Jump to content

Usman Abd'Allah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Usman Abd'Allah
Rayuwa
HaihuwaKano, 16 ga Yuni, 1974 (52 shekaru)
Sana'a
Sana'aassociation football coach (en) Fassara
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Usman Abd'Allah (an haife shi ranar 16 ga Yuni, 1974 a jihar Kano) ƙwararren mai horas da ƙwallon ƙafa ne ɗan Najeriya mai kuma ɗauke da ɗan ƙasar Faransa. Ya yi aiki a matsayin mai horaswa da mashawarci ga ƙungiyoyi daban-daban a Najeriya, Asiya da Turai. An fi saninsa da jagorantar ƙungiyar Enyimba FC zuwa lashe gasar NPFL ta shekarar 2018/2019. [1]

Rayuwar farko

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Usman Abd'Allah a Kano, Najeriya. Ya fara karatunsa a makarantar Tarauni Primary School sannan ya halarci Government Secondary School Kazaure. Daga bisani ya yi karatun Chemical Engineering a Kaduna State Polytechnic. [2]

Aikin ɗan wasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Usman Abd'Allah ya fara harkar ƙwallo a Najeriya inda ya taka leda a kungiyoyi irin su Stationery Stores, UNTL Kaduna da Mogas 90 ta Jamhuriyar Benin. Bayan haka ya buga ƙwallo a wasu ƙasashe na Turai da Asiya ciki har da Singapore, Bangladesh da Malaysia. Ya dakatar da buga ƙwallo a shekarar 2006 bayan ya taka leda a Faransa. [3]

Aikin horaswa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ya daina taka leda, Usman Abd'Allah ya fara aikin horaswa a ƙananan kungiyoyi a Faransa kafin ya dawo Najeriya. Ya yi aiki a Kano Pillars a matsayin mataimakin koci sannan daga baya ya shiga Enyimba FC. A Enyimba ya kai ƙungiyar zuwa wasan kusa da na ƙarshe a gasar CAF Confederation Cup sannan ya lashe kofin NPFL na shekarar 2018/2019. [4]

A shekarar 2026, ƙungiyar Remo Stars ta naɗa shi a matsayin Technical Adviser domin taimakawa ƙungiyar wajen bunƙasa sakamakonta a gasar Najeriya. Rahotanni sun bayyana cewa yana da takardun horaswa na UEFA Pro Licence da kuma ƙwarewa daga cibiyoyin horaswa na Faransa da Singapore. [5]

  • Enyimba FC
    • Najeriya Premier Football League (NPFL): 2018/2019 [6]

Rayuwar sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Usman Abd'Allah yana da zama ɗan ƙasa biyu wato Najeriya da Faransa. Yana aure da wata Bafaranshiya kuma suna da ‘ya’ya tagwaye mata. [7]

  1. ↑ "Usman Abd'Allah". Wikipedia. Retrieved 2026-05-21.
  2. ↑ "Usman Abd'Allah - Early life". Wikipedia. Retrieved 2026-05-21.
  3. ↑ "Usman Abd'Allah - Playing career". Wikipedia. Retrieved 2026-05-21.
  4. ↑ "Usman Abd'Allah - Coaching career". Wikipedia. Retrieved 2026-05-21.
  5. ↑ "Remo Stars Appoint Usman Abd'Allah As Technical Adviser". Voice of Nigeria. 2026-02-27. Retrieved 2026-05-21.
  6. ↑ "NPFL: Remo Stars Appoint Abd'Allah New Technical Adviser". Complete Sports. Retrieved 2026-05-21.
  7. ↑ "Usman Abd'Allah - Personal life". Wikipedia. Retrieved 2026-05-21.