Yakolo Indimi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Yakolo Indimi
Rayuwa
Haihuwa 19 ga Maris, 1977 (47 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa, Mai tsara tufafi da business executive (en) Fassara

Yakolo Indimi (an haifeta ranar 19 ga watan Maris, 1977) kuma an santa da Rahama Indimi ta kasance sananniyar yar kasuwa kuma mai taimaka ma al'uma. Ta kasance shugaba-(CEO) kuma wacce ta samar da gidauniyar Yakolo indimi. Ta kasance darakta ce a Oriental Energy Resources Limited kuma yanzu haka darakta ce a Oriental OML 115. kuma ta kasance wacce ta ci lambar girma na duniya a shekarar 2019.[1]

Farkon rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Yakolo Indimi ne a Maiduguri, dake jihar Borno a shekarar alif 1977, ta kasance ƴar shahararran ɗan kasuwa Mohammed Indimi da kuma Hajiya Fatima Mustapha Haruna.[2][3] Tayi karatu a makarantan University Primary dake Maiduguri. Ta yi karatun firamare a University Primary School, Maiduguri, a Jihar Borno sannan aka kai ta makarantar kwana a kasar Masar inda ta yi karantun sakandare boko da addini a El Nasr Girl College, da ke Alexandria, wadda ta kammala a 1989. Yakolo ta yi karartu a Jami’ar Lynn, Boca Raton da ke Florida a kasar Amurka. A nan ta yi digirina na farko a fannin kimiyyar aikin likitanci sannan ta yi digiri na biyu fannin gudunarwa na kasa da kasa.[4]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ta kammala yi wa kasa hidima a 2000, ta samu aiki kamfnin mahaifina na Oriental Energy Resources, inda ta yi aiki a sassa da kuma matakai daban-daban na tsawon shekara 20. Yanzu haka darekta ce rijiyar hakar mai ta OML 115. A shekarar 2010, ta shiga harkar ado da kwalliya inda ta bude kamfani mai suna Fashion Café, daga bisani ta sake samar wani kamfanin mai suna Devas Petal a shekarar 2015.[5][6]

Ayyukan kyautatawa[gyara sashe | gyara masomin]

Yakolo Indimi ta kafa gidauniya mai suna Yakolo Indimi Foundation, da manufar yaki da talauci, kawar da yunwa, isar da kayan agaji da samar da ayyukan kiwon lafiya ta hanyar samar da kudade da kayan tallafi ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a sansanonin yan gudun hijirar da ke cikin Borno.[7][8]

Lambar yabo[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2019, Indimi ta samu lambobin yabo a babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 da aka yi a birnin New York dake kasar Amurka, a bisa gudummawa da take bayarwa don cimma burin ci gaba mai dorewa (Sustainable Development Goals SDGs), a matakin na farko # 1 Babu [9]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://dailytrust.com/my-parents-lifestyle-influenced-mine-yakolo-indimi
  2. Alhassan, Amina (25 September 2015). "Dad allowed us to learn from our mistakes – Yakolo Indimi". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 6 October 2020.
  3. "Rahma Indimi's Fantasy". THISDAYLIVE. This Day Live. 13 September 2020. Retrieved 6 October 2020.
  4. Olorunyomi, Adebola (28 January 2019). "Meet The Young Female Entrepreneurs Rocking ABUJA". City People Magazine. Retrieved 6 October 2020.
  5. "Rahama Babangida takes over Abuja fashion world by storm". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics. 3 July 2015. Retrieved 6 October 2020.
  6. "Rahama Indimi's new vocation". Tribune Online. 18 November 2017. Retrieved 6 October 2020.
  7. "Rahma Indimi is helping 'the most vulnerable people in our society as she covers May 2019 Edition of Pleasures Magazine – Pleasures Magazine". Pleasure Magazine. Archived from the original on 23 January 2020. Retrieved 6 October 2020.
  8. "Reaching Out To Less Privileged My Joy - Rahma Indimi". Leadership Newspaper. 15 September 2020. Archived from the original on 9 October 2020. Retrieved 6 October 2020.
  9. "The Permanent Mission of Nigeria to the United Nations A Celebration of Peace". blacktiemagazine.com. Retrieved 6 October 2020.