Jump to content

Winnie Kiiza

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Winnie Kiiza
Leader of Opposition (en) Fassara

Mayu 2016 - ga Augusta, 2018 - Betty Aol Ochan
Member of Parliament of Uganda (en) Fassara

2006 - 2021
Rayuwa
Haihuwa Kasese District (en) Fassara, 26 Nuwamba, 1972 (53 shekaru)
ƙasa Uganda
Mazauni Kampala
Karatu
Makaranta Makarantar Kasuwanci ta Jami'ar Makerere
(1994 - 1996)
Jami'ar Kyambogo
(2002 - 2005)
Jami'ar Makerere
(2019 - 2021)
Harsuna Turanci
Konjo (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da secretary (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Forum for Democratic Change (en) Fassara
Alliance for National Transformation (mul) Fassara
winniekiiza.com

Winifred Kiiza (an haife ta a ranar 26 ga watan Nuwamba 1972) malama ce kuma 'yar siyasa 'yar ƙasar Uganda, wacce ta yi aiki a matsayin Jagorar 'yan adawa a Majalisar Ugandan, daga watan Mayu 2016 [1] har zuwa watan Agusta 2018. [2] Betty Aol Ochan ta maye gurbinta a matsayin shugabar adawa. [3]

Ta kuma kasance 'yar majalisa mai wakiltar matan gundumar Kasese a majalisar dokokin Uganda ta 10 a shekarar (2016 zuwa 2021). [4]

Tarihi da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Winifred Kiiza a ranar 26 ga watan Nuwamba 1972, a Ƙauyen Nsenyi, ƙaramar hukumar Kisinga, gundumar Kasese, a Yankin Yamma na Uganda. Mahaifiyarta, Modesty Muke, ta kasance mai goyon bayan jam'iyyar siyasa ta Uganda Peoples Congress (UPC), yayin da mahaifinta, Kanyere Constance Muke, na jam'iyyar Democratic Party (DP). Mahaifin Kiiza ya rasu tana da shekara goma, inda ya bar kulawar ta da na ‘yan uwanta a hannun uwa ɗaya tilo da ba ta da aikin yi. [4]

Ta halarci makarantar firamare ta Nsenyi, Makarantar Firamare ta Kajwenge da kuma Kisinga Primary School domin karatun firamare. Don karatun matakin O-Level, ta halarci Makarantar Sakandare ta Saadi Memorial, inda ta koma makarantar Saint Maria Goretti a Fort Portal na shekaru biyu na ƙarshe na makarantar sakandare. [4]

Daga baya ta halarci Kwalejin Nazarin Kasuwanci ta Ƙasa (NCBS), a Nakawa, Kampala, a lokacin ta rikiɗe zuwa Makarantar Kasuwancin Jami'ar Makerere (MUBS). [4]

Gogewa a fagen aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Kiiza ta fara koyarwa ne a makarantar almater ɗinta, Kisinga Primary School, a lokacin hutun da ta yi a jarabawar Senior 4. Haka ta yi a makarantar Saint Maria Goretti, inda ta koyar a can bayan kammala jarrabawar A-Level. [4] A daidai lokacin da aka gina babban asibitin Bwera, ta yi aiki da ɗaya daga cikin ƴan kwangilar, a sashen shagunan su. Daga baya ta yi aiki da wani kamfanin jagora a wurin shakatawa na Sarauniya Elizabeth a kusa. [4]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Kiiza ta shiga harkokin siyasa na cikakken lokaci ya faru ne a kakar siyasar shekarun 1996 zuwa 2001, inda ta yi aiki a ƙaramar hukumar Kasese a matsayin sakatariyar kuɗi ta gundumar. A cikin 2001, an sake zaɓen ta a matsayin 'yar majalisar gundumomi, ta zama Sakatariyar Ilimi kuma daga baya Sakatariyar Ayyukan Jama'a. [4] Ta tsaya takarar kujerar majalisar mata ta gundumar Kasese a shekarar 2006, kan tikitin jam'iyyar siyasa ta Forum for Democratic Change (FDC). Ta yi nasara kuma an zaɓe ta ax 2011 [5] da kuma a cikin 2016. [4]

A watan Mayun 2016, Kiiza, mai shekaru 44, an naɗa ta shugabar 'yan adawa a majalisar dokokin Uganda, wanda ya sa ta zama mace ta farko da ta hau wannan matsayi a tarihin ƙasar.

A ranar 16 ga watan Yuli, 2020, ta ba da sanarwar cewa ba za ta sake neman zama 'yar majalisar dokokin Uganda ba ta sake kawo karshen mulkinta na shekaru 15 a matsayin 'yar majalisar mata ta Kasese duk da cewa har yanzu tana da farin jini. [1] [6]

Kiiza tana da aure kuma uwace. [4] [7]

  • Rikici Kasese
  • Joy Doreen Biira
  1. 1.0 1.1 Observer Reporter (27 May 2016). "FDC's Winnie Kiiza, Ssemujju Nganda eat big". Archived from the original on 27 March 2019. Retrieved 4 November 2017.
  2. Daily Monitor Staff (2 August 2018). "FDC's Amuriat sacks Leader of Opposition Winnie Kiiza". Retrieved 4 August 2018.
  3. Dickens H Okello (3 August 2018). "Betty Aol Replaces Winnie Kiiza as Leader of Opposition". Chimp Reports Uganda. Retrieved 3 August 2018.
  4. 4.0 4.1 4.2 4.3 4.4 4.5 4.6 4.7 4.8 Watchdog Uganda (31 January 2017). "Winnie Kiiza; the exceptional Leader of the Opposition who rose from grass to grace". Watchdoguganda.com. Archived from the original on 7 November 2017. Retrieved 4 November 2017.
  5. Felix Basiime, Enid Ninsiima and Thembo Kahungu (9 August 2012). "FDC's Winfred Kiiza wins Kasese by-election". Nation Media Group. Retrieved 4 November 2017.
  6. Vision Reporter (26 May 2017). "Kizza new Leader of Opposition in Parliament". Retrieved 4 November 2017.
  7. Michael Mubangizi (19 June 2011). "Interview: Kiiza on 'whipping' her husband in Parliament". Archived from the original on 7 November 2017. Retrieved 4 November 2017.