Wilson dos Santos
| Rayuwa | |
|---|---|
| ƙasa | Angola |
| Mutuwa | 1991 |
| Karatu | |
| Harsuna | Portuguese language |
| Sana'a | |
| Sana'a | ɗan siyasa |
| Imani | |
| Jam'iyar siyasa | UNITA |
Fernando Wilson dos Santos (ya rasu a watan Nuwamba 1991)[1][2] ya yi aiki a matsayin wakilin National Union for the Total Independence of Angola (UNITA),[3] wata kungiyar 'yan gwagwarmayar samun 'yanci kai a Angola, zuwa Portugal.[3] Surukinsa, Tito Chingunji, ya yi aiki a matsayin sakataren harkokin wajen UNITA, babbar kungiyar 'yan tawaye da ta yaki gwamnatin dos Santos a yakin basasar Angola.[4] Ya karanci shari'a a Jami'ar Lisbon da Jami'ar Coimbra a ƙarshen shekarun 1960, sannan ya karatu a Cibiyar Nazarin Ƙasa da Ƙasa da ke Geneva.[5]
Mutuwa da bincike
[gyara sashe | gyara masomin]An kashe Wilson dos Santos a watan Nuwamba 1991 da wasu mutane da ba a san ko su waye ba. [6] A cikin shekarar 1990s, Ministan Harkokin Wajen UNITA Tony da Costa Fernandes da Ministan Harkokin Cikin Gida na UNITA Janar Miguel N'Zau Puna sun gano gaskiyar cewa Jonas Savimbi ya ba da umarnin kashe Dos Santos da Chingunji.[7] Mutuwar Dos Santos da Chingunji da sauya sheka na Fernandes da Puna sun raunana dangantakar UNITA da Amurka tare da cutar da martabar Savimbi a duniya. Savimbi ya musanta zargin.[8]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]- Jerin kisan da ba a warware ba
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Brittain, Victoria (1998). Death of Dignity: Angola's Civil War (in Turanci). Pluto Press. ISBN 978-0-7453-1247-7.
- ↑ Minter, William (1994). Apartheid's Contras: An Inquiry Into the Roots of War in Angola and Mozambique (in Turanci). William Minter. ISBN 978-1-85649-266-9.
- ↑ 3.0 3.1 Summary of World Broadcasts. BBC Monitoring Service, 1959.
- ↑ Kukkuk, Leon (2005). Letters to Gabriella. p. 102.
- ↑ The UNITA Leadership. União Nacional para a Independência Total de Angola. 1990. p. 77-78.
- ↑ "Savimbi accepts responsibility for death of two UNITA officials". UPI (in Turanci). Retrieved 2019-11-28.
- ↑ "Savimbi accepts responsibility for death of two UNITA officials". UPI (in Turanci). Retrieved 2019-11-28.
- ↑ Meredith, Martin (2005). The Fate of Africa: From the Hopes of Freedom to the Heart of Despair: A History of 50 Years of Independence. PublicAffairs. p. 604. ISBN 9781586482466.