Zofeen T. Ebrahim
Zofreen T. Ebrahim 'yar jarida ce mai zaman kanta daga Karachi, Pakistan.[1][2] Ta kasance editan mujallar Woman's Own kuma a halin yanzu ita ce editan The Third Pole;[3] wata kafa da aka sadaukar wajen yada bayanai game da ruwan koguna da kuma tushen su daga tsaunukan Himalayas.[4][5]
Ta ba da gudunmawa ga jaridu da dama na cikin gida da na ƙasashen waje.[6] Haka kuma, an yaba mata saboda gudunmawar da ta bayar a fannin muhalli da al’amuran zamantakewa.[7][6][8]
Ilmi
[gyara sashe | gyara masomin]Ebrahim ta halarci Kinnaird College a shekarar 1982, inda ta kammala digirinta na B.A (Bachelor of Arts) a fannin Adabin Turanci da Ilmin Ƙasa. Bisa ga sha’awarta ta rubuce-rubuce, ta kammala digirinta na master’s a fannin jarida daga Jami’ar Punjab, Lahore a shekarar 1985.[9]
Aikin Yi
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2001, ta fara aiki a matsayin ɗan jarida mai zaman kansa.[10] A aikinta, ta yi aiki tare da wasu jaridu na Turanci da dama kamar Dawn, The News,[11] Tribune, First Post, News Line da mujallar wata-wata ta Current Affairs.[12][13][14]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Zofeen Ebrahim | The Guardian". the Guardian (in Turanci). Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Zofeen T Ebrahim, Author at China Dialogue". China Dialogue (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-28. Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Zofeen T Ebrahim". chinadialogue ocean (in Turanci). Archived from the original on 2020-11-29. Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Zofeen T. Ebrahim – Karachi Literature Festival" (in Turanci). Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Our Team". The Third Pole (in Turanci). Retrieved 2020-11-21.
- ↑ 6.0 6.1 "Zofeen T. Ebrahim". The Independent (in Turanci). Archived from the original on 2022-05-07. Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Writer - Geo.tv: Latest News Breaking Pakistan, World, Live Videos". www.geo.tv (in Turanci). Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Pakistan: Green again". UNESCO (in Turanci). 2019-08-07. Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "CEJ-IBA (Centre for Excellence in Journalism)". cej.iba.edu.pk. Archived from the original on 2020-11-17. Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "SAMAA - zofeentebrahim". www.samaa.tv. Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Zofeen T. Ebrahim:The News on Sunday (TNS) » Weekly Magazine - The News International". www.thenews.com.pk (in Turanci). Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "News stories for Zofeen T. Ebrahim - DAWN.COM". www.dawn.com (in Turanci). Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Zofeen T Ebrahim, Author at The Express Tribune". The Express Tribune (in Turanci). Retrieved 2020-11-21.
- ↑ "Zofeen T Ebrahim, Author at Firstpost". Firstpost. Retrieved 2020-11-21.