Yakubu Gowon

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Yakubu Gowon tsohon soja ne kuma ɗan siyasan Nijeriya ne. An haife shi a shekara ta 1934 a Lur, Arewacin Najeriya (a yau jihar Filato). Yakubu Gowon shugaban kasar Nijeriya ne daga Agusta 1966 zuwa Yuli 1975 (bayan Johnson Aguiyi-Ironsi - kafin Murtala Mohammed). A karkashin mulkin Gowon ne masu fafutukar neman ficewa daga Nijeriya daga al'umman ibo karkashin jagorancin shugabandu Odemegwu Ojukwu suka kafa kasar Biafara, inda gwamnatin Gowon din tafito ta yakesu har sai da suka mika wuya.