User talk:Gwale101

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Hadisi ya tabbata daga Abū Sa’īdul Khudrī  ya ce: na ji Manzon Allah  ya ce:

((مَنْ رَأَى مِنْكُمْ مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الإيمَانِ)). Ma’ana: Wanda ya ga wani mummunan aiki a cikin ku, to, ya kawar da shi da hannunsa, idan ba zai iya ba, to, ya kawar da shi da harshensa, idan ba zai iya ba, to, ya qi abin a zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani . Haka kuma wani hadisin ya tabbata daga Ubadatu Ibn as-Samit  ya ce:

((بَايَعْنَا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى السَّمْعِ وَالطَّاعَةِ، فِي عُسْرِنَا وَيُسْرِنَا، وَمَنْشَطِنَا وَمَكَارِهِنَا، وَعَلَى أَنْ لاَ نُنَازِعَ الأَمْرَ أَهْلَهُ، وَعَلَى أَنْ نَقُولَ بِالْعَدْلِ أَيْنَ كُنَّا، لاَ نَخَافُ فِي اللَّهِ لَوْمَةَ لاَئِمٍ)). Ma’ana: Mun yi mubaya’a ga Manzon Allah  a kan ji da bi cikin quncinmu da yalwarmu da abin da ya yi mana daxi da wanda bai yi mana ba, kuma kada mu ja da shugabanni a kan mulkinsu, kuma mu faxi gaskiya a duk inda muke, ba tare da jin tsoron zargin mai zargi ba . Haka kuma Manzon Allah  yana buga misali don faxakar da al’ummarsa game da haxarin qin yin umarni da kyakkyawa ko hani daga mummuna, kamar yadda ya buga misali a cikin hadisin da ya tabbata daga Nu’umān Ibn Bashīr رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا ya ce: Manzon Allah  ya ce:

((مَثَلُ الْقَائِمِ عَلَى حُدُودِ اللَّهِ وَالْوَاقِعِ فِيهَا، كَمَثَلِ قَوْمٍ اسْتَهَمُوا عَلَى سَفِينَةٍ، فَأَصَابَ بَعْضُهُمْ أَعْلاَهَا، وَبَعْضُهُمْ أَسْفَلَهَا، فَكَانَ الَّذِينَ فِي أَسْفَلِهَا إِذَا اسْتَقَوْا مِنَ الْمَاءِ مَرُّوا عَلَى مَنْ فَوْقَهُمْ، فَقَالُوا : لَوْ أَنَّا خَرَقْنَا فِي نَصِيبِنَا خَرْقًا، وَلَمْ نُؤْذِ مَنْ فَوْقَنَا، فَإِنْ يَتْرُكُوهُمْ وَمَا أَرَادُوا، هَلَكُوا جَمِيعًا، وَإِنْ أَخَذُوا عَلَى أَيْدِيهِمْ نَجَوْا وَنَجَوْا جَمِيعًا)). Ma’ana: Misalin wanda yake tsaye kan iyakokin Ubangiji da wanda yake qetare su, kamar misalin wasu mutane ne da suka yi quri’a wajen hawa jirgin ruwa, sai wasu suka sami sama, wasu kuma suka sami qasa. Sai ya zamana na qasan ba sa samun ruwa, har sai sun hau sama, sai suka ce: ina ma mu huda (jirgin) ta vangarenmu tun da mu a qasa muke, ba sai mun hau sama mun cutar da su ba. A nan sai Manzon Allah  ya ce: idan na saman nan suka bari na qasan nan suka huda jirgin, to, baki xayansu za su halaka, amma idan suka yi riqo da hannunsu (ma’ana suka hana su), to, sai su kuvuta kuma su kuvuta baki xaya . Haka kuma Manzon Allah  ya kan yi bayanin narkon azaba ga waxanda suke qin yin umarni da kyakkyawan aiki kamar yadda ya tabbata a cikin hadisin da Uwar muminai Zaīnab Bint Jahsh رضى الله عنها ta ruwaito cewa:

((أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَخَلَ عَلَيْهَا فَزِعًا، يَقُولُ : لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ، وَيْلٌ لِلْعَرَبِ مِنْ شَرٍّ قَدِ اقْتَرَبَ، فُتِحَ الْيَوْمَ مِنْ رَدْمِ يَأْجُوجَ وَمأْجُوجَ مِثْلُ هَذَا، وَحَلَّقَ بِإِصْبَعِهِ وَبِالَّتِي تَلِيهَا، فَقَالَتْ زَيْنَبُ : فَقُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهِ: أَنَهْلِكُ وَفِينَا الصَّالِحُونَ؟ قَالَ : نَعَمْ إِذَا كَثُرَ الْخَبَثُ)). Ma’ana: Haqiqa wata rana Manzon Allah  ya shigo mini hankalinsa a tashe yana cewa: Lā’ilaha Illallah! Azaba ta tabbata ga Larabawa dangane da wani sharri da ya kusanto! A yau an buxe toshewar/ginewar Yajuju da Majuju kamar haka, sai ya yi zobe da ‘yan yatsunsa (ya haxa babban yatsa da manuniya). Sai Nana Zaīnab رضى الله عنها ta ce: Ya Manzon Allah  yanzu a halakar da mu bayan a cikin mu akwai salihai? Sai Manzon Allah  ya ce: Na’am! Matuqar varna ta yawaita .

AIKIN HISBARSA WAJEN KAWAR DA ABIN QI (MUNKARI) DA HANNUNSA MAI ALBARKA[gyara masomin]

Hisbar Manzon Allah ba ta taqaita wajen yin umarni ko hani ba kawai. Ya kasance yana kawar da munkari da hannayensa masu albarka, kamar yadda ya tabbata daga Abdullahi Ibn Mas’ūd ya ce:

((بَيْنَا النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُصَلِّي، رَأَى فِي قِبْلَةِ الْمَسْجِدِ نُخَامَةً، فَحَكَّهَا بِيَدِهِ، فَتَغَيَّظَ، ثُمَّ قَالَ : إِنَّ أَحَدَكُمْ إِذَا كَانَ فِي الصَّلاَةِ فَإِنَّ اللَّهَ حِيَالَ وَجْهِهِ، فَلاَ يَتَنَخَّمَنَّ حِيَالَ وَجْهِهِ فِي الصَّلاَةِ)). Ma’ana: Wata rana Manzon Allah yana sallah a masallaci, sai ya ga majina a jikin bangon masallacin, sai ya sa hannunsa mai albarka ya kankare wannan majinar kuma ransa ya vaci, sannan ya ce: haqiqa idan xaya daga cikin ku yana sallah, to, Allah yana gaba gare shi, don haka kada wanda ya qara tofar da majina a gabansa idan yana sallah .

Haka kuma hadisi ya tabbata daga Uqbatu Ibn Āmir ya ce: ((أُهْدِيَ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَرُّوجُ حَرِيرٍ، فَلَبِسَهُ فَصَلَّى فِيهِ، ثُمَّ انْصَرَفَ فَنَزَعَهُ نَزْعًا شَدِيدًا كَالْكَارِهِ لَهُ، وَقَالَ : لاَ يَنْبَغِي هَذَا لِلْمُتَّقِينَ)). Ma’ana: An baiwa Manzon Allah kyautar alkyabba ta alharīr , sai ya sanya ta ya yi sallah da ita, yayin da ya idar da sallar, sai ya fincike ta daga jikinsa kamar ya qyamace ta, sannan ya ce: sanya irin wannan tufafin bai kamata ba ga masu tsoron Allah . Da kuma hadisin da ya tabbata daga Abdullahi Ibn Abbās ya ce:

((أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَأَى خَاتَمًا مِنْ ذَهَبٍ فِي يَدِ رَجُلٍ، فَنَزَعَهُ فَطَرَحَهُ، وَقَالَ : يَعْمِدُ أَحَدُكُمْ إِلَى جَمْرَةٍ مِنْ نَارٍ فَيَجْعَلُهَا فِي يَدِهِ، فَقِيلَ لِلرَّجُلِ بَعْدَ مَا ذَهَبَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : خُذْ خَاتِمَكَ انْتَفِعْ بِهِ، قَالَ : لاَ وَاللَّهِ لاَ آخُذُهُ أَبَدًا وَقَدْ طَرَحَهُ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ)). Ma'ana: Manzon Allah ya ga zoben zinariya a hannun wani mutum, sai Manzon Allah ya fizge zoben ya jefar da shi, kuma ya ce: Xayanku ya xauki garwashin wuta, ya sanya a hannunsa. Sai aka ce da mutumin ka xauki zobenka ka yi wani amfanin da shi mana, sai ya ce: A’a wallahi ba zan xauke shi ba har abada, tun da Manzon Allah ya jefar da shi .

AIKIN HISBARSA A VANGAREN INGANTA AQIDA[gyara masomin]

A kullum burin Manzon Allah  shi ne ya gyara aqidar al’ummarsa da xora su kan tsantsar tauhidi. Wannan kuwa shi ne mafi girman aikin da ya sanya a gaba. Haka ne ma ya sa duk lokacin da ya ga wata varaka za ta shigo cikin aqidar al’ummarsa yake qoqarin toshe ta. Kamar yadda ya yi wa wasu daga cikin sahabbansa  inkari a cikin hadisin da ya tabbata daga Abū Wāqidul Laīsī  ya ce: ((أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لَمَّا خَرَجَ إِلَى حُنَيْنٍ، مَرَّ بِشَجَرَةٍ لِلْمُشْرِكِينَ يُقَالُ لَهَا ذَاتُ أَنْوَاطٍ، يُعَلِّقُونَ عَلَيْهَا أَسْلِحَتَهُمْ، فَقَالُوا يَا رَسُولَ اللَّهِ : اجْعَلْ لَنَا ذَاتَ أَنْوَاطٍ كَمَا لَهُمْ ذَاتُ أَنْوَاطٍ، فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : سُبْحَانَ اللَّهِ، هَذَا كَمَا قَالَ قَوْمُ مُوسَى اجْعَلْ لَنَا إِلَهًا كَمَا لَهُمْ آلِهَةٌ، وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ، لَتَرْكَبُنَّ سُنَّةَ مَنْ كَانَ قَبْلَكُمْ)). Ma’ana: Yayin da Manzon Allah  ya fita shi da sahabbansa  zuwa yaqin Hunaīn, sai suka wuce ta wajen wata bishiya da ake kira “Zātu Anwāx” wadda mushirikai suke rataya kayan yaqinsu a jikinta don neman sa’a, sai waxannan sahabban suka ce da Manzon Allah  mu ma ka sanya mana wata bishiyar da za mu riqa rataya mata kayan yaqinmu kamar yadda mushirikai suke da ita, sai Manzon Allah  ya cikada mamaki sannan ya ce: Tsarki ya tabbata ga Allah! Wannan maganar ta yi kama da abin da mutanen Annabi Musa  suka nema daga gare shi cewa: “ka sanya mana wani abin bauta kamar yadda kafirai suke da abin bauta” sai Manzon Allah  ya ce: Na rantse da Allah za ku bi tafarkin waxanda suka gabace ku (wato Yahudu da Nasara wanda suka kauce daga kan hanya madaidaiciya). Da kuma hadisin da ya tabbata daga Abdullahi Ibn Abbās  ya ce: Umar  ya ce:

((كُنْتُ فِي رَكْبٍ أَسِيرُ فِي غَزَاةٍ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَحَلَفْتُ فَقُلْتُ : لاَ وَأَبِي، فَنَهَرَنِي رَجُلٌ مِنْ خَلْفِي، وَقَالَ : لاَ تَحْلِفُوا بِآبَائِكُمْ، فَالْتَفَتُّ، فَإِذَا أَنَا بِرَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ)). Ma’ana: Na kasance a cikin tawagar yaqi, tare da Manzon Allah  sai na yi rantsuwa na ce: Na rantse da mahaifina. Sai na ji daga bayana wani mutum ya yi mani tsawa ya ce: Kada ku rantse da iyayenku. Ina juyawa sai na ga Manzon Allah  ne . A wata ruwayar Umar  yana cewa:

((فَوَاللَّهِ مَا حَلَفْتُ بِهَا بَعْدُ ذَاكِرًا وَلاَ آثِرًا)). Ma’ana: Wallahi ban qara yin irin wannan rantsuwar ba, a bisa sani ko kuskure . Daga cikin irin aikin Hisbarsa  a vangaren aqida har yanzu, akwai hadisin da ya tabbata daga Abdullahi Ibn Abbas  ya ce:

((أَنَّ رَجُلاً قَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : مَا شَاءَ اللَّهُ وَشِئْتَ، فَقَالَ لَهُ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ : أَجَعَلْتَنِي وَاللَّهَ عَدْلاً، بَلْ مَا شَاءَ اللَّهُ وَحْدَهُ)). Ma’ana: Wani mutum ya cewa Manzon Allah : Abin da Allah ya so kai ma ka so. Sai Manzon Allah  ya ce: Yanzu ka sanya ni tamka ga Allah? Maimakon haka ka ce: Abin da Allah ya so shi kaxai . Haka kuma yana daga cikin aikin Hisbarsa  a wannan vangaren, gusar da gumakan da ke kewaye da xakin Allah, kamar yadda ya tabbata daga Abdullahi Ibn Mas’ūd  ya ce: ((دَخَلَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ مَكَّةَ يَوْمَ الْفَتْحِ، وَحَوْلَ الْبَيْتِ سِتُّونَ وَثَلاَثُ مِائَةِ نُصُبٍ، فَجَعَلَ يَطْعُنُهَا بِعُودٍ فِي يَدِهِ وَيَقُولُ : {جَاءَ الْحَقُّ وَزَهَقَ الْبَاطِلُ} { جَاءَ الْحَقُّ وَمَا يُبْدِئُ الْبَاطِلُ وَمَا يُعِيدُ}. Ma’ana: Manzon Allah  ya shiga Makka ranar Fathu Makka (watau ranar da ya buxe Makka) alhali a kewaye da Ka’aba akwai gumaka xari uku da sittin (360). Sai Manzon Allah  ya riqa ture su da sanda yana cewa: “Gaskiya ta zo, qarya kuma ta kau”. “Gaskiya ta zo qarya ta gushe babu dawowa .