Wahshi dan Harb
|
| |
| Rayuwa | |
| Haihuwa | Yankin Larabawa, 7 century |
| Mutuwa | Yankin Larabawa, 660s |
| Sana'a | |
| Sana'a | Jarumi |
| Aikin soja | |
| Ya faɗaci |
Yaƙin Uhudu Yaƙe -yaƙe Ridda |
| Imani | |
| Addini | Musulunci |
Sahabin ne na Annabi Muhammad. Yayi rayuwa tare da manzon Allah.(SAW ). Sunan shi Wahshiy bin Harb Al-habashi bawane na wani mutum dake garin Makkah,a farko kafin shigarsa Musulunci lokacin yana bawa,Wahshi yayi ƙaurin suna sakamakon kisan da yayiwa Hamza bin Abdu-Mudallib(baffan Manzon Allah SAW) ayaƙin Hudu yayin da Hindu Bint Umayyah matar Abu Sufyan tamishi Alƙawarin yanci idan har yakashe Hamza a filin yaƙi. Wahshiy ya ƙware sosai wajen harbin kibiya, hakan yasa yabi tawagar mayaƙa ya shige cikinsu ya laɓe ya harbe Hamza da mashi wanda wannan yayi sanadiyar shahadarsa.
Kodayake daga baya Wahshiy ya tuba kuma yashiga Musulunci to amma duk dahaka idan yatuna kisan Hamza da yayi abin yana damunshi kuma jama'a suna kallonshi da lafin har sai lokacin daya kashe Muthailamatul- Kazzhab wanda yayi ikirarin Annabtar ƙarya to sa'annan ne Wahshiy yasamu mutuwa Sahabbai suka yaba mishi domin yayiwa addinin musulunci babban hidima.