Jump to content

Yarjejeniyar Nakuru

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentYarjejeniyar Nakuru
Iri peace treaty (en) Fassara

Yarjejeniyar Nakuru, wacce aka sanya hannu a ranar 21 ga watan Yuni, 1975, a Nakuru, Kenya, ƙoƙari ne na ceto yarjejeniyar Alvor, wacce ta bai wa Angola 'yancin kai daga 'yan mulkin mallaka na Portugal da kuma kafa gwamnatin riƙon kwarya.[1] Yayin da Yarjejeniyar Nakuru ta haifar da sulhu tsakanin ƙungiyoyin masu kishin ƙasa guda uku - Popular Movement for the Liberation of Angola (MPLA), National Liberation Front of Angola (FNLA), and National Union for the Total Independence of Angola (UNITA) - shi ne sulhu mai rauni da ya wargaje a ranar 9 ga watan Yuli, 1975.[1]

Manyan shugabannin 'yan awaren uku, Agostinho Neto na MPLA, Jonas Savimbi na UNITA, da Holden Roberto na FNLA sun haɗu a Nakuru daga ranakun 15-21 ga watan Yuni.[2] Shugaban Kenya Jomo Kenyatta ne ya jagoranci tattaunawar. Shugabannin sun yi Allah-wadai da yin amfani da karfi a matsayin hanyar magance matsalolin, sannan suka sake amincewa da ajiye makamansu da kuma kwance ɗamarar fararen hula.[2]

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]
  1. 1.0 1.1 McDannald, Alexander Hopkins. The Americana Annual: An Encyclopedia of Current Events, 1976. Page 86.
  2. 2.0 2.1 Wright, George (1997). The Destruction of a Nation: United States' Policy Towards Angola Since 1945. Pluto Press. pp. 60–61. ISBN 9780745310299.