Yunkurin juyin mulki a Nijar, 2021
| ||||
| Iri |
attempted coup d'état (en) | |||
|---|---|---|---|---|
| Kwanan watan | 31 ga Maris, 2021 | |||
| Ƙasa | Nijar | |||
| Adadin masu shiga | unknown value | |||
| Adadin waɗanda suka rasu | unknown value | |||
| Adadin waɗanda suka samu raunuka | unknown value | |||
| Number of arrests (en) |
unknown value | |||
Yunkurin juyin mulkin ƙasar Nijar dai wani yunkuri ne da niyar kifar da gwamnati mai ci da ya faru ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2021 da misalin karfe 3 na dare; WAT, (2 na safe UTC) bayan harbin bindiga ya tashi a titunan birnin Niamey, babban birnin ƙasar, kwana biyu kafin rantsar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa na ƙasar, Mohamed Bazoum.
Yunkurin juyin mulki ya faru ne ta silar sojoji, kuma an danganta lamarin ga rundunar soja Sama da ke yankin Filin jirgin saman Niamey da alhakin kitsawa. Shugaban da da ake zargi da jagorancin shirin shi ne Kyaftin Sani Saley Gourouza, wanda ke kula da tsaro a sansanin.[1] Bayan an cimma daƙile yunkurin juyin mulkin, an kama masu ruwa da tsaki game da shirin ko aikata laifin.[2]
Yanayi
[gyara sashe | gyara masomin]Yunkurin juyin mulkin ya zo yanayin da ƙasar ta Nijar ke Yaƙi a yankin Sahel, tare da samun masu ayyukan ta'addanci da sauran tashe-tashen hankula tsakanin ƙabilu mabanbanta. Kasashen tankin Sahel suna samun taimakon Faransa a kan 'yan ta'addan yankin daga Operation Barkhane. A shekara ta 2020, juyin mulki ne ya yi silar hambarar da gwamnatin Shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keïta. Nijar ta samu nasarar kammala babban zagaye na zaɓen ƙasar na kakar 2020-21, irin hakan ya zama sabon gani-(ba a taɓa gani ba) a Nijar. Duk-da haka dai, abokin hamayyar takarar neman kujerar shugaban kasa ta kasar da ya sha kaye-(ya faɗi zaɓe) kuma tsohon shugaban ƙasar Mahamane Ousmane ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen inda ya gabatar da roƙo bisa shari'a ga kotun kundin tsarin mulki, sai dai haƙa bata cimma ruwa ba-(an yi fatali da lamarin).[3] A ranar 21 ga watan Maris, 2021, ƙungiyoyin jihadi sun jagoranci kisan kiyashi a Tilia , inda aka kashe mazauna ƙauyuka 137.
Abubuwan da suka faru
[gyara sashe | gyara masomin]A cewar Cyril Payen na Faransa 24, "an ji ƙara mai karfi na makami tsawon rabin sa'a a yankin fadar shugaban kasa. Amman rukunin Jami'an Tsaron Shugaban ƙasar sun dakile harin", kuma hayaniyar rikicin ta sa mazauna kusa da yankin suka farka daga bacci, a lokacin dai-dai karfe 3 na dare. [4] Gwamnati ta kama mafi yawan masu hannu a lamarin, amma wasu, gami da shugaban jagorancin juyin mulkin Sani Saley Gourouza, ba'a kama su ba.[5]
Martani
[gyara sashe | gyara masomin]Shugaban maƙobciyar kasar mai ci a lokacin na Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana aikin a matsayin "marasa amfani kuma tsohon yayi".[6] Shugaban Tarayyar Afirka da Kungiyar Tattalin Arziki ta Yammacin Afirka sun yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin, [7] sauran wasu ƙasashe Afirka; Chadi [8] da Aljeriya, sun bi sahu a Allah wadai ɗin. [9][10]
Bayan lamarin
[gyara sashe | gyara masomin]An cigaba daga inda aka tsaya, an aiwatar da rantsuwar sabon shugaban kasar Mohamed Bazoum kwana biyu bayan lamarin. Duk-da haka ga shugaban kasar Bazoum, an kore shi a wani juyin mulkin ƙasar na shekarar 2023 da kayi nasarar akai ta hannun mambobin tsaron shugaban ƙasar da sojojin da ke ƙarƙashin jagorancin Abdourahamane Tchiani.[11]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Niger: Military officials who wanted to overthrow president-elect Bazoum". APA news. APA. 1 April 2021. Archived from the original on 23 April 2021. Retrieved 23 April 2021.
- ↑ "Soldiers arrested in Niger after 'attempted coup'". France 24. Agence France-Presse. 31 March 2021. Archived from the original on 31 March 2021. Retrieved 31 March 2021.
- ↑ "Invité Afrique - Mahamane Ousmane, au Niger: "Je continue de rejeter la décision de la Cour constitutionnelle"" [Guest Africa - Mahamane Ousmane, in Niger: "I continue to reject the decision of the Constitutional Court"]. RFI (in Faransanci). 2021-03-31. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "Niger: le gouvernement dénonce une "tentative de coup d'État"" [Niger: the government denounces an "attempted coup"]. France 24 (in Faransanci). 2021-03-31. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ Yayadiomandehero (2021-03-31). "Niger – Coup d'état : Le capitaine GOUROUZA SANI SALEY serait le cerveau de la tentative du coup d'État avorté, il est le chargé de la sécurité de la compagnie aérienne de l'escadrille de Niamey. Il est actuellement recherché par les forces de l'ordre et de sécurité. D'après une source sécuritaire plusieurs de ses éléments ont été arrêtés" [Niger – Coup d'etat: Captain GOUROUZA SANI SALEY would be the mastermind of the failed coup attempt, he is the security officer of the Niamey squadron of the airforce. He is currently wanted by law enforcement and security forces. According to a security source, several of its elements have been arrested.]. Omega Médias (in Faransanci). Archived from the original on 2021-03-31. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ Dit, Sultan Aziz (2021-04-01). "Tentative de coup d'État au Niger: Buhari condamne un acte naïf et démodé" [Coup attempt in Niger: Buhari condemns naive and old-fashioned act]. La Nouvelle Tribune (in Faransanci). Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "Le Président de la Commission de l'Union africaine condamne fermement la tentative de coup d'Etat au Niger" [The Chairperson of the African Union Commission strongly condemns the coup attempt in Niger]. au.int. Archived from the original on 2021-04-01. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "Le Tchad condamne la tentative de coup d'Etat au Niger" [Chad condemns coup attempt in Niger]. Tchadinfos.com (in Faransanci). 2021-04-01. Archived from the original on 2021-04-01. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ Aib, Ab (2021-04-01). "Niger: La CEDEAO réaffirme sa ferme opposition aux coups d'Etat" [Niger: ECOWAS reaffirms its firm opposition to coups]. AIB - Agence d'Information du Burkina (in Faransanci). Archived from the original on 2021-04-01. Retrieved 2021-04-01.
- ↑ Marouf-Araibi, Yasmine (2021-04-01). "L'Algérie condamne la tentative de coup d'Etat au Niger" [Algeria condemns coup attempt in Niger]. INTERLIGNES Algérie (in Faransanci). Retrieved 2021-04-01.
- ↑ "Niger general Tchiani named head of transitional government after coup". Al Jazeera. 28 July 2023. Archived from the original on 28 July 2023. Retrieved 5 August 2023.
