Volodymyr Zelensky

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Volodymyr Zelensky
Murya
6. President of Ukraine (en) Fassara

20 Mayu 2019 -
Petro Poroshenko (en) Fassara
Supreme Commander of the Armed Forces of Ukraine (en) Fassara

20 Mayu 2019 -
Rayuwa
Haihuwa Kryvyi Rih (en) Fassara, 25 ga Janairu, 1978 (46 shekaru)
ƙasa Ukraniya
Kungiyar Sobiyet
Mazauni Mariinskyi Palace (en) Fassara
Ƙabila Ukrainian Jews (en) Fassara
Harshen uwa Rashanci
Harshan Ukraniya
Ƴan uwa
Mahaifi Oleksandr Zelenskyy
Mahaifiya Rimma Zelenska
Abokiyar zama Olena Zelenska (en) Fassara  (2003 -
Yara
Karatu
Makaranta Kyiv National Economic University named after Vadym Hetman (en) Fassara
Kryvyi Rih Institute of Economics (en) Fassara
(1995 - 2000) : Doka
Harsuna Rashanci
Harshan Ukraniya
Ibrananci
Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, cali-cali, mai gabatar wa, mai tsara fim, marubin wasannin kwaykwayo, Jarumi, mai tsare-tsaren gidan talabijin, mai gabatarwa a talabijin, entertainer (en) Fassara, mawaƙi, humorist (en) Fassara, filmmaker (en) Fassara, showman (en) Fassara, KVN actor (en) Fassara, soja, international forum participant (en) Fassara da impressionist (en) Fassara
Tsayi 167 cm
Wurin aiki Kryvyi Rih (en) Fassara da Kiev
Employers Kvartal 95 (en) Fassara
1+1 (en) Fassara
Inter (en) Fassara
Office of the President of Ukraine (en) Fassara
Muhimman ayyuka Servant of the People (en) Fassara
Kyaututtuka
Wanda ya ja hankalinsa Alexander Maslyakov (en) Fassara
Sunan mahaifi Зелёный
Artistic movement parody (en) Fassara
barkwanci
humor (en) Fassara
Kayan kida murya
Aikin soja
Fannin soja Armed Forces of Ukraine (en) Fassara
Digiri Soldat (rank) (en) Fassara
Ya faɗaci Mamayewar Rasha na Ukraine na 2022
War in Donbas (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Servant of the People (en) Fassara
IMDb nm3305952
president.gov.ua da ze2019.com
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da ilham
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy a majalisar dokokin kasar Koriya
Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da gwamnan holan

Volodymyr Oleksandrovych Zelenskyy da Hausa ana furta sunan shi da Zelenskai an haife shi a ranar 25 ga watan Janairu shekara ta 1978. Ɗan ƙasar Ukraniya ne, tsohon ɗan wasan kwaikwayo kuma ɗan wasan barkwanci wanda shi ne shugaban ƙasa na shida kuma shi ne shugaban ƙasar Ukraniya na yanzu.[1][2]

Zelenskyy ya girma a Kryvyi Rih, babban birni a yankin da ake magana da harshen Ukraniya a tsakiyar Ukraniya. ya sami digiri a fannin shari'a daga Jami'ar Tattalin Arziƙi ta Kyiv. Daga nan sai ya fara wasan kwaikwayo shi ne wanda ya ƙirƙiro kamfanin Kvartal 95, wanda ke samar da fina-finai, zane-zane/kaatuun, da kuma watsa fina-finai na shows TV cikin finafinan shi akwai Servant of the People, wanda Zelenskyy ya fito a matsayin shugaban kasar Ukraniya. Film ɗin mai dogon zango ya fito daga 2015 zuwa 2019 kuma ya shahara sosai ya samu ƙarɓuwa a gun jama'a. Ma'aikatan Kvartal 95 ne suka ƙirƙiro wata jam'iyyar siyasa mai suna iri ɗaya da sunan gidan talabijin ɗin shi (Shows TV) a watan Maris shekarar 2018.

Zelenskyy ya sanar da maganar tsayawa takararsa a zaɓen shugaban ƙasar Ukraniya na shekara ta 2019 a yammacin ranar 31 ga Disamba shekara ta 2018, tare da jawabin jajibirin sabuwar shekara na shugaban ƙasar Petro Poroshenko akan tashar talabijin ta 1+1 TV channel. Ɓangaren siyasa, ya riga ya zama ɗaya daga cikin masu fafutukar neman shugabanci a siyasance, ya lashe zaɓen ne da kashi 73.2 na ƙuri'un da aka kaɗa a zagaye na biyu, inda ya doke Poroshenk. An gane cewa shine ya shahara sosai a lokacin. ya yima kansa laƙabi da ɗan gwagwarmayar kafa sabbin cigaba (anti-establishment), da kuma wargaje cin hanci da rashawa (anti-corruption).

A matsayinsa na shugaban ƙasa, Zelenskyy ya kasance mai goyon bayan gwamnatin zamani ta e-government da haɗin kai tsakanin sassan ƙasar Ukraniya da masu magana da harshen Rashanci. Salon yadda yake amfani da kafofin watsa labarun yana burgewa sosai, musamman a Instagram .

Gwamnatin Zelenskyy ta fuskanci babban hatsaniya da ƙasar Rasha a cikin shekara ta 2021, wanda a ƙarshe taƙaddamar ta haifar da har sai da shugaban ƙasar Vladimir Putin Rasha ya bada umurnin sojojin Rasha su mamaye ƙasar Ukraniya a watan Fabrairu shekara ta 2022. Dabarar Zelenskyy a lokacin da Rasha ta girke sojojin ta don mamaye Ukraniya ita ce kwantar da hankalin al'ummar Ukraniyawa tare da tabbatar wa ƙasashen duniya cewa Ukraniya ba ta neman daukar fansa akan Rasha. Bayan da Rasha ta fara mamaye Ukraniya, Zelenskyy ya ayyana dokar-ta-ɓaci a duk faɗin ƙasar da taron gama gari.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Dickinson, Peter (9 June 2019). "Zelensky, Zelenskiy, Zelenskyy: Spelling Confusion Doesn't Help Ukraine". Atlantic Council (in Turanci). Archived from the original on 11 June 2019. Retrieved 10 June 2019.
  2. Mendel, Iuliia [@IuliiaMendel]. "Dear colleagues, this is the official form of the last name that the President has in his passport. This was decided by the passport service of Ukraine. The President won't be offended if BBC standards assume different transliteration" (Tweet) (in Turanci). Archived from the original on 12 November 2020. Retrieved 10 June 2019 – via Twitter.