Jump to content

Valère Somé

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Valère Somé
Rayuwa
Haihuwa Burkina Faso, 17 Oktoba 1950
ƙasa Burkina Faso
Mutuwa Metz, 30 Mayu 2017
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da minista
Imani
Jam'iyar siyasa Union of Communist Struggles – Reconstructed (en) Fassara

Valère Dieudonné Somé (17 Oktoba 1950 - 30 Mayu 2017) ɗan siyasa ne kuma masani daga Burkina Faso. Somé ya kasance shugaban Ƙungiyar Union of Communist Struggles - Reconstructed (ULC-R) a cikin shekarar 1980s.[1] Ya kasance masanin tattalin arziki-Anthropo-economist, kuma ya jagoranci bincike a INSS-CNRST.[2]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Shiga cikin tsarin juyin juya hali na shekarar 1983 tare da goyon baya daga ƙungiyoyin ɗalibai, Somé ya zo ya taka muhimmiyar rawa a cikin harkokin siyasar ƙasar a lokacin mulkin Majalisar juyin juya hali na ƙarƙashin jagorancin Thomas Sankara. Somé da wani shugaban ULC-R, Basile Guissou, sun fi aiki a matsayin 'masu akidar' gwamnatin juyin juya hali.[3]

A cikin watan Janairu 1985 ULC-R ta lashe zaɓe a Jami'ar Ouagadougou Kwamitin Tsaro na juyin juya hali. Sai dai wani ɓangare, kungiyar 'yan gurguzu ta Burkinabè (UCB), ta mallaki hukumar jami'ar ta hannun babban jami'in Clément Oumarou Ouedraogo. A ranar 29 ga watan Agusta 1986 aka naɗa Somé Ministan Ilimi mai zurfi da Bincike. Sakamakon haka, daga hamayyar ULC-R/UCB a jami’a, an rushe kwamitin CDR na jami’ar a ranar 1 ga watan Satumba 1986. Somé ya fuskanci suka daga cikin kungiyarsa bayan ya riƙe muƙamin minista.

A ranar 9 ga watan Satumbar 1987 aka kafa sabuwar gwamnati, ba tare da Somé ba. A cikin wannan watan ne Sankara ya baiwa Somé aikin shirya wani shiri na haɗa kan kungiyoyin juyin juya hali daban-daban. Bayan kifar da kisa na Sankara a shekarar 1987, Somé ya tafi gudun hijira a Kongo-Brazzaville na wani ɗan lokaci.[4][5]

A cikin shekarar 1989 Somemé ya kafa Jam'iyyar Social Democracy (PDS) tare da wasu tsoffin membobin ULC-R waɗanda suka ƙi haɗa kai da Organization for Popular Democracy - Labor Movement. A cikin watan Janairu 1995 PDS da wasu jam'iyyu suka haɗe cikin jam'iyyar Unified Social Democracy (PDSU), tare da Somé a matsayin shugabanta.

Somé ya kammala karatun digirinsa a shekarar 1996.

A ranar 21 ga watan Mayu, 2000, jam'iyyar Somé ya haɗe cikin Yarjejeniyar Pan-African ta Sankarist (CPS). Somé ya zama babban sakatare na CPS. Daga baya ya kafa sabuwar jam’iyya mai suna Convergence for Social Democracy (CDS). A cikin watan Oktoba 2004 Djéjouma Sanon ya maye gurbinsa a matsayin shugaban CDS.[4][6]

Somé ya mutu a ranar 30 ga watan Mayu 2017 a Faransa yana da shekaru 66.

Littattafai

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. Hughes, Arnold. Marxism's Retreat from Africa. London: F. Cass, 1992. p. 100
  2. Tic & développement: Dr. Valère Somé Archived 2007-10-28 at the Wayback Machine
  3. Bianchini, Pascal. Ecole et politique en Afrique noire: sociologie des crises et des réformes du système d'enseignement au Sénégal et au Burkina Faso (1960–2000). Paris: Karthala, 2004. pp. 106, 145
  4. 4.0 4.1 "PAGE TRISTE : Valère Somé n'est plus". Le Pays. 2017-05-31.
  5. "Burkina : Dr Valère Somé est décédé". Burkina24.com. 2017-05-31.
  6. "Burkina : Dr Valère Somé est décédé". Burkina24.com. 2017-05-31.