Yaƙin Sidi Semiane
Appearance
| Iri | faɗa |
|---|---|
| Ƙasa | Aljeriya |
Yakin Sidi Semiane an ɗauki tsawon sa'o'i 4 ana gwabza yaki na 'yancin kai na ƙasar Aljeriya a ranar 20 ga watan Mayun 1957 a tsaunin Dahra a Wilaya IV.[1]
Dakarun Faransa sun haɗa sojoji 850 domin kai farmakin ba-zata kan mujahidai 35 na ƙungiyar 'yantar da ƙasar Aljeriya a matsayin ramuwar gayya ga nasarar da Aljeriya ta samu a yakin Sidi Mohand Aklouche a ranar 26 ga watan watan Afrilun shekarar 1957.[2] An kwashe sama da sa'o'i 4 ana gwabzawa, kuma kwamandan Faransa Gaudion da bataliyarsa sun sha kashi mai tsanani wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 150 da raunata fiye da 200, yayin da 'yan Algeria suka rasa maza biyu kawai, Si Slimane da Si Mahfoud. [3] [4]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Archives d'Algérie (in Faransanci). Marsa éditions. November 2004. p. 80.
- ↑ Archives d'Algérie (in Faransanci). Marsa éditions. November 2004. p. 80.
- ↑ Chérif, Chérif (5 July 2004). "On était 35 moudjahidine contre 850 soldats français". L'Expression.
- ↑ Chérif, Mohamed (2 November 2004). "La bataille de Sidi Semiane". L'Expression.