Jump to content

Garin wurma

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Wurma(Kauye))

Wurma gari ne dake a karkashin Karamar Hukumar Kurfi dake Jihar Katsina, Nigeria. Mutanen Wurma hausawa ne kuma masu magana da yaren Hausa.[1]

Garin Wurma gari ne mai dumbin Tarihi Wanda samuwarsa,anlakaba wa garin Suna daga kalmar Wuro kalmar fulani ce garin yakai akalla shekara 100 tun kafin kafuwar Jihar katsina da Kuma gwamanati,inda Mai Mulkin yanzun Alhaji shehu Muhammad Wurma Dan-dadin Wurma ya gaji kujerar Daga Kaka da kakani, Kuma grain ya tara manyan Yan siyasa da kuma Yan boko, kamar su Hon. Mannir shehu tsahon malamin koleji Kuma tsohon shugaban karamar Hukumar Kurfi sannan kuma P.A ga gwamnan Jihar katsina mai ci wato Dr. Dikko Ummaru Radda, Engr. Aliyu Iliyasu Wurma darakta a jami'ar gwamnatin tarayya dake Dutsin-Ma, da dai sauransu. Sannan a fanin zamani ba abarsu a baya ba garin Wurma yana da Makarantar firamari Wurma Modal Primary School da kuma makarantar gaba da firamare wato sakandire duk a garin Wurma.

Mafi akasarin Mutanen Wurma makiyaya ne da Kuma manoma inda suke noma na'ika daban damban na hatsi irinsu Dawa, Wake, Gyada, Gero, Ridi, da sauran kayan hatsi, haka kuma a barsu a baya ba wajen noma Rani.

Abubuwan da suke nomawa

[gyara sashe | gyara masomin]

Sukanyi noman Dawa,gero,wake,masara dakuma sauran kayan abinchin na hausawa.

Yanayin garin Wurma yakasance yanayin Sanyi ko Zafi 36°C garin wanda take karkashin Karamar Hukumar Kurfi wace da girman kasa da yakai kimanin 573Km² da Kuma lambar gidan waya 831 a kidayar shekarar 2006 [2]

Manyan Yan boko na garin

[gyara sashe | gyara masomin]

Yan BOKO

1. Prof. Abdullahi Garba Wurma

2. Dr. Dikko Muhammad Wurma

3. Dr. Ibrahim Amiru Wurma

4. Dr. Bala Ibrahim Wurma

5. Dr. Mannir Shehu Wurma

6. Engr. Aliyu Iliyasu Wurma

7. Engr. Gambo Barau Wurma

8. Dr. Tasi'u Rabi'u Wurma

9.Bar. Sani Yahaya Wurma

  1. "Post Offices- with map of LGA"
  2. "Post Offices- with map of LGA"