Wikipedia:Gasar Wikipedia25
a shekaru Ashirin da Biyar!
Gasar Bunkasa Hausa Wikipedia, 2025

A ranar 15 ga watan Janairu, 2026, Wikipedia za ta cika shekaru 25 (Silver Jubilee) da kafuwa. An kafa wannan babban kundin ilimi ne a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 2001. Gidauniyar Hausa Wikimedians User Group tana farin cikin kasancewa tare da sauran masu bada gudummuwa a Wikipedia da ma sauran al'ummar duniya wajen gudanar da gagarumin bikin murna da kuma gasar rubutu domin murnar wannan muhimmin lokaci da kuma inganta Wikipedia ta harshen Hausa.

Wikipedia ba kawai kundin ilimi ba ne; taska ce ta ilimin bil'adama baki daya. A cikin shekaru ashirin da biyar, ta tattara bayanai akan kowane fanni na rayuwa domin samar da ilimi kyauta ga kowa, a ko'ina, ba tare da biyan ko sisi ba ko kuma saka talla kamar sauran manyan shafukan intanet na duniya.
Manufar Wikipedia ita ce kowane dan'adam ya samu ilimi akan kowane abu ba tare da shan wahala ko biyan kudi ba.
Menene Manufar Gasar?
Ba da damar kowa ya ba da gudummawa wajen ƙirƙirar sababbin maƙaloli masu inganci a harshen Hausa, a cikin shirye-shiryen farko na murnar cikar Wikipedia shekaru ashirin da biyar (25) da kafuwa.
Wa ya kamata ya shiga?
Kowa na iya shiga! Ko kai sabon marubucin Hausa ne ko tsohon edita mai bada gudummuwa a Wikipedia ta Hausa, wannan damar taku ce. Idan baku da account na Wikipedia, zaku iya kirkirar sabo a nan: Special:CreateAccount.
Me zai biyo baya?
Mu bada gudummuwar bunkasa harshen Hausa kadai abun alfahari ne babba! Amma duk da haka akwai kyaututtuka na musamman na kuɗi, da takardun shaidar karramawa daga gidauniyar Wikimedia Hausa.
Ka'idojin Gasar
Akwai wasu muhamman ƙai'doji da za a bi domin kasance a ciki wannan shiri:
- Dole ya zama an rubuta muƘalar a Hausa Wikipedia kuma da harshen Hausa.
- Muƙala da aka rubuta cikin salo na daidaito da adalci ba tare da son zuciya ba.
- Muƙala da aka rubuta da kyau, a taƙaice, kuma ba tare da kwafin rubutu daga wani wuri ba, ko kuma yawan kurakuran ƙa'idojin rubutun Hausa.
- Muƙala da aka rubuta da ingantattu kuma sanannun manazarta kuma a cikin tsari.
- Yana da kyau muƙalar ta zama tana da hoton a inda hakan ya dace, ko zai kara sa makaranci fahimtar jigon saƙon.
- An bi ƙa'dojin rubutun wikitext ta hanyar amfani da mahaɗa ta ciki da ta waje zuwa wasu shafukan.
- Dukkan bayanan da ke cikin muƙalar su zama masu sahihanci da madogara (references)
- Dole ya zama mai son shiga gasa yana da account na Wikipedia kuma yayi rajista a Dashboard na Gasa
- Sabbin mukaloli da aka kirkira a lokacin gasa ne kadai za'a yi alkalanci a kansu.
A shafuka na kasa akwai karin bayanai masu muhimmanci akan kirkira da kuma inganta mukaloli a Hausa Wikipedia
Alƙalan Gasa
- Domin ƙasancewa cikin alƙalan gasa, zaku iya tura username dinku a wikipedia25@wikimediahausa.org, tare da gajeren bayanin me yasa kuka cancanta.
- Dole ya zama mai son zama alƙalin gasa yana bada gudummuwa a Hausa Wikipedia kuma ya ƙirƙiri mukaloli da kanshi masu inganci.
- Duk alƙalan gasa ba za su iya shiga gasar ba.
Lokuta
Farawa:
15 ga Disamba, 2025
Gamawa:
15 ga Janairu, 2026
Bada kyauta:
Cikin watan Janairu, 2026
Kyaututtuka
- Akwai kyautar kuɗi kwatan miliyan (250,000) ga wanda suka fi kowa ƙirƙirar muƙaloli masu yawa da kuma inganci.
- Akwai sauran kyatuttuka na kayan sawa masu logon Wikipedia25 ga ƙarin mutanen da suka nuna ƙwazo sosae wajen rubuta muƙaloli masu sahihanci da kuma madogara (references).
- Za'a gayyaci mutanen da suka nuna ƙwazo sosae domin amar kyaututtukan a gagarumin bikin bada kyaututtuka da za'a shirya.
GIDAUNIYAR WIKIMEDIA HAUSA