Jump to content

Vincenzo(shirin talabijin mai dogon zango)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Vincenzo(shirin talabijin mai dogon zango)
Asali
Asalin suna 빈센조
Asalin harshe Bakoriye
Ƙasar asali Koriya ta Kudu
Yanayi 1
Episodes 20
Distribution format (en) Fassara video on demand (en) Fassara
Characteristics
Genre (en) Fassara action television series (en) Fassara, comedy television series (en) Fassara da crime television series (en) Fassara
Direction and screenplay
Darekta Kim Hee-won (en) Fassara
Marubin wasannin kwaykwayo Park Jae-beom (en) Fassara
'yan wasa
Samar
Production company (en) Fassara Logos Film (en) Fassara
Other works
Mai rubuta kiɗa Park Se-joon (en) Fassara
Screening
Asali mai watsa shirye-shirye tvN (en) Fassara
Lokacin farawa Fabrairu 20, 2021 (2021-02-20)
Lokacin gamawa Mayu 2, 2021 (2021-05-02)
External links
program.tving.com…

Vincenzo (Yaren Koriya: 빈센조; RR: Binsenjo) shirin talabijin ne mai dogon zango na Koriya ta Kudu na shekarar 2021 wanda ke dauke da jarumi Song Joong-ki a matsayin wanda fim din keda sunan sa, tare da Jeon Yeo-been, Ok Taec-yeon, Kim Yeo-jin, da Kwak Dong-yeon. An haska shirin a TVN daga ranar 20 ga Fabrairu, 2021, zuwa Mayu 2, 2021, kowace Asabar da Lahadi a 21:00 (KST); kowane kashi an fito dashi akan Netflix a Koriya ta Kudu da kuma a duniya baki daya bayan watsa shi a talabijin.[1][2]

Kashi na farko ya kai darajar kashi 7.7% (AGB a duk faɗin ƙasar), wanda hakan ya sa ya zama wasan kwaikwayo na tvN mafi girma na huɗu. Kashi na karshe ya sami kima kashi 14.6%, wanda hakan ya sa ya zama wasan kwaikwayo mafi girma na goma sha ɗaya a tarihin gidan talabijin na USB na Koriya a lokacin.[3] Har ila yau, ya sanya shiri mai dogon zangon ya zama na shida mafi girma a tarihin tvN.[4]

Shirin kuma ya shahara tsakanin masu kallo na duniya ta hanyar Netflix, yana mai rike matsayinsa a cikin manyan shirye-shiryen TV 10 akan Netflix a duniya tun farkonsa kuma ya kai matsayi na hudu a ranar 26 ga Afrilu.[5] Ya zama na hudu akan jerin Forbes na shirin mai dogon zango na Koriya da aka fi kallo akan Netflix a cikin 2021.[6]

  1. Song, Eun-kyung (August 10, 2020). 송중기-전여빈-옥택연, tvN '빈센조' 출연 … 내년 방송 [Song Joong-ki, Jeon Yeo-been and Ok Taecyeon to appear on tvN 'Vincenzo' ... Broadcast next year]. Yonhap (in Korean). Archived from the original on February 6, 2021. Retrieved October 27, 2020.
  2. MacDonald, Joan (January 6, 2021). "10 Dramas To Watch Out For In 2021". Forbes. Archived from the original on January 11, 2021. Retrieved January 9, 2021.
  3. "Nielsen Korea". AGB Nielsen Media Research. Archived from the original on February 21, 2021. Retrieved March 22, 2021.
  4. 빈센조' 송중기, 악당의 방식으로 빌런 옥택연X김여진X조한철 처단. The Korea Economic Daily (in Korean). May 3, 2021. Archived from the original on May 12, 2021. Retrieved May 3, 2021.
  5. Update] "Vincenzo" Currently Ranked 4th Most Popular TV Show On Netflix Worldwide". Kpopmap. April 27, 2021. Archived from the original on December 18, 2021. Retrieved December 18, 2021.
  6. Feldman, Dana. "Here Are The 10 Most-Viewed Korean Series On Netflix In 2021". Forbes. Archived from the original on December 15, 2021. Retrieved December 18, 2021.