Yaƙin Duniya na II

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentYaƙin Duniya na II

Iri world war (en) Fassara
historical period (en) Fassara
Bangare na newest history (en) Fassara da late modern period (en) Fassara
Kwanan watan 2 Satumba 1945
Wuri Rasha
Turai
Afirka
Pacific Ocean
Bahar Rum
Asiya
Tekun Atalanta
Gabas ta tsakiya
Southeast Asia (en) Fassara
Scandinavia (en) Fassara
Yakin Pacific
Battle of the Atlantic (en) Fassara
Tekun Indiya
South Asia (en) Fassara
Arewacin Asiya
Sin
Japan
Kudancin Afirka
Gabashin Afirka
Afirka ta Tsakiya
Asturaliya
Amirka ta Arewa
Amurka ta Kudu
Participant (en) Fassara
Sanadi Secret Additional Protocol to the Molotov–Ribbentrop Pact (en) Fassara
Yana haddasa British pet massacre (en) Fassara
The Holocaust
atomic bombings of Hiroshima and Nagasaki (en) Fassara
Bombing of Dresden (en) Fassara
Allies of the Second World War (en) Fassara
Nazi Germany (en) Fassara
Empire of Japan (en) Fassara
Allied-occupied Germany (en) Fassara
Austriya
League of Nations (en) Fassara
Majalisar Ɗinkin Duniya
Tarayyar Amurka
Kungiyar Sobiyet
Cold War
Adadin waɗanda suka rasu 73,000,000
Hanyar isar da saƙo
Has part(s) (en) Fassara
Yakin Pacific
Attack on Pearl Harbor (en) Fassara
Operation Barbarossa (en) Fassara
Battle of the Scheldt (en) Fassara
Bloody Sunday (en) Fassara
Battle of Madagascar (en) Fassara
Big Week (en) Fassara
Battle of France (en) Fassara
Slovak Republic (en) Fassara
Battle of Aachen (en) Fassara
Mediterranean and Middle East Theater of World War II (en) Fassara
Battle of the Atlantic (en) Fassara
Eastern Front (en) Fassara
Middle East Theater of World War II (en) Fassara
Battle of Britain (en) Fassara
Battle of the Bulge (en) Fassara
Normandy landings (en) Fassara
Operation Flashpoint (en) Fassara
Third Battle of Kharkov (en) Fassara
Bayan harin bom na Vallø a Norway, Afrilu 1945 (WWII)

Yaƙin Duniya na 2 da turanci World War II akan kintse rubutun kamar haka WWII ko WW2, har wayau ana ƙiran shi da turanci Second World War. Yaƙin duniya dai wani yaƙine da duniya baki ɗaya suka afka a ciki wanda ya kwashi tsawon shekaru shida (6) ana gwabzawa, tun daga shekara ta alif 1939 har zuwa shekara ta alif 1945. Mafiya yawan ƙasashen duniya tare da ƙasashe masu ƙarfi su ne suka ja daga a tsakanin su, inda suke yaƙan juna: Hakane ya haifar da gagarumin gumurzu tsakaninsu wanda aƙalla mutane sama da miliyan ɗari ne (100,000,000) suka tsunduma a ciki daga kasashe sama da talatin (30). Mafiya yawan ƙasashen da suka shiga cikin yaƙin sun saka dukkan tattalin arzikin su, da kuma Masana'antunsu da ilimin su na kimiyya da fasaha don ganin sun yi galaba a yaƙin. Yaƙin duniya na II shi ne yaki mafi muni a duniya wanda Dan Adam bai taba gani ba, inda aka samu rasa rayukan mutane daga miliyan 50 zuwa miliyan 85, yawan cinsu fararen kaya ne daga Ƙasar Soviet Union wato Rasha a yanzu da kuma Kasar Sin. An kuma sami kashe-kashe, kisan kiyashi akan Yahudawa, tsarin jefa bama-bamai, mutuwa sanadiyyar yunwa da cututtuka, da kuma amfani da makaman kare-dangi a yaƙin Atomic Weapeons.

Ansoma yaƙin ne daga rana ga watan Satumba, shekara ta alif 1939 zuwa ranar 2 ga watan Satumba, shekara ta alif 1945 tsawon shekaru (6 da kwana daya 1)

Ƙasashen ƙawance Allied Countries sunyi nasara, an kifar da Gwamnatin Nazi dake Jamus, An samu faɗuwar Daulolin yankin Japan dana Italiya, Anfara amfani da Makaman kare dangi wato Atomic weapons, Inganta ayyuka da jiragen sama, rusa kungiyar League of Nations, ƙirƙirar Majalisar Dinkin Duniya wato United Nations, Fara ƙiyayya tsakanin Kasar Amurka da Rasha, fara yaƙin mummuƙe wato Cold war. Jagororin ƙungiyar ƙawance na Kasa da kasa,

Kwamandodi da Shuwagabanni[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Soviet Union Joseph Stalin
  2. United States Franklin D. Roosevelt
  3. United Kingdom Winston Churchill
  4. Jamhoriyar Sin (1912–1949) Chiang Kai-shek

Wa 'yanda ake fada dasu

  1. Nazi Germany Adolf Hitler
  2. Masarautar Japan Hirohito
  3. Masarautar Italy Benito Mussolini

Abubuwan da akayi asaransu An kashe Sojoji: Sama da miliyan 16,000,000 An kashe farin kaya: Sama da miliyan 45,000,000 Adadin rayukan da aka rasa: Sama da miliyan 61,000,000 (1937–1945)

ƙasar Japan da ke son ta mamaye nahiyar Asiya da yankin Pacific, ta fara yaƙi da Kasar Sin tun daga shekara ta alib 1937, duk da cewar babu bangaren da yafito a fili ya ayyanar da yaki akan wanin sa. Ana dai ganin yakin ya soma ne a 1 ga watan Satumbar, shekara ta alib 1939, bayan mamaye ƙasar Poland da ƙasar Jamus tayi, da kuma ƙaddamar da yaki da Kasar Faransa da Ingila sukayi akan kasar Jamus a karshen shekarar 1939 har zuwa farkon shekara ta 1941, sai dai irin gumurzu da shirin da Jamus din tayi ne, hakan yasa ta samu nasarar mallakar kusan duka nahiyar Turai, kuma sai suka kulla ƙawance da kasar Italiya da Japan (Axis powers) a karkashin yarjejeniyar Molotov–Ribbentrop Pact of August 1939, Jamus da ƙasar Soviet sun rarraba tare da mallakar yankunan Turai na kasashe kamar irin su Poland, Finland, Romania da jihohin dake Baltic. Bayan fara yaƙi akan kasashen dake yankin Afirka ta arewa da Afirka ta gabas, da kuma faɗuwar ƙasar Faransa a tsakiyar shekarar 1940. Yaƙin ya koma mafi yawanchi tsakanin ƙasashen Jamus,Italiya da kuma Daular Romania akan Daular Biritaniya. Sai kuma fara Yaƙi a Balkans,Da kuma Fafatawar sararin samaniya a Ingila wato Aerial Battle of Britain da kuma harin sama tare dayin ruwan bomabomai da ƙasar Jamus din tayi wa Birtaniya wato Blitzkrieg, sai kuma fafatawar Mallakar Tekun Atlantik da ya biyo baya, Ana Chikin wannan Bala'in ne sai kuma Kasashen haɗakar (Axis Powers) a turai suka ƙaddamar da hari akan kasar Soviet Union (Rasha) wato Operation Barbarossa a ranar 22 ga watan june, shekara ta alib 1941 , hakan yasa suka bude wani sabon shafin yaƙin mafi muni a tarihi, A kuma watan December, shekara ta alib 1941, Japan ta kaddamar da wani hari a kasar Amurka da wasu yankunan turawa dake yankin tekun Pacific. Hakane yasa kasar ta Amurka ta shiga Yaƙin a gefen Allied Countries kuma ta Ayyana yaƙi akan ƙasar Japan, hakan yasa ta samu goyon bayan kasar Biritaniya, amma sai ƙasashen dake ƙawance da Japan na turawa suma suka mara wa Japan din baya, hakane yasa Japan ta ƙwace yawancin yankunan turawa dake yankin tekun Pacific, wanda yawancin kasashen Asiya suke ganinsa a matsayin wani shiri ne daga ƙasashen yamma na yin mamaye a yankunan su, amma kuma bayan ƴan Watanni da suka gane wa idanuwan su irin zalunchin da Axis Powers keyi yasa dagabisani ra'ayin mutanen ƙasashen ya juya akan su. Yaki ya tsaya a shekara ta 1945 bayan Japan ta miƙa wuya, kuma Jamus da Italiya suma anyi galaba akanmsu a arewacin Afirka da gabashin ta, da kuma gagarumar nasarar da Red Army suka yi akan jamus da Italiya a garin Stalingrad dake Soviet Union a shekara alib 1943, da kuma mamaye Sicily da Italiya, da nasarar kasashen kawance (Allied Powers) a yankin Pacific, a shekara ta alib 1944, kasashen ƙawance sun ƙwace yankin Faransa daga hannun Jamus wato D-day Invasion kuma itama kasar Soviet Union ta dawo da duka yankunan ta daga hannun Jamus da ƙawayenta. Sa'annan kuma a shekara ta alib 1944, zuwa shekara ta alib 1945, kasar Japan ta sha kashi sosai a yankin Asiya, musamman a fafatawar da suka yi da Amurka a Tekun Pacific wato Battle Of Midway,da kuma tsakiyar kasar Sin da kasar Burma, hakan ya sanya su rasa dukkanin yankunan da suka mamaye.

Yaƙi a nahiyar turai ya ƙare ne sanadiyar mamaye Jamus da ƙasashen kawance (Allied Countries) da ƙasar Soviet suka yi wanda yakai ga kama garin Berlin da mutuwar Adolf Hitler da miƙa wuyan da Jamus tayi a 8 ga watan May, shekara ta alib 1945. Bayan Potsdam Declaration daga kungiyar ƙawance a 26 ga watan July, shekara ta alib 1945.

yakin duniya na biyu

ƙin da ƙasar Japan tayi na miƙa wuya, yasa ƙasar Amurka ta jefa mata Makamin ƙare dangi wato atomic bomb a garuruwan Hiroshima da Nagasaki a 6 da 9 ga watan Augusta. Da kuma mamaye tsibirin archipelago imminent, da ganin irin asarar rayukan da ake yi, da kuma mamayen yankuna da kasar Soviets ta ke chi gaba dayi a garuruwan Manchuria da tsibirin Kuril dake arewacin ƙasar ta Japan, hakan yasa Sarkin ƙasar japan wato Hirohito a 2 ga watan satumba, shekara ta alib 1945. ya miƙa wuya, wannan ya bada damar yin nasarar sojojin ƙawance a nahiyar Asiya, sai kuma aka fara tuhumar kasar Jamus da japan akan laifukan yaƙi a kotunan International Military Tribunal (IMT) da kuma The International Military Tribunal For The Far East ko kuma (IMTFE).

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.