Jump to content

Zohran Mamdani

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zohran Mamdani
member of the New York State Assembly (en) Fassara

1 ga Janairu, 2021 -
Aravella Simotas (mul) Fassara
District: New York Assembly district 36 (en) Fassara
Rayuwa
Cikakken suna Zohran Kwame Mamdani
Haihuwa Kampala, 18 Oktoba 1991 (34 shekaru)
ƙasa Uganda
Tarayyar Amurka
Mazauni Astoria (mul) Fassara
Ƙabila Indian Americans (en) Fassara
Ugandan Americans (en) Fassara
Ƴan uwa
Mahaifi Mahmood Mamdani.
Mahaifiya Mira Nair
Abokiyar zama Rama Duwaji (mul) Fassara  (ga Faburairu, 2025 -
Karatu
Makaranta St. George's Grammar School (en) Fassara
Bronx High School of Science (en) Fassara
Bank Street College of Education (mul) Fassara
Bowdoin College (en) Fassara 2014) Bachelor of Arts (mul) Fassara : Africana studies (en) Fassara
Harsuna Turanci
Harshen Hindu
Swahili (en) Fassara
Luganda (en) Fassara
Yaren Sifen
Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, housing counselor (en) Fassara, rapper (en) Fassara da social activist (en) Fassara
Wurin aiki Albany (mul) Fassara da New York
Kayan kida murya
Imani
Addini Shi'a
Jam'iyar siyasa Democratic Party (en) Fassara
Democratic Socialists of America (en) Fassara
Working Families Party (en) Fassara
IMDb nm8421715
transition2025.com

Zohran Kwame Mamdani (an haife shi a ranar 18 ga watan Oktoba, 1991) ɗan siyasa ne, ɗan asalin Uganda da Indiya wanda yake zaune a Amurka. Shi ne ɗan majalisar jiha a New York mai wakiltar Gunduma ta 36, wanda ya haɗa yankuna irin su Astoria da Birnin Long Island a Birnin New York. Mamdani ɗan jam’iyyar Democrat ne, kuma yana daga cikin mambobin Democratic Socialists na Amurka. A shekarar 2025, ya tsaya takara don zama Magajin Garin Birnin New York.[1][2][3][4]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Zohran Mamdani an haife shi a Kampala, babban birnin Uganda. Mahaifinsa, Mahmood Mamdani, sanannen masanin siyasa ne kuma malami, yayin da mahaifiyarsa Mira Nair fitacciyar mai shirya fina-finai ce ta Indiya. Iyalinsa sun koma Amurka tun yana ƙarami. Ya halarci Kwalejin Bowdoin a Maine, inda ya karanci Africana. Bayan kammala karatunsa, yayi aiki a matsayin mai taimakon jama’a da kuma mai shirya harkokin al’umma a New York.

Mamdani a wajen gangamin adawa da wariyar launin fata a Bryant Park, Oktoba 27, 2024


A matsayinsa na ɗan majalisa, ya kasance mai tsayawa kan kare haƙƙoƙin masu haya, rage farashin sufuri, da tallafawa masu karamin karfi. Har ila yau, yana da ra’ayin “democratic socialist”, wato ra’ayin dake neman daidaito a tsakanin talakawa da masu kuɗi.

  1. Gidaje masu arha: Mamdani yana goyon bayan tsare-tsaren da za su kare masu haya daga hauhawar farashin haya da kuma hana korar su daga gidajensu.
  2. Sufuri kyauta: Ya yi kira da a fara shirin gwaji na sufuri kyauta (free bus pilot) domin rage wa jama’a wahala.
  3. Abinci mai rahusa: Ya nemi gwamnati ta bude kantunan abinci a kowanne yanki na birnin domin rage tsadar kayan abinci.
  4. Kare ma’aikata: Ya goyi bayan dokokin dake kare hakkin ma’aikata masu motar haya, musamman bayan matsalolin bashi na "taxi medallion".

Takarar Magajin Garin New York

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2025, Mamdani ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar Magajin Garin Birnin New York a karkashin jam’iyyar Democrat. Ya samu goyon baya daga matasa da masu ra’ayin canji a Siyasa.

A watan Yuni shekarata 2025, ya lashe zaben sharar fage na jam'iyyar Democrat, inda ya doke tsofaffin shahararrun yan siyasa, wannan nasara ta sashi cikin manyan ‘yan takarar da ke neman kujerar Magajin Gari.

Rayuwa ta kashin kai

[gyara sashe | gyara masomin]

Zohran Mamdani yana zaune a Astoria, Queens, tare da matarsa. Yana magana a fili game da adalcin jama’a, yaƙi da wariya, da kuma kare marasa ƙarfi. Tushen rayuwarsa daga Uganda, Indiya da Amurka hakan ya sa ya zama ɗaya daga cikin ‘yan siyasa da ke haɗa al’adun duniya cikin ra’ayinsa na adalci da hadin kai.

Girmamawa da tasiri

[gyara sashe | gyara masomin]

Mamdani yana daga cikin sabbin matasan siyasa da suka kawo sauyi a tsarin siyasa na New York. Ra’ayinsa na siyasa ya jawo hankalin al’umma, musamman matasa da ma’aikata, kuma yana daga cikin fitattun ‘yan Democratic Socialists na Amurka a halin yanzu.

  1. Zohran K. Mamdani – Assembly District 36 – Video. Assembly Member Directory. New York State Assembly. June 6, 2023. Retrieved June 26, 2025.
  2. Mamdani, Zohran (June 15, 2020). New York for the Many | Zohran Mamdani (Vote June 23). Event occurs at 00:12. Retrieved June 27, 2025 – via YouTube.
  3. Samfuri:Cite Instagram
  4. Singh, Anshul (June 25, 2025). ज़ोहरान ममदानी: न्यूयॉर्क मेयर का चुनाव लड़ रहे भारतीय मूल के नेता कौन हैं? [Zohran Mamdani: Who are the Indian-American leaders running for New York mayor?] (in Harshen Hindi). BBC News. Retrieved June 27, 2025.