Yusra Mardini
An haifi Mardini ne acikin iyalin Sunni na Siriya. Ya girma a Damascus, Siriya, Mardini ya horar dayin iyo tare da goyon bayan Kwamitin Wasannin Olympics na Siriya. [1] In 2012, she represented Syria in the 2012 FINA World Swimming Championships (25 m) 200 metre individual medley, 200 metre freestyle and 400 metre freestyle events.[2]
An lalata gidan Mardini a Yaƙin basasar Siriya . [3] Mardini da 'yar'uwarta Saratu sun yanke shawarar tserewa daga Siriya a watan Agusta shekarar 2015. Sun isa Lebanon, sannan Turkiyya, inda suka shirya a shigo da su cikin jirgin ruwa zuwa Girka tare da wasu baƙi 18, kodayake jirgin ya kasance ba fiye da mutane 6 ko 7 ba ne zasuyi amfani dashi. Bayan Motar ta daina aiki kuma jirgin ya fara ɗaukar ruwa a cikin Tekun Aegean, Yusra, Sarah, da wasu mutane biyu da suka iya yin iyo sunyi tsalle cikin ruwa kuma suka tura kuma suka ja jirgin cikin ruwa sama da awanni 3 har sai kungiyar ta isa tsibirin Lesbos.[4] Daga nan sai suka yi tafiya da ƙafa ta Turai zuwa Jamus, inda suka zauna a Berlin a watan Satumbar 2015.[1] Iyayenta da ƙanwarta, Shahed, suma sun tsere daga Siriya kuma suna zaune a Jamus.[5]
- ↑ 1.0 1.1 Philip Oltermann (18 March 2016). "From Syria to Rio: refugee Yusra Mardini targets Olympic swimming spot". the Guardian. Retrieved 25 March 2016.
- ↑ "The inspirational Olympic journey of refugee swimmer Yusra Mardini". Olympic.org. Olympic Games. Retrieved 25 March 2016.
- ↑ "Olympics hopeful Syrian refugee swims for three hours pushing boat of migrants". Stuff. 21 March 2016. Retrieved 25 March 2016.
- ↑ "After Surviving Aegean Sea, Syrian Swimmer Hopes For Spot In Olympics". NPR.org. 20 March 2016. Retrieved 25 March 2016.
- ↑ "Refugee swimmer Yusra Mardini gets a chance to go the Olympic Games". SwimSwam. 20 March 2016. Retrieved 25 March 2016.