Jump to content

Tukur Yusuf Buratai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Yusuf Buratai)
Tukur Yusuf Buratai
Aliyu Muhammad Gusau

13 ga Yuli, 2015 - 26 ga Janairu, 2021
Kenneth Minimah - Ibrahim Attahiru
military commander (en) Fassara

Mayu 2014 - ga Yuli, 2015
Rayuwa
Haihuwa Biu, 24 Nuwamba, 1960 (65 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Babur
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Jami'ar Tsaron Nijeriya
Harsuna Turanci
Babur
Kanuri
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a soja
Aikin soja
Digiri lieutenant general (en) Fassara
Ya faɗaci Rikicin Boko Haram

Tukur Yusuf BurataiAbout this soundTukur Yusuf Buratai  Laftanar Janar din soja ne a Najeriya kuma tsohun shugaban sojojin kasan Najeriya wanda Muhammadu Buhari ya nada shi tun a 2015. An haife shi a garin Buratai dake karamar hukumar Biu ta jihar Borno, a ranar 24 ga watan Nuwamba a shekarar 1960. Don haka, Buratai ɗan asalin jihar Borno ne dake arewa maso gabashin Najeriya.

Ty Buratai sambisa forest 2017

Laftana Janar TY Buratai shi ne hafsan Sojoji na ashirin da shida 26 a tarayyar Najeriya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar 13 ga watan Juni na shekarar 2015.

Burtai ya yi karatun Furamari a garinsu buratai, daga nan ne ya zarce zuwa Kwalejin Malaman Gwamnati dake garin Potiskum a jihar Yobe. A watan Junairu na shekarar 1981, Buratai ya halarci Nigerian Defence Academy dake Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin membobi a shirin nan na ‘29 Regular Combatant Course (29R)’. Haka zalika, Burtai ya samu takardar shaidar kammala Jami’a, wato Digiri a fannin History daga Jami’ar Maiduguri. Kuma yana da Digiri a fannin Philosophy daga Jami’ar Bangladesh University of Professions dake garin Dhaka.

Kafin naɗinsa a matsayin hafsan Soji, Buratai shi ke jagorantar rundunar tsaro ta hadin–gwiwa wacce ke da hedikwata a birnin Ndjamena na kasar Chadi. Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin ne suka kafa rundunar domin yaki da ’yan ta’addan da ke yankinsu.

A baya dai, Janar Buratai ya yi aiki a matsayin Kwamandan runduna ta Biyu ta sojin Najeriya dake birnin Fatakwal na jihar Rivers, sannan ya taba zama Kwamandan makarantar horas da sojin kasa dake Jaji, a jihar Kaduna.

Tarihin sa da karatun sa

[gyara sashe | gyara masomin]
Tukur Yusuf Buratai

Janar Buratai an haifeshi a garin Buratai, karamar hukumar Biu ta jahar Borno. Mahaifinsa Yusuf Buratai ma tsohon soja ne na Royal West African Frontier Force da kuma Yakin duniya na biyu inda yayi yaki a kasar Burma. Buratai yayi karatunsa na firamare a garin Buratai daga nan kuma ya samu takarar shiga makarantar horar da malamai ta garin Potiskum dake jahar Yobe, inda ya kammala da kyakkyawab sakamako.

Shiga Aikin Soja

[gyara sashe | gyara masomin]
Buratai da wasu manyan mutane

A watana janairu na 1981, Buaratai ya shiga makarantar horar da sojoji dake garin Kaduna. Sakamakon gwaggwabar nasarar da ya samu ta kammalawa ne sai ya samu matsayin Laftanar na biyu a ranar 17 ga Disamba na 1983 a cikin Kuratan sojojin Najeriya. Buratai yayi digiri a fannin ilimin tarihi a jami'ar Maiduguri da kuma wani digirin a fannin falsafa daga jami'ar kwararru ta kasar Bangalidash wato Bangladesh University of Professionals, Dhaka. Ya kuma yi karatu a makaranatr National Defence college, Mirpur, duka a kasar ta Bangalidash.

Ya shiga bataliyar matasan sojoji ta 26 a garin Elele dake Fatakwal, sai kuma mai nazari na harkar soja cikin rundunar sojoji ta majalisar dinkin duniya a kasar Angola, daga baya kuma sai yakoma bataliyar sojojin tsaro a 26 a Lagos wato Lagosa Garroson command Camp. Laftanar Janar Buratai kuma ya rike mukamin mai tafiyarwa na gidan yankin jaha a Abuja; wato 82 Motoruzed Batalion; sai 81 Balation, Bakasi Penninsular; Army Headquaters Garrison, Abuja kafin daga baya kuma sai yazama daraktan ma'aikata a kwalejin horon mayan jami'an soja dake Jaji.

Babban Hafsan Sojin Najeriya Yusuf Buratai
Tukur Yusuf Buratai

Ya kuma rike makamai kamar haka; AHQ Army Policy and Plans, Abuja; Mataimakin Shugaban tsare tsare na al'amuran gudabarwa, HQ Infantry Centre Jaji. Yadai rike mukamai da dama a bangarori daban daban.

Manyan Ayyuka a Matsayin Shugaban Rundunar Sojin Kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan nadin sa a matsayin Shugaban Rundunar Sojin Kasa, Tukur Yusuf Buratai ya jagoranci ayyukan soji da dama da suka shafi yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya. A cikin watanni na farko da fara aiki, dakarun Najeriya sun sake karɓar iko a yankuna irin su Gamboru Ngala, wanda a baya 'yan ta'adda suka mamaye.[1][2][3][4][5][6]

A ranar 25 ga Yuli 2017, Buratai ya amince da karin girma na musamman ga sojoji 6,199 da suka shiga ayyukan yakar 'yan ta'adda.[7]

Buratai ya kuma ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da suka shafi ci gaban ababen more rayuwa da walwalar sojoji a Najeriya. Wannan ya haɗa da kafa gonakin soja da kiwo (Nigerian Army Farms and Ranches), gine-ginen gidaje a wurare kamar Jaji da sansanin Khobe (Jihar Filato), da kuma gyaran ruwa da gidan baƙi.[8][9]

A zamaninsa, an kafa cibiyoyi da dama da kuma shirye-shirye na musamman, ciki har da:

  • Cibiyar Fasaha da Nazarin Muhalli ta Sojojin Kasa, Biu
  • Makarantar Sakandare ta Command, Kebbi
  • Ginin matatar jiragen sama ta soji, Jaji
  • Rundunar Yaƙin Cyberwar ta Sojojin Kasa
  • Kamfanin Kera Motocin Sojoji na Najeriya
  • Kwalejin Yaƙi na Sojojin Kasa (Army War College Nigeria)
  • Gidan Tarihi na Yaƙin Ta'addanci da Yakkin Yankewa
  • Asibitin Matayen Jami’an Sojojin Kasa
  • Gidajen soja (misali: Tinapa da Otukpo Post Housing Developments)
  • Kamfanin Kasuwancin Noma na Sojojin Kasa
  • Rundunonin Special Forces da kuma na Babura
  • Motar sintiri mai kariya daga fashewa (MRAP) da sauran na'urorin gida
  • Kafa Division na 6 da 8
  • Cibiyar Koyon Harsunan Najeriya

[10] [11] [12] [13] [14] [15] [16] [17] [18] [19] [20] [21] [22] [23] [24] [25]

Wallafe-wallafe

[gyara sashe | gyara masomin]

Tukur Yusuf Buratai yana da alaƙa da wasu wallafe-wallafe da suka haɗa da batutuwa kan jagoranci, gogewar soja, da kuma labaran ƙirƙira:

  • The Legend of Buratai (2020) – littafi ne na yara da ke ƙunshe da labarin ƙirƙira wanda aka samo daga tarihin aikinsa.[26]
  • Thought and Principles on Leadership (2022) – littafi ne da ke bayyana kimar jagoranci da ƙa'idodin rayuwa na mutum.[27]
  • Nigeria’s War on Terror – wallafa ce da ke tattauna dabarun yaƙin Najeriya da ta'addanci da tsare-tsaren tsaro.[28]
  • Makintakururi: The Disaster That Never Was – cikakkun bayanai ba su samuwa a yanzu.
  • In the Mind of the General – cikakkun bayanai ba su samuwa a yanzu.

Lambobin Yabo

[gyara sashe | gyara masomin]

Lambobin yabo da karramawa da Laftanar Janar Buratai ya samu sun haɗa da:

  • Tauraron Sabis na Soji (FSS)
  • Tauraron Sabis na Kwarewa (MSS)
  • Tauraron Sabis na Girmamawa (DSS)
  • Tauraron Sabis na Babban Mataki (GSS)
  • Kammala Kwasa-Kwase na Ma’aikata da Digga (psc(+))
  • Lambar Girmamawa ta Jagoranci a Filin Daga
  • Lambar Tallafin Horarwa
  • Lambar MDD don Aikin Tantancewa a Angola (Angolan Verification Medal II)
  • 2022 – Kwamandan Jihar Tarayyar Najeriya (CFR)[29]

Ranakun da ya samu Karin Girma

[gyara sashe | gyara masomin]

Ranakun da aka ba Buratai karin girma sune[30]

Shekara Tambarin Girma Matsayi
Disamba 1983 Laftanar na biyu (An ba shi mukami)
1985 Laftana
1989 Kyaftin
1994 Mejo
1998 Laftanar Kanar
2004 Kanar
2009 Brijadiya Janar
2012 Mejo Janar
Agusta 2015 Laftanar Janar[31]
  1. "Nigerian president replaces military top brass". aljazeera.com (in Turanci). 2015-07-14. Retrieved 2015-07-14.
  2. "Nigeria military recaptures border town from Boko Haram". dailytimesng.com (in Turanci). 2020-09-25. Retrieved 2020-09-25.
  3. "Nigerian troops cross border after Boko Haram clashes". bbc.com (in Turanci). 2016-04-25. Retrieved 2016-04-25.
  4. "Nigerian army blockades Boko Haram base". aljazeera.com (in Turanci). 2013-05-20. Retrieved 2013-05-20.
  5. "Wasu sojojin Nijeriya sun yi Allah wadai da Buratai". bbc.com (in Turanci). 2020-05-20. Retrieved 2020-05-20.
  6. "Nigeria mass abduction seen as copycat attack". wsj.com (in Turanci). 2022-02-22. Retrieved 2022-02-22.
  7. "Operation Lafiya Dole: Buratai grants special promotion to 6,199 soldiers". dailytrust.com (in Turanci). 2017-07-25. Retrieved 2017-07-25.
  8. "Buratai inspects multiple projects in Jos Cantonment". guardian.ng (in Turanci). 2020-09-25. Retrieved 2020-09-25.
  9. "Buratai says Nigerian Army Farm and Ranches Limited will reduce unemployment, insecurity". guardian.ng (in Turanci). 2020-12-29. Retrieved 2020-12-29.
  10. "Nigerian Army commissions smart factory building and accommodation for its personnel". thewhistler.ng (in Turanci). 2018-08-25. Retrieved 2018-08-25.
  11. "Nigerian army creates new division in South-South". pmnewsnigeria.com (in Turanci). 2016-01-14. Retrieved 2016-01-14.
  12. "Buratai launches banking scheme for army in Taraba". dailytrust.com (in Turanci). 2021-01-28. Retrieved 2021-01-28.
  13. "Buratai visits troops of Operation Lafiya Dole". guardian.ng (in Turanci). 2019-11-29. Retrieved 2019-11-29.
  14. "Baba Buhari emerges best participant at Army War College". dailypost.ng (in Turanci). 2020-11-27. Retrieved 2020-11-27.
  15. "Nigerian Army formalises collaboration with firm on food security". nannews.ng (in Turanci). 2025-01-07. Retrieved 2025-01-07.
  16. "Nigerian Army Vehicles Manufacturing Company". theeagleonline.com.ng (in Turanci). 2020-02-15. Retrieved 2020-02-15.
  17. "Buratai still focused on victory over Boko Haram". thecable.ng (in Turanci). 2019-04-25. Retrieved 2019-04-25.
  18. "Army budgets 3.350 billion naira for new aviation unit, drone command centre". dailytrust.com (in Turanci). 2020-03-22. Retrieved 2020-03-22.
  19. "Nigerian Army's Cyber Warfare Command begins operation". vanguardngr.com (in Turanci). 2018-08-12. Retrieved 2018-08-12.
  20. "Insurgency: Army unveils Nigerian-made anti-ambush protected vehicles". businessday.ng (in Turanci). 2016-04-25. Retrieved 2016-04-25.
  21. "Buratai left legacy of service transformation in the army – Analyst". vanguardngr.com (in Turanci). 2025-06-20. Retrieved 2025-06-20.
  22. "Why Army established farms, ranches – Major General CG Musa". dailytrust.com (in Turanci). 2019-06-15. Retrieved 2019-06-15.
  23. "TY Buratai donates 40 books to encourage reading culture among school children". thesun.ng (in Turanci). 2021-04-25. Retrieved 2021-04-25.
  24. "Why 6 Division was created in Niger Delta – GOC". punchng.com (in Turanci). 2019-05-20. Retrieved 2019-05-20.
  25. "Nigerian Army commissions smart factory building and accommodation for its personnel". thewhistler.ng (in Turanci). 2020-04-25. Retrieved 2020-04-25.
  26. "The Legend of Buratai: The children's book and animation that reveals Nigeria's former army chief as the lion killer". sunrise.ng (in Turanci). 2022-01-15. Retrieved 2022-01-15.
  27. "Book Review: Principles for greatness from the life of General Tukur Buratai for youths". guardian.ng (in Turanci). 2022-04-25. Retrieved 2022-04-25.
  28. "A blueprint for tomorrow's leaders: How General Buratai's life lessons are guiding Nigerian youth to greatness". thisdaylive.com (in Turanci). 2025-04-01. Retrieved 2025-04-01.
  29. "FULL LIST: 2022 National Honours Award Recipients The Nation Newspaper". The Nation. 2022-10-09. Retrieved 2022-10-26.
  30. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named NA
  31. Agba, George. "As Service Chiefs Get Promotion: PMB Gives Marching Orders On Boko Haram". Leadership Nigeria. Archived from the original on 20 August 2015. Retrieved 14 August 2015.