Jump to content

Zuleikha Hassan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Zuleikha Hassan
Member of the National Assembly (en) Fassara

31 ga Augusta, 2017 -
District: Kwale County (en) Fassara
Election: 2017 Kenyan general election (en) Fassara
Member of the National Assembly (en) Fassara


Member of the National Assembly (en) Fassara

Rayuwa
ƙasaKenya
Karatu
MakarantaJami'ar Cape Town
HarsunaTuranci
Sana'a
Sana'aɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasaOrange Democratic Movement (en) Fassara

Zuleikha Hassan ƴar siyasa ce ta ƙasar Kenya. Ita mamba ce a ƙungiyar Orange Democratic Movement kuma wakiliyar mata ta gundumar Kwale kuma 'yar majalisar dokoki. [1] [2]

Shekarun farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Hassan ta halarci Kwalejin Coast da Cibiyar Karatu ta Gaborone inda ta sami iliminta na O-Level. A Legae Academy da ke Gaborone, Botswana, ta sami karatun sakandare. Tana da kuma digiri na farko a fannin Ci gaba da Sauyin Al'umma daga Jami'ar Cape Town, Afirka ta Kudu. [1] [2]

A halin yanzu Zuleikha Hassan ƴar majalisa ce a gundumar Kwale, muƙamin da ta riƙe tun daga shekarar 2017. Ta kasance mai kula da matasa na ƙasa na ƙungiyar Orange Democratic Movement (ODM) har zuwa shekarar 2008, lokacin da aka ɗaukaka ta a matsayin Mataimakiyar Shugabar Matasa ta Ƙasa ta jam'iyyar. Ita ce ta kafa kuma shugabar ƙungiyar mata Musulmi ta Taqwa, Mariakani. Ta haɗu da kafa ƙungiyar matasa ta Inter Party Forum a Kenya kuma ita ce mai kula da shirye-shiryen ƙungiyar ilimi da walwalar musulmi (MEWA). [1] [2]

A ranar 7 ga watan Agustan shekarar 2019, an kore ta daga Majalisar Dokoki saboda kawo jaririnta mai watanni biyar zuwa zauren Majalisar Dokoki. Don nuna rashin amincewarsu da cire ta, 'yan majalisa da dama sun fita daga Majalisar a wannan rana. Wannan lamari ya bazu a shafukan sada zumunta kuma ya haifar da muhawara.[3][4][5][6][7][8][9]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Zuleikha Hassan tana da aure, kuma tana da 'ya'ya uku. [10] [11]

  1. 1 2 3 "Hon. Zuleikha Juma Hassan, Nominated Member of Parliament | KEWOPA KENYA" (in Turanci). Retrieved 2019-12-03.
  2. 1 2 3 "Hon. Hassan, Zuleikha Juma | The Kenyan Parliament Website". www.parliament.go.ke. Retrieved 2019-12-03.
  3. ↑ "WATCH: MP thrown out of Kenyan parliament after bringing her 5-month-old to work". News24 (in Turanci). 2019-08-08. Retrieved 2019-12-03.
  4. ↑ "Kenya: Female MP removed from parliament for bringing baby". www.aljazeera.com. Retrieved 2019-12-03.
  5. ↑ "This Kenyan MP Was Kicked Out of Parliament for Bringing Her Baby". OkayAfrica (in Turanci). 2019-08-07. Retrieved 2019-12-03.
  6. ↑ "Kenyan MP and baby ejected from parliament session". The Guardian (in Turanci). Associated Press. 2019-08-08. ISSN 0261-3077. Retrieved 2019-12-03.
  7. ↑ Mureithi, Carlos; Specia, Megan (2019-08-07). "Lawmaker Kicked Out of Kenyan Parliament for Taking Baby to Work". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Retrieved 2019-12-03.
  8. ↑ "Kenyan MP with baby ordered to leave parliament" (in Turanci). 2019-08-07. Retrieved 2019-12-03.
  9. ↑ Kimeria, Ciku (12 August 2019). "The entrenched patriarchy of Kenyan politics kicked out an MP for bringing her baby to parliament". Quartz Africa (in Turanci). Retrieved 2019-12-03.
  10. ↑ Kagweni Micheni, for (7 August 2019). "Kenyan MP sent out of chamber for bringing her baby". CNN. Retrieved 2019-12-03.
  11. ↑ Mabonga, Masolo (2019-08-10). "MP Zuleikha Hassan reveals she planned with hubby to sneak baby into chambers". Tuko.co.ke - Kenya news. (in Turanci). Retrieved 2019-12-03.