Zainab Ahmed
Zainab Ahmed | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
21 ga Augusta, 2019 - 29 Mayu 2023
14 Satumba 2018 - 21 ga Augusta, 2019 ← Kemi Adeosun
11 Nuwamba, 2015 - 19 Satumba 2018 | |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | Jihar Kaduna, 16 ga Yuni, 1960 (64 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Mazauni |
Kaduna Abuja | ||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar Olabisi Onabanjo | ||||||
Matakin karatu |
Digiri a kimiyya Master of Business Administration (en) | ||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da accountant (en) | ||||||
Mahalarcin
| |||||||
Wurin aiki | Kaduna da Abuja | ||||||
Employers |
Jihar Kaduna NITEL Federal Government of Nigeria (en) | ||||||
Mamba |
Association of National Accountants of Nigeria (en) Nigerian Institute of Management (en) | ||||||
Imani | |||||||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Zainab Shamsuna Ahmed lafazin magana CON (an haife ta a ranar 16 ga watan Yuni, shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da sittin 1960). ta kasance accountant din Najeriya ne, wacce ta yi ministan kudi, kasafin kuɗi da tsare-tsare na ƙasa tun daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023. Ta taba rike mukamin ministar kudi daga shekarar 2018 zuwa shekarar 2019. A lokacin shekarar 2019, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ma’aikatun biyu a karkashinta a matsayin ministar tattalin arziki.[ana buƙatar hujja]
Accountant ce a sana'an tayi digirin farko a fannin lissafi a ABU Zaria sannan kuma ta yi digiri na biyu a fannin kasuwanci (MBA), Ahmed Zainab an nada ta a matsayin ministan kudi bayan murabus din tsohuwar ministar kudi Kemi Adeosun a ranar 14 ga watan Satumba, shekarar 2018. A shekarar 2015 ne shugaba Buhari ya nada ta a matsayin karamar ministar kasafi da tsare-tsare ta kasa.
Rayuwar farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Ahmed Zainab a jihar Kaduna . Ta yi karatun sakandare a Kwalejin Queen Amina da ke Kaduna, sannan ta ci gaba da karatun A'Level a Zariya. Ta samu digiri na farko a fannin Accounting a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 1981, inda daga nan ta wuce Jami’ar Olabisi Onabanjo don yin MBA.
Ahmed Zainab ta samu MBA a watan Agusta shekarar 2004 daga Jami'ar Jihar Ogun, Ago Iwoye; yayin da ta samu BSc Accounting (1981) daga Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya; IJMB 'A' Levels (1979) daga SBS/ABU Zaria; da WASC 'O' Level a shekarar (1977) daga Queen Amina College Kaduna.[ana buƙatar hujja]
Aikin Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ahmed Zainab ita ce ministan kudi, kasafin kudi da tsare-tsare na kasa na Tarayyar Najeriya. Aikin da ya sa ta zama minista mafi tasiri a ƙasar. A wannan matsayi, tana neman bunkasa kudaden shiga na gwamnati, tare da shirye-shiryen kara yawan harajin da aka kara da ita tare da tauye bashin jama'a wanda a yanzu an kiyasta fiye da dala biliyan 80.[ana buƙatar hujja]
Ahmed Zainab ta kasance tsohuwar sakataren zartarwa na kasa kuma coordinator kungiyar fayyace masana'antu ta Najeriya (NEITI). Ta kuma kasance memba a kwamitin NEITI guda biyu na ƙarshe, wanda tayi aiki a NEITI da na duniya EITI.[ana buƙatar hujja]
Bayan kammala karatunta, Ahmed Zainab ta samu aiki a shekarar 1982 a matsayin Accountant II a babban asusu na ma’aikatar kudi ta jihar Kaduna, sannan aka kara mata girma zuwa Accountant I a watan Maris shekarar 1984, amma a shekarar 1985 ta yi murabus ta koma NITEL. Tun da farko ta yi hidimar matasa ta kasa a jihar Kaduna a shekarar 1981 zuwa shekarar 1982 inda aka tura ta aikin farko zuwa Messrs. Egunjobi Suleiman & Co. Chartered Accountants, kuma ta yi aiki a matsayin mai horas da Audit.[ana buƙatar hujja]
Ahmed Zainab ta yi wa al’ummar Najeriya aiki a manyan mukamai daban-daban, ciki har da matsayin manajan darakta na kamfanin saka jari na jihar Kaduna, da kuma babban jami’ar kudi na kamfanin sadarwa ta wayar salula ta Najeriya. An sake nada Zainab kuma aka rantsar da ita a matsayin ministar kudi a ranar 21 ga watan Agusta, shekarar 2019 daga shugaban kasa
Sauran ayyukan
[gyara sashe | gyara masomin]- Africa Development Bank (AfDB), tsohon memba na kwamitin gwamnoni (tun 2018) [1]
- Bankin ECOWAS don Zuba Jari da Ci Gaba (EBID), Tsohon Mamba na Hukumar Gwamnoni (tun a shekarar 2018) [2]
- Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), tsohon memba na kwamitin gwamnoni (tun a shekarar 2018) [3]
- Islamic Development Bank, Tsohon Shugaban Hukumar Gwamnoni (tun a shekarar 2018) [4]
- world Bank, Tsohon Jami'in Hukumar Gwamnoni (tun a shekarar 2018) [5]
Kyauta
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Oktoban shekarar 2022, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba ta lambar girma ta kasa ta Najeriya mai suna Command of the Order of the Niger (CON).
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 2019 Annual Report African Development Bank (AfDB).
- ↑ Board of Governors ECOWAS Bank for Investment and Development (EBID).
- ↑ Members International Monetary Fund (IMF).
- ↑ Board of Governors Islamic Development Bank.
- ↑ Board of Governors World Bank.