Jump to content

Ushra da Jangali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ushra da Jangali
class="wikitable"
Ushra da Jangali
Bayani Cikakken Bayani
Nau'in Harajin Noma da Kiwo
Yanki Arewacin Najeriya, Yankunan Hausawa
An fara amfani Kafin karni na 19
An daina amfani sosai Bayan zuwan Turawa
Dalili Tara haraji daga manoma da makiyaya
Haraji masu kama da shi Zakka, Harajin gargajiya

Ushra da Jangali haraji ne da aka saba karɓa a zamanin da a yankunan Hausawa, musamman a lokacin daular Musulunci da kuma zamanin mulkin sarauta. Sun shafi noma da kuma kiwo, inda ushra ke shafar manoma, yayin da jangali ke shafar makiyaya.[1]

Ushra haraji ne da ake karɓa daga amfanin gona, musamman a tsarin Musulunci. Ana cire kaso ɗaya cikin goma (1/10) na amfanin noma daga manoma, sannan a bayar da shi a matsayin haraji ko sadaka. Wannan tsari yana da dangantaka da zakka da ake bayarwa a Musulunci. A wasu lokuta, ushra na iya kasancewa ƙarin haraji da masu mulki ke karɓa daga manoma. Wannan yana taimakawa wajen kula da masarautu, addini, da kuma jin daɗin al'umma.

Jangali kuwa haraji ne da ake karɓa daga makiyaya bisa adadin dabbobinsu, musamman shanu. Ana amfani da kudin jangali wajen kula da rayuwar makiyaya,:

  • kamar Gina rijiyoyi don makiyaya
  • Kare hakkokin makiyaya
  • Samar da tsaro a filayen kiwo

Harajin jangali yana taimakawa wajen tabbatar da cewa makiyaya na da gudunmawa a cikin tattalin arziki da shugabanci.[2]

  1. name=:www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.jstor.org/stable/221307&ved=2ahUKEwiV3tvXh7eMAxUtVkEAHbNNOagQFnoECCEQAQ&usg=AOvVaw3dJbIBFo5ZTjUvFjtDmDZK
  2. name=www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://ehrafworldcultures.yale.edu/cultures/ms12/summary&ved=2ahUKEwj2xJi_hreMAxX-G9AFHcxoKkEQFnoECCMQAQ&usg=AOvVaw3mr2ChPI6FsiztvIGQ9o_X[permanent dead link]