Yaƙin Tepe
| ||||
| Iri | faɗa | |||
|---|---|---|---|---|
| Bangare na | Kamfen ɗin Kamerun | |||
| Kwanan watan | 25 ga Augusta, 1914 | |||
| Participant (en) | ||||
Yakin Tepe (ko Tebe) a ranar 25 ga Agusta 1914 shine karo na farko tsakanin sojojin Jamus da Birtaniyya a lokacin yakin Kamerun a yakin duniya na farko . Rikicin dai ya faru ne a kan iyakar Najeriyar Birtaniya da Jamus Kamerun, inda ya kare da nasarar Birtaniya da kuma janyewar Jamus daga tashar.
Gabatarwa
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 4 ga watan Agustan shekarar 1914, Birtaniya ta shelanta yaki da Daular Jamus a farkon yakin duniya na farko.[1] A ranar 8 ga watan Agusta, wasu dakaru daga Rundunar Sojojin Yammacin Afirka sun tashi daga Kano a arewacin Najeriya zuwa yankin Kamerun da Jamus ta yi wa mulkin mallaka. Wadannan sojojin Birtaniya na farko sun ketara kan iyakar kasar Jamus a ranar 25 ga Agusta.
Yaƙi
[gyara sashe | gyara masomin]Sojojin dawakin Birtaniya sun yi arangama da sojojin Jamus a tashar kan iyaka da ke Tepe a kan kogin Benue a ranar 25 ga watan Agusta. Bayan an gwabza kazamin fada da sojojin Jamus suka janye sannan turawan ingila suka mamaye tashar. An samu asarar rayuka kaɗan daga yaƙin. Mamaya da Birtaniyya ta yi wa tashar ta bai wa dakarun nasu damar kara tura gabas zuwa tungar Jamus da ke Garua.[2] Turawan Ingila sun sha kashi a yunƙurinsu na kai sansani a can a yaƙin farko na Garua kwanaki kaɗan bayan rikicin Tepe.
