Yasser Abu Shabab
| Rayuwa | |
|---|---|
| Haihuwa | Rafah, 19 Disamba 1993 |
| ƙasa | State of Palestine |
| Mutuwa |
Beersheba (en) |
| Yanayin mutuwa |
death in battle (en) |
| Karatu | |
| Harsuna | Larabci |
| Sana'a | |
| Sana'a |
mercenary (en) |
| Mamba |
Popular Forces (en) |
| Aikin soja | |
| Fannin soja |
Popular Forces (en) |
| Ya faɗaci | Yaƙin Gaza |
| Imani | |
| Addini | Musulunci |
Yasser Abu Shabab(19 Disamba 1993 ko 27 ga Fabrairu 1990 - 4 Disamba 2025) ɗan gwagwarmayar Falasdinu ne kuma shugaban Popular Forces, ƙungiyar masu adawa da Hamas a zirin Gaza. Shi Badawiyya ne na kabilar Tarabin.[1][2][3][4] Abu Shabab ya fito a matsayin dan adawa na cikin gida ga Hamas a yakin Gaza. A cikin watan Mayun 2024, kungiyarsa ta fara wawashe manyan motocin agaji, suna masu cewa yana bayar da tsaro ga ayarin motocin agaji da ke shiga Gaza a lokacin farmakin Rafah.[5][4]An ruwaito cewa Abu Shabab yana bayan ayarin motocin Kerem Shalom da wawure dukiyar kasa[9]. Isra'ila ta fara baiwa kungiyar Abu Shabab makamai da kayan aiki a shekarar 2025.[6] Isra'ila ta fara baiwa kungiyar Abu Shabab makamai da kayan aiki a shekarar 2025.[7] Tun a watan Yunin 2025 kungiyar da yake jagoranta ke iko da wasu yankunan gabashin Rafah[2]Bayan mutuwar Yasser Abu Shabab, Ghassan Duhine ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban rundunar soji.[8]
Rayuwar farko da ayyukan aikata laifuka
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Abu Shabab a gabashin Rafah a ranar 19 ga Disamba 1993,[9]ko kuma mai yiyuwa ne 27 ga Fabrairu 1990.[10]Ya kasance dan kabilar Tarabin Badawiyya kuma yana da ɗa mai suna Hassan Abu Shabab.[11][12][13]A cewar majiyoyin da ke kusa da Abu Shabab, ya bar makaranta tun yana karami ya shiga harkar safarar miyagun kwayoyi.[14][15]Ya kuma kasance yana safarar taba sigari da sauran kwayoyi zuwa zirin Gaza.[16]A shekara ta 2010, Abu Shabab ya yi yunkurin shiga jami'an tsaron Hamas.[11]A shekara ta 2015, Hamas ta kama shi bisa zargin fataucin miyagun kwayoyi tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yarin Asda da ke yammacin Khan Yunis.[14]
Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Iyalan Abu Shabab sun yi watsi da shi saboda "baya goyon bayan sojojin yahudawan sahyoniyawan" kuma sun ce "ba su da wata alaka da wadanda ke kewaye da shi su kawar da shi nan take"[17]Hamas dai ta sanya Abu Shabab a cikin manyan wuraren da suka kai musu hari, lamarin da ya sa suka yi yunkurin kashe shi har sau biyu, ba su yi nasara ba. A ranar 4 ga Disamba 2025, an harbe Abu Shabab tare da raunata a kusa da Rafah. Wata majiyar tsaro ta Isra'ila ta ce ya mutu ne sakamakon raunukan da ya samu jim kadan kafin isarsa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Soroka da ke Biyersheba a Isra'ila.
MANAZARTA
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.haaretz.com/middle-east-news/palestinians/2025-05-26/ty-article/.premium/new-palestinian-militia-operating-in-southern-gaza-local-sources-say/00000197-0cd9-d165-a9ff-1dff7dc00000
- 1 2 Tondo, Lorenzo (5 June 2025). "Israel accused of arming Palestinian gang who allegedly looted aid in Gaza". The Guardian. ISSN 0261-3077. Retrieved 6 June 2025.
- ↑ Eichner, Itamar; Halabi, Einav (5 June 2025). "Liberman accuses Netanyahu of arming ISIS-linked militias in Gaza; PM's office offers no denial". Ynetnews. Retrieved 6 June 2025.
- 1 2 Netanyahu Says Israel Fighting Hamas 'In Various Ways' Amid Claims It Armed ISIS-affiliated Gaza Militia". Haaretz. 5 June 2025
- ↑ Doak, Sam (29 May 2025). "How the rollout of new Gaza aid system collapsed into chaos". Sky News. Retrieved 4 June 2025.
- ↑ Ibrahim, Sally (19 November 2024). "Gaza: Hamas security forces kill 20 aid looters 'linked to Israel, ISIS'". The New Arab.
- ↑ Fabian, Emanuel (5 June 2025). "Sources confirm Israel arming Gazan gang to bolster opposition to Hamas". The Times of Israel. Retrieved 5 June 2025
- ↑ https://www.jpost.com/middle-east/article-879358
- ↑ Janardhanan, Vinod (11 June 2025). "Drug trafficker, traitor, gangster: What you didn't know about Yasser Abu Shabab, the anti-Hamas clan leader helping Israel in Gaza". WION. Retrieved 4 August 2025.
- ↑ https://www.middleeasteye.net/live-blog/live-blog-update/who-militia-leader-abu-shahab-man-wanted-court-gaza-report
- 1 2 van der Merwe, Ben; Doak, Sam (4 October 2025). "Guns, cash and American aid: Investigation reveal Israel's support for Gaza militia". Sky News. Retrieved 4 December 2025.
- ↑ Guns, cash and American aid: Investigation reveal Israel's support for Gaza militia
- ↑ "'Popular Forces': Who are the Gaza gangsters being armed by Israel?". Middle East Eye. 14 June 2025
- 1 2 https://www.abc.net.au/news/2025-07-14/gaza-aid-looting-gangs-yasser-abu-shabab-israel-netanyahu-hamas/105501926
- ↑ https://www.ynetnews.com/article/s1skwx7xgx
- ↑ https://apnews.com/article/gaza-armed-groups-hamas-israel-looting-b3033fd46a25a6382c8e13d3b4ae7f42
- ↑ https://www.theguardian.com/world/2025/jun/06/netanyahu-defends-arming-palestinian-clans-accused-of-ties-with-jihadist-groups