Jump to content

Wikipedia:Gasar Mata da Al’adun Gargajiya 2025 a Hausa Wikipedia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Mata da Al’adun Gargajiya 2025 a Wikipedia Hausa gasa ce ta duniya da ake gudanarwa a Wikipedia a kowace shekara a watan Fabrairu da Maris don rubuta labaran al’adun gargajiya da rawar da mata ke takawa a tatsuniyoyi daga sassa daban-daban na duniya. Wannan shiri ne na Wikipedia da aka tsara bisa ga gasar daukar hoto Wiki Loves Folklore (WLF) da ake gudanarwa a Wikimedia Commons don adana al’adun gargajiya na duniya.

Babban burin wannan gasa shine tattara makalu kan bambance-bambancen al’adu a cikin Wikipedia da sauran shirye-shiryen Wikimedia Foundation. A wannan shekara, za mu mayar da hankali kan batutuwa masu alaka da mata, tarihin rayuwar mata, da kuma batutuwan da suka shafi jinsi a cikin taken babba na Mata da Al’adun Gargajiya 2025. Wannan shiri na da nufin rage gibin jinsi a Wikipedia ta hanyar bincike da gabatar da muhimman batutuwa da suka shafi al’adun gargajiya da gudunmuwar mata.

Tun daga shekarar 2019, an kara gasar rubuce-rubuce a Wikipediya mai harsuna da dama tare da gasar Wikimedia Commons, kuma an sanya shirin a Meta don bada damar hadin gwiwa tsakanin harsuna, Wikipediya daban-daban, da kuma sauran shirye-shiryen Wikimedia, don kara habaka burin mu na 'Wiki Loves' a duniya.

Makalu da za a rubuta dole ne su dace da jigon gasa, wato za a iya samun batutuwa da yawa masu dangantaka da jigon, kamar bukukuwa, raye-raye, abinci, sutura, da rayuwar yau da kullum, musamman wadanda suka danganci al’adun gargajiya na yankuna daban-daban. Kuna da ’yancin zabar makala daga jerin batutuwan da aka samar ko kuma zabar wani batu na kanku matukar yana da alaka da taken gasar kuma yana mayar da hankali kan rage gibin jinsi a Wikipedia. Al’adun gargajiya na da ma’anoni daban-daban ga kowane yanki, kuma wannan gasa tana taimakawa wajen bunkasa abun ciki, inganta tattaunawa tsakanin al’adu, da kuma karfafa girmamawa ga hanyoyin rayuwa daban-daban.

Lokutan Gasa

[gyara masomin]

1 Fabrairu 2025 00:01 UTC – 31 Maris 2025 11:59 UTC

Taken Gasa

[gyara masomin]
  • Al’adun Gargajiya: Masu gasa ana bukatar su bincika batutuwa daban-daban masu nasaba da al’adun gargajiya daga sassa daban-daban na duniya. Ana maraba da batutuwa kamar bukukuwa, raye-raye, kiɗa, wasanni, abinci, sutura, tatsuniyoyi, wasan kwaikwayo, addini, almara, da sauran batutuwan da suka shafi al’adun gargajiya. Wannan na bada damar zurfafa fahimta game da al’adu masu tarin yawa na duniya da kuma adana su don amfanin duniya baki daya.
  • Mata a cikin Al’adun Gargajiya: Wannan jigo yana fadada tattaunawa don jaddada gudunmuwar da mata da mutane masu jinsi daban-daban suka bayar a cikin al’adun gargajiya. Masu gasa za su iya bincika labaran mata masu fasaha, ’yan rawa, mawaka, masu kidan gargajiya, da kuma yadda mata ke fitowa a cikin tatsuniyoyi da almara. Hakanan ana iya rubuta makalu kan mata mayaka, matsafa, da yadda ake kallon nau’in jinsi a cikin al’adun gargajiya.

Ka’idoji da Dokoki

[gyara masomin]
  • Sabuwar makala ko fadada wata dole ne ta kai akalla 3000 bytes da/ko 300 kalmomi.
  • Ba a yarda da makala da aka fassara da na’ura ba tare da ingantawa ba.
  • Sabuwar makala ko gyaran da aka yi dole ne ya kasance tsakanin 1 Fabrairu da 31 Maris.
  • Makala dole ne ta kasance a cikin taken gasa wato Mata da Al’adun Gargajiya (Ana yarda da makalu kan Al’adun Gargajiya kawai ko Mata kawai).
  • Ba a yarda da makala da ba ta da haɗi zuwa wasu makalu.
  • Dole ne makalu su kasance da tushe masu inganci kuma su bi ka’idodin Wikipedia wajen amfani da tushe da tsarin rubutu.

Kyaututtuka

[gyara masomin]

Kyaututtukan Duniya

[gyara masomin]

Za a ba da kyaututtuka ga manyan masu gudunmawa (wadanda suka fi rubuta makalu da yawa):

  • Kyauta ta 1: – 300 USD
  • Kyauta ta 2: – 200 USD
  • Kyauta ta 3: – 100 USD
  • Masu gudunmawa mafi kyau 10: – 50 USD

Kyaututtukan Yanki

[gyara masomin]

Za a bayyana daga baya.

Masu Shirya

[gyara masomin]

Mambobin Alkalai

[gyara masomin]

Sakamako

[gyara masomin]
Alƙali Gwanki
Sunan mai amfaniJimillar ƘirƙiraSabbin AbubuwaƘarin BayaniMaki
Mr. Snatch 7587580751
Ibrahim Sani Mustapha6106091609
A Sulaiman Z7878077
Sirjat2828027
Mlamido3303
Gwanki1100
Jimillar Ƙirƙira: 1478 · Sabbin Maƙaloli: 1477 · Maƙalolin da aka faɗaɗa: 1 · Jimillar Maki: 1467