Jump to content

Zeinab Camara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zeinab Camara
Rayuwa
Haihuwa Gine, 27 ga Janairu, 1981 (44 shekaru)
ƙasa Gine
Karatu
Makaranta De Montfort University (en) Fassara
University of Leicester (en) Fassara
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
zeinabcamara.com

Zeinab Camara (an Haife ta a ranar 27 ga watan Janairu, 1981) 'yar siyasar ƙasar Guinea ce. Ita ce mace ta farko da ta jagoranci kungiyar kwallon kafa a Guinea.

An haifi Camara a Guinea. Ta koma Leicester don yin karatu; Alakar ƙasa da ƙasa ta farko a Jami'ar De Montfort sannan kuma a jami'ar Leicester dake kusa da ita inda ta karanci Dabarun Gudanar da Jama'a. Ta koma Guinea inda ta yi aiki da Rio Tinto Simandu tare da ministocin gwamnati. A cikin shekarar 2014 ta kasance Archbishop Desmond Tutu Fellow Leadership. [1]

Camara yt zama shugabar majalisar ministocin ma'aikatar ilimi mai zurfi da bincike na kimiyya ta Guinea. [2] Shugaba Alpha Conde ne ya naɗa ta duk da cewa tana matashiya. [3]

Ta kasance mai sha'awar kwallon kafa kuma ta gan shi a matsayin abin hawa don jagorantar buƙatun matasan yankin. Ta zama shugabar kungiyar kwallon kafa ta Fatala a Boffa kuma ta zama mace ta farko da ta jagoranci kungiyar kwallon kafa a ƙasar Guinea. [4] Kulob ɗin yana ƙoƙarin magance rashin zuwa makaranta ta hanyar buɗe makarantar ƙwallon ƙafa ta Ortega inda halartar makaranta ya zama tilas. Kulob ɗin yana cikin rukuni na biyu na ƙasa, amma ya kasance a cikin shekarar 2014 a cikin na uku. [5]

Camara ta tsaya takarar Boffa na jam'iyya mai mulki a watan Fabrairun 2020, bisa aikinta a gwamnati da aikinta na kwallon kafa. A shekarar 2020 an yi taro a filin wasa na Koba. [2]

  1. "Zeinab Camara". alinstitute.org. Archived from the original on 2019-02-24. Retrieved 2020-02-04.
  2. 2.0 2.1 "Législatives 2020: Zeinab Camara accueillie en héroïne à Koba". Africaguinee.com - Site officiel d'informations sur la Guinée et l'Afrique (in Faransanci). 2020-02-03. Archived from the original on 2022-02-24. Retrieved 2020-02-04.
  3. admin. "FORUM: discours de bienvenue de la Présidente du Conseil d'Administration du LEJEDEV – Lejedev" (in Faransanci). Retrieved 2020-02-04.[permanent dead link]
  4. "Fatala FC: Zeinab Camara, now 1st president of a football club in Guinea". OBJECTIF224. Archived from the original on 2025-03-29.
  5. "Ligue 2 : Tabounssou et Fatala relégués en D3". Foot224 - Actualité Sport Guinée (in Faransanci). 2014-08-12. Retrieved 2020-02-04.