Wajen Ramsar
|
conservation designation (en) | |
| Bayanai | |
| Ƙaramin ɓangare na | Dausayi, al'adun muhalli da Yankin kariya |
| Applies to jurisdiction (en) |
Ramsar Convention (en) |
| Shafin yanar gizo | rsis.ramsar.org |
| Babban tsarin rubutu |
Ramsar Convention (en) |
| Nada jerin |
list of Ramsar sites (en) |




A gurin Ramsar wani yanki ne na dausayi (wetland) da aka keɓance domin ya zama mai mahimmancin gaske a matakin ƙasa da ƙasa a ƙarƙashin Yarjejeniyar Ramsar,[1] wacce kuma aka sani da "Yarjejeniyar Dausayi", wata yarjejeniyar muhalli ce ta ƙasa da ƙasa da aka sanya wa hannu a ranar 2 ga Fabrairu 1971 a birnin Ramsar da ke ƙasar Iran, a ƙarƙashin kulawar UNESCO. Yarjejeniyar ta fara aiki a ranar 21 ga Disamba 1975, lokacin da isasshen adadin ƙasashe suka amince da ita. Tana ba da damar ɗaukar matakai a matakin ƙasa da kuma haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa game da kiyaye dausayi, da kuma yin amfani da albarkatunsu cikin hikima da dorewa.[1] Membobin yarjejeniyar Ramsar suna haɗuwa akai-akai don ganowa da amincewa kan kiyaye "Dausayi Mai Mahimmanci a Matakin Ƙasa da Ƙasa", musamman waɗanda ke zama mazaunin tsuntsayen ruwa (waterfowl).
Ya zuwa watan Janairun 2026, akwai guraren Ramsar guda 2,520 a duniya, waɗanda ke kiyaye yanki mai faɗin hekta 253,075,668, kuma gwamnatocin ƙasashe 172 ne ke shiga cikin wannan yarjejeniya.[1]
Jerin Gurare
[gyara sashe | gyara masomin]Ƙungiyar da ba ta neman riba ta Wetlands International tana ba da damar yin amfani da bayanan Ramsar ta hanyar Sabis ɗin Bayanai na Guraren Ramsar (Ramsar Sites Information Service).[2]
Sharuɗɗan Zama Gurin Ramsar
[gyara sashe | gyara masomin]Ana iya ɗaukar dausayi a matsayin mai mahimmanci a matakin ƙasa da ƙasa idan ɗaya daga cikin waɗannan sharuɗɗan guda tara ya tabbata a kansa:[3]
- Sharadi na 1: "yana ɗauke da misali na musamman, na daban, ko wanda ba a cika samun irinsa ba na nau'in dausayi na halitta ko kusa da na halitta da ake samu a cikin yanki mai dacewa na biogeographic."
- Sharadi na 2: "yana tallafawa jinsunan da ke cikin haɗari, waɗanda ke fuskantar barazanar ƙarewa, ko kuma al'ummomin muhalli da ke fuskantar barazana."
- Sharadi na 3: "yana tallafawa yawan jinsunansu na tsirrai da/ko dabbobi masu mahimmanci don kiyaye nau'ikan halittu (biological diversity) na wani yanki na musamman na biogeographic."
- Sharadi na 4: "yana tallafawa jinsunan tsirrai da/ko dabbobi a wani mataki mai mahimmanci na tsarin rayuwarsu, ko kuma yana ba da mafaka lokacin da yanayi ya yi tsanani."
- Sharadi na 5: "akai-akai yana tallafawa tsuntsayen ruwa guda 20,000 ko fiye da haka."
- Sharadi na 6: "akai-akai yana tallafawa kashi 1% na daidaikun halittu a cikin yawan jinsin tsuntsun ruwa guda ɗaya ko ƙarƙashin jinsinsa (subspecies)."
- Sharadi na 7: "yana tallafawa kaso mai tsoka na jinsunan kifin gida, ƙarƙashin jinsunansu ko iyalansu, matakan tarihin rayuwa, alaƙar jinsuna da/ko yawansu waɗanda ke wakiltar fa'idodi da/ko darajar dausayi, kuma ta hakan yana ba da gudummawa ga nau'ikan halittu na duniya."
- Sharadi na 8: "shi ne tushen abinci mai mahimmanci ga kifaye, gurin yin ƙwai, gurin renon 'ya'ya da/ko hanyar yin ƙaura wacce albarkatun kifi ke dogara da ita, ko dai a cikin dausayin ko a wani gurin daban."
- Sharadi na 9: "akai-akai yana tallafawa kashi 1% na daidaikun halittu a cikin yawan jinsin dabba guda ɗaya ko ƙarƙashin jinsinta na dabbobin da suka dogara da dausayi waɗanda ba tsuntsaye ba."
Tsarin Rarrabawa
[gyara sashe | gyara masomin]Tsarin Rarraba Nau'ukan Dausayi na Ramsar (Ramsar Classification System for Wetland Type) wani tsari ne na rarraba dausayi da aka ƙirƙira a ƙarƙashin Yarjejeniyar Ramsar da nufin zama hanyar cikin sauri don gano manyan nau'ikan dausayi don manufofin Yarjejeniyar.[4]
Dausayin Teku/Gaɓar Teku
[gyara sashe | gyara masomin]- Ruwan Gishiri (Saline water):
- Madawwami (Permanent):
- (A) Madawwamin ruwan teku maras zurfi: Kasa da mita 6 na zurfi lokacin da ruwa ya koma (low tide); ciki har da kwarurukan teku (bays) da mashigai (straits)
- (B) Shimfiɗar ciyawar teku ta ƙarƙashin ruwa (Marine subtidal aquatic beds): Tsire-tsire na ƙarƙashin ruwa; ciki har da ciyawar kelp da shimfiɗar ciyawar teku, da filayen ciyawar teku na wurare masu zafi
- (C) Duwatsun murjani (Coral reefs)
- Gaɓar teku (Shores):
- (D) Gaɓar teku mai duwatsu
- (E) Gaɓar teku ta yashi ko tsakuwa
- Madawwami (Permanent):
- Ruwan gishiri ko ruwan da bai nuna gishiri sosai ba (brackish water):
- Yankin da ruwa ke hawa da sauka (Intertidal):
- (G) Filayen laka, yashi ko gishiri na tsakanin igiyoyin ruwa
- (H) Dausayin gishiri na tsakanin igiyoyin ruwa
- (I) Dausayi mai bishiyoyi na tsakanin igiyoyin ruwa
- Ƙananan tafkuna na gaɓar teku (Lagoons):
- (J) Ƙananan tafkuna na gaɓar teku masu gishiri-gishiri
- Ruwan mashigar kogi zuwa teku (Estuarine):
- (F) Ruwan mashigar kogi zuwa teku
- Yankin da ruwa ke hawa da sauka (Intertidal):
- Ruwa mai gishiri, gishiri-gishiri, ko Ruwa mai Daɗi (fresh water):
- Na ƙarƙashin ƙasa (Subterranean):
- (Zk(a)) Tsarin karas (Karst) da sauran tsarin ruwa na ƙarƙashin ƙasa
- Na ƙarƙashin ƙasa (Subterranean):
- Ruwa mai Daɗi (Fresh water):
- Ƙananan tafkuna (Lagoons):
- (K) Ƙananan tafkuna na ruwa mai daɗi na gaɓar teku
- Ƙananan tafkuna (Lagoons):
Dausayi na Cikin Ƙasa (Inland wetlands)
[gyara sashe | gyara masomin]- Ruwa mai Daɗi (Fresh water):
- Ruwa mai gudu:
- Madawwami:
- Madawwamin madatsar ruwan kogi na cikin ƙasa (river deltas) (L)
- Madawwamin ƙoramu/koguna/rafuka (M)
- Maɓuɓɓugar ruwa mai daɗi, oases (Y)
- Rafuka/koguna na wasu lokuta ko masu ɗaukewa (N)
- Madawwami:
- Tafkuna/wuraren lami (pools):
- Madawwami > 8 ha (O)
- Madawwami < 8 ha (Tp)
- Na wasu lokuta / Masu ɗaukewa > 8 ha (P)
- Na wasu lokuta / Masu ɗaukewa < 8 ha (Ts)
- Dausayi a kan ƙasa maras rurruven ganye (inorganic soils):
- Madawwami (wanda ciyayi suka mamaye) (Tp)
- Madawwami / Na wasu lokuta / Masu ɗaukewa (wanda ganyayen daji suka mamaye) (W)
- Madawwami / Na wasu lokuta / Masu ɗaukewa (wanda bishiyoyi suka mamaye) (Xf)
- Na wasu lokuta / Masu ɗaukewa (wanda ciyayi suka mamaye) (Ts)
- Dausayi a kan ƙasar fiti ko rurruven ganye (peat soils):
- Madawwami (marar bishiyoyi) (U)
- Madawwami (mai bishiyoyi) (Xp)
- Dausayi a kan ƙasa maras rurruven ganye ko ƙasar fiti:
- Dausayi a kan ƙasa maras rurruven ganye ko ƙasar fiti / Maɗaukakin yanki (alpine) (Va)
- Dausayi a kan ƙasa maras rurruven ganye ko ƙasar fiti / Tundra (Vt)
- Ruwa mai gudu:
- Ruwa mai gishiri, gishiri-gishiri ko ruwa mai sinadarin alkali:
- Tafkuna
- Madawwami (Q)
- Na wasu lokuta / Masu ɗaukewa (R)
- Dausayi/wuraren lami
- Madawwami (Sp)
- Na wasu lokuta / Masu ɗaukewa (Ss)
- Tafkuna
- Ruwa mai daɗi, mai gishiri, gishiri-gishiri ko mai sinadarin alkali:
- Ruwan zafi na ƙarƙashin ƙasa (Geothermal) (Zg)
- Na ƙarƙashin ƙasa (Zk(b))
Dausayi Na Ƙirƙirar Ɗan Adam
[gyara sashe | gyara masomin]- (1): Guraren kiwon kifi (Aquaculture ponds)
- (2): Wuraren tara ruwa (wuraren shan dabbobi na gona, ƙananan tankunan ruwa, ko yankin da bai kai hekta 8 ba)
- (3): Ƙasar da ake yi wa feshin ruwa (Irrigated land)
- (4): Ƙasar noma da ambaliyar ruwa ke shafa a wasu lokuta
- (5): Guraren haƙar gishiri
- (6): Guraren ajiye ruwa/Madatsun ruwa (Reservoirs)
- (7): Guraren da aka tona (Excavations)
- (8): Guraren tace gurbataccen ruwa (Wastewater treatment areas)
- (9): Hanyoyin ruwa (Canals) da magudanun ruwa ko ramuka
- (Zk(c)): Tsarin karas (karst) na ƙirƙirar ɗan adam da sauran tsarin ruwa na ƙarƙashin ƙasa
Nassoshi
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 3 "The Convention on Wetlands". Ramsar. Retrieved 3 October 2016.
- ↑ Ramsar.org: Ramsar Sites Information Service website, by Wetlands International. Accessed 03.10.2016.
- ↑ "Ramsar Information Paper no. 5: the criteria for identifying wetlands of international importance" (PDF). The Ramsar Convention Secretariat. Retrieved 21 September 2018.
- ↑ "Ramsar Classification System for Wetland Type", Annex I of the Information sheet
Hanyoyin Haɗi na Waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Ramsar Sites Information Service.org: Official List of all Ramsar Sites website—ta hanyar Sabis ɗin Bayanai na Guraren Ramsar
- Ramsar Sites Information Service.org—hotunan guraren Ramsar
- Ramsar.org: Ramsar Convention website