Zanen barkwanci na Annabi Muhammad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Wikidata.svgZanen barkwanci na Annabi Muhammad
controversy (en) Fassara
Bayanai
Kwanan wata 2005
Start time (en) Fassara 30 Satumba 2005
Shafin yanar gizo jp.dk

Zanen barkwanci na Annabi Muhammad, zanen ɓatanci ne da wasu jaridu suke yi. An fara buga su a jaridar kasar Denmark . Lamarin ya haifar da hatsaniya ta tashin hankali, kuma ya haifar da mummunar zanga-zanga a duniyar Islama, inda mutane da yawa suka mutu.

Rikicin ya fara ne bayan da aka buga zane-zanen da ke nuna annabin Islama Muhammadu a cikin jaridar Jyllands-Posten ta Denmark a ranar 30 ga Satumba, 2005 . Ƙungiyoyin musulmin Denmark sun gudanar da zanga-zanga don mayar da martani. Yayin da rikice-rikicen ya girma, an sake buga wasu ko duk zane-zanen a cikin jaridu a cikin wasu ƙasashe fiye da hamsin. Zanga-zangar ta ta'azzara lokacin da aka saki katun na bogi.

Ɗaya daga cikin zane-zanen ya nuna Muhammad tare da bam a cikin rawaninsa. Wadansu mutane sun ɗauka wannan yana cewa ne cewa dukkan Musulmi 'yan ta'adda ne. Amma wasu zane-zane sun yi wa jaridar Jyllands-Posten ba'a. Daya ya zagi editocin jaridar, ta hanyar amfani da yaren Farsi.

Masu sukar sun yi ikirarin cewa zane-zanen na cin mutuncin al'adu, kyamar Islama, sabo, kuma an yi niyyar wulakanta tsirarun "wadanda aka ware". Koyaya, magoya bayan majigin ya yi iƙirarin cewa suna ba da muhimmiyar magana kuma buga su yana da ' yancin faɗar albarkacin baki . Sun kuma yi iƙirarin cewa ana yin irin waɗannan zane-zane game da wasu addinai, suna masu hujjar cewa ba a yi wa Musulunci da mabiyansa wata alama ta nuna bambanci ba.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]

Sauran yanar gizo[gyara sashe | Gyara masomin]