Yakin Begums
| Bayanai | |
|---|---|
| Ƙasa | Bangladash |

A siyasar Bangladesh, kalmar yakin Begums (Bengali: বেগমদের যুদ্ধ) tana nufin adawar siyasa tsakanin Sheikh Hasina Wazed ta Awami League da takwararta Begum Khaleda Zia ta Jam'iyyar Nationalist[1][2][3][4]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Rikicin siyasa tsakanin Awami League da Jam'iyyar Nationalist Party ya samo asali ne tun kafin samun 'yancin kai na Bangladesh inda batun wanda ya yi shelar 'Yancin Bangladesh, a cewar majiyoyi da yawa Sheikh Mujibur Rahman[5][6] mahaifin Sheikh Hasina wanda ya shelanta 'yancin kai na Bangladesh amma ga wasu Ziaur Rahman[7] shi ne mijin Khaleda Zia. Dangane da wadannan sabani shekaru da dama da suka gabata an yi ta adawa a tsakaninsu wanda ya haifar da tarzoma a cikin kasa.[3]
Bayan
[gyara sashe | gyara masomin]A tsawon shekaru, amfani da kalmar ya ragu yayin da Sheikh Hasina ke kan karagar mulki tun 2009 kuma yayin da Khaleda ke tsare da shi na tsawon lokaci a sakamakon haka mutane da yawa sun yi imanin cewa Hasina ce kawai ta lashe wannan hamayyar siyasa har Hasina ta tsere zuwa Indiya a tashin hankalin dalibai a ranar 5 ga Agusta, 2024.[3][8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Web Desk (2 December 2013). "Battle Of The Begums". OutLookIndia. Retrieved 14 May 2023
- ↑ NAYAR, KULDIP (2018-03-04). "The Battle of the Two Begums of Bangladesh". www.thecitizen.in. Retrieved 2023-05-14.
- 1 2 3 "Bangladesh grows tired of the Battling Begums". BBC News. 2018-02-11. Retrieved 2023-05-14
- ↑ Kapila, Subhash. "The Battle of the Begums". www.boloji.com. Retrieved 2023-05-14
- ↑ League, Bangladesh Awami. "10th day of April, 1971: The Proclamation Of Independence". www.albd.org. Retrieved 2023-05-14.
- ↑ Bangladesh Independence Day, 26 March - Assumption University of Thailand". www.au.edu. Retrieved 2023-05-14
- ↑ Journal, South Asia (2021-03-30). "Bangladesh: Declaration of Independence and Falsehood!". South Asia Journal. Retrieved 2023-05-14.
- ↑ Amza, Azaera. "PM Hasina on top in battle of the Bangladesh Begums". TRT World. AP. Retrieved 2023-05-14